Iran: Goyon Bayan Shugaban Gwamnatin Jamus Ga ‘Yan Sahayoniya, Yin Tarayya Ne A Fada Da Iran
Published: 12th, July 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; Amincewa da aikata zalunci, ya yi daidai da hada baki da mai aikata shi.”
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Dr. Baka’i wanda ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Shugaban gwamnatin kasar Jamus yana ci gaba da nuna goyon baya ga munanan ayyukan da HKI take aikatawa wanda yake cin karo da yarjeniyoyin MDD da kuma dokokin kasa da kasa.
Haka nan kuma Dr. Baka’i ya ce; Abinda Jamus din ta aikata zai mayar da ita wacce za ta amsa tambayoyi a matsayin wacce take yin zuga a aikata laifi.
A lokacin da HKI ta fara kawo wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hare-hare dai shugaban gwamnatin Jamus ya bayyana cewa; Da sunansu HKI take yin kazamin aikin da take yi.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Tarayya Ta Karrama NPA Da Kyautar Gaskiya Da Riƙon Amana Ta 2025
Shi ma Shugaban Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Wadada, ya bayyana cewa wannan kyauta alama ce ta gaskiya da amincewa da ayyukan hukumar.
Ya ce NPA ta nuna ƙwazo wajen bin ƙa’idojin lissafi da kuma tallafa wa hanyoyin bayyana gaskiya a ayyukan gwamnati.
Shugaban NPA, Dr. Abubakar Dantosho, wanda ya karɓi kyautar a madadin hukumar, ya sake tabbatar da ƙudirinsa na yin gyare-gyare da kuma tabbatar da gaskiya a dukkanin ayyukan hukumar.
Dr. Dantosho ya ƙara da cewa yin adalci da riƙon amana wajen harkokin kuɗi na daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da niyya a ƙarƙashin shirin “Renewed Hope”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp