Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu
Published: 10th, July 2025 GMT
Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya (Kwastam), ta ce ta kama wata mota da ke ɗauke da wata kontena maƙare da mazaƙutar jakai a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Hukumar ta Kwastam ta sanar da kama motar ne a ranar Alhamis.
Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a JosAn gano waɗanda suka yi safarar ne da ake zargin suna shirin fitar da shi zuwa ƙasashen waje ba bisa ƙa’ida ba.
An samu nasarar ne a ranar Juma’a 5 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 9 na dare, bayan wani haɗin gwiwa da jami’an ofishin kula da namun daji na musamman da na hukumar Kwastam suka gudanar.
Kwaturola Janar na Hukumar kwastam, Mista Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.
Maimagana da yawun hukumar ta Kwastam, Abdullahi Aliyu Maiwada wanda ya wakilci Kwanturola Janar na Kwastam ya bayyana cewa, nasarar kama masu aikata hakan na cikin ƙoƙarin da ake yi na daƙile kasuwancin dabbobin dawa ta ɓarauniyar hanya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Kwastam
এছাড়াও পড়ুন:
Sakin Maryam Sanda shi ne ƙololuwar zalunci —Dangin Bilyaminu
Dangin Marigayi Bilyaminu Ahmed Bello sun bayyana takaicinsu bisa sanya matarsa, Maryam Sanda, wadda kotu ta ɗaure ta kan laifin soka masa wuka har lahira, a cikin jerin mutanen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa.
A shekarar 2020 ne kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu.
Sanarwar da dangin marigayin suka fitar ɗauke da sa hannun Dakta Bello Haliru Mohammed (Dangaladiman Gwandu) ta bayyana afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda a matsayin “mummunan famu,” da kuma ƙololuwar rashin adalci ga ɗan uwansu.
Sun bayyana takaici bisa sakin Maryam Sanda daga gidan yari, wanda suka kira da neman faranta wa danginta rai, ba tare da la’akari da rabi na har abada da ta yi wa ’yan uwa da iyaye da dangi da a aminan Bilyaminu da kashe ba.
Maryam Sanda mai shekara 37 tana daga cikin jerin mutane 175 da Shugaba ya yi wa afuwa a ranar Alhamis da ta gabata.
Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila Issa Bakary Tchiroma ne ya lashe zaɓen Kamaru —’Yan adawaLaifukan da aka yanke musu hukunci su haɗa da cin amanar ƙasa, kisan kai, da masu sayar da makamai ga ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da dillalan miyagun ƙwayoyi da ’yan damfara da masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar da kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya fitar ta nuna cikinsu akwai masu zaman rai da rai da aka yi wa afuwa gaba ɗaya da waɗanda aka sassauta hukuncin.
Akwai kuma wadanda aka yi wa afuwa bayan ransu kamar Manjo-Janar Mamman Vatsa da Cin Herbert Macaulay da Ken Saro Wiwa, da fitattun mutane irin su Farfesa Wole Soyinka da Faruk Lawan da Farfesa Magaji Garba da Manjo Akubo da sauransu.
Jerin sunayen mutanen da aka yi afuwar ya haifar da ce-ce-ku-ce. Onanuga ya ce an yi musu afuwa ne bayan sun nuna nadama tare da zama mutanen kirki gami da yawan shekaru da sauransu.
Shari’ar Maryam SandaDambarwar Maryam Sanda yana daga cikin shari’o’in rikicin ma’aurata da ya kai ga kisa suka fi ɗaukar hankali a baya-bayan nan.
Abin ya faro ne bayan rikici tsakaninta da Bilyaminu wanda a ƙarshe ta soka masa wuƙa har lahira.
Ta musanta tuhumar da ake mata, a ayin da aka gurfanar da ita a gaban Babbar Kotun Abuja.
Bayan tsawon lokaci ana shari’a, a watan Disambar 2020, Mai Shari’a Yusuf Halilu, na Kotun Ɗaukaka Ƙara yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya, wanda daga baya Kotun Koli ta tabbatar a watan Oktoba 2023.
Daga lokacin zuwa yanzu ta yi zaman shekara shida da wata takwas a Babban Gidan Yarin Suleja.
Martanin dangin BilyaminuDangin Bilyaminu sun bayyana sakin Maryam Sanda a matsayin “rashin adalci mafi raɗaɗi da za a iya jefa iyali saboda wanda suke ƙauna,” inda suka bayyana ta a matsayin “mai kisa da kotu ta tabbatar da laifinta” wadda ba ta taɓa nuna nadama ba tun daga farkon shari’arta har zuwa ƙarar da ta daukaka.
Sun ce tun bayan mummunan abin da ya faru a ranar 19 ga Nuwamba, 2017, sun zabi su yi shiru saboda girmama ’ya’yan da aka bari, duk da ƙaryar ɓangarenta ake yaɗawa.
Sun bayyana cewa sun dogara ne da tsarin shari’a, wanda ya tabbatar da hukuncin kisa da kotunan farko suka yanke — har zuwa Kotun Koli a 2023.
Iyalin sun ce wannan hukunci ya ba su ɗan nutsuwa, amma yafiyar shugaban ƙasa ta sake buɗe musu raunin da ke ci gaba da zubar da jini, tare da rage darajar rayuwar wanda aka kashe. Sun soki dalilan yafiyar, suna cewa an yi ta ne bisa roƙon iyalan Sanda, alhali kuwa Bilyaminu ma ɗa ne, aboki, kuma uba mai ƙauna wanda “aka tauye masa damar rayuwa da renon ’ya’yansa.”
Sun kammala da cewa sun bar komai ga adalcin Allah, “Mai Shari’a na gaskiya,” tare da yin addu’a ga Allah Ya jikan Bilyaminu, Ya kuma ba ’ya’yansa da masoyansa ƙarfin jure wannan raɗaɗin.