Mayakan Huthi Sun Kara Kai Wasu Hare-Hare da Makamai Masu Linzami Kan BenGurio
Published: 11th, July 2025 GMT
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu ci gaba da kai wadan nan hare-hare har zuwa dakatar da kissan kiyashin Falasdinawa a Gaza.
Yahyah Saria kakakin sojojin kasar ta Yemen sun bayyana cewa, sojojinsa sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistic maim suna Zulfikar wanda kuma ya fadi a kan tashar jiragen saman na Lod Airport kusa da Yafa ko tel’aviv.
Ya ce makamin ya sami bararsa kuma ya sa aka tada jiniyar hatsari a garuruwa 300 a yankin. Banda haka yace miliyoyin yahudawa ne suka je karkashin kasa don tsira da ransu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin
A matsayin birnin dake karbar bakuncin taron, Dunhuang mazauni ne ga wurare 3 dake cikin jerin wuraren gargajiya na hukumar UNESCO da kuma wuraren kayayyakin gargajiya sama da 260, wanda kuma ke nuna hadaddun dabarun da aka dauka a shekarun baya-bayan nan da nufin kare al’adun gargajiya yayin da ake bunkasa birnin. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA