Kwamandan Sojin Iran Ya Jaddada Kare Kan Iyakokin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Published: 10th, July 2025 GMT
Kwamandan sojojin kasa na sojojin Iran ya jaddada wajabcin Karin daukan matakan kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Kwamandan sojojin kasa na kasar Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya jaddada wajibcin kare cikakken kan iyakokin kasar akida, al’adu, da yanki, yana mai cewa: Dole ne dukkanmu al\umma su zama masu kare wannan kasa da kuma samun kwarin gwiwa daga tafarkin shahidai.
A yayin wata ganawa da iyalan shahidan kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyawa ta kakaba wa Iran a birnin Sarpol-e Zahab na lardin Kermanshah a ranar Larabar da ta gabata, Birgediya Janar Heidari ya bayyana cewa: Sojojin kasar suna kan gaba wajen kare ‘yancin kai da yankinsu na kasar, kuma a kodayaushe suna nuna godiya da irin hakurin da iyalan shahidan suke yi.
Ya kara da cewa: Tutar tsaro da tsayin daka za ta ci gaba da tashi har zuwa bayyanar Imam Mahdi (Allah madaukakin sarki ya gaggauta bayyanar da shi), kuma a ko da yaushe za ta kasance tana daga hannun mujahidai masu sadaukarwa.
Babban kwamandan dakarun sojin kasar Iran ya bayyana cewa: Shahidai masu haskaka hanyar daukakan ne da ‘yancin al’ummar Iran, kuma sun sadaukar da rayuwarsu wajen tabbatar da tsaro da kuma abin alfaharin al’ummar musulmi a yau.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kiyaye Hadura Ta Kasa Za Ta Aiki Da ‘Yan Jarida A Kano
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, ta bayyana kudurinta na kara zurfafa dangantakarta da kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Kano.
Wannan alkawari ya fito ne daga bakin kwamandan sashin, Kwamandan Corps Muhammad Bature, a lokacin da yake karbar sabbin shugabannin majalisar a hedikwatar hukumar FRSC da ke Kano.
Sabbin shugabannin kungiyar masu aiko da rahotanni ta NUJ sun ziyarci hukumar FRSC ta Kano domin taya rundunar murna kan kokarin da take yi na inganta hanyoyin kiyaye hadurra da kuma gano sabbin hanyoyin hadin gwiwa.
Kwamandan sashin ya yi maraba da ziyarar, inda ya bayyana ta a matsayin wata babbar alama ta tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin FRSC da NUJ.
Ya bayyana jin dadinsa na yin aiki kafada da kafada da NUJ domin inganta moriyar juna.
Kwamandan sashin ya kuma gayyaci mambobin Kungiyar da su shiga rundunar FRSC Special Marshal Corps a matsayin masu aikin sa kai. Wannan shiri na da nufin tallafa wa kokarin da hukumar ta ke yi a fadin kasar na rage hadurran ababen hawa da asarar rayuka.
Da yake mayar da martani ga kwamandan sashin, zababben shugaban kungiyar ta Chapel, Murtala Adewale, ya ce makasudin ziyarar shi ne don kara tabbatar da alakar da ke tsakanin FRSC da jami’an kungiyar.
Adewale ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa FRSC zai bayar da dandali fadakarwa da zai kara wayar da kan jama’a kan kiyaye hanyoyin mota a fadin Kano da ma wajen.
Abdullahi Jalaluddeen Kano