HausaTv:
2025-10-15@02:30:58 GMT

 Arakci:  Babu Batun Tattaunawa Akan Makaman Kasar Iran

Published: 13th, July 2025 GMT

Ministan harkokin wajen JMI Abbas Arakci ya bayyana cewa: ” Iran za ta ci gaba da riko da Karfin makaman da Iran take da shi, babu kuma wata tattaunawa da za a yi a kansa.”

Arakci wanda ya gana da jakadun kasashen waje da suke a nan Iran ya fada a jiya Asabar cewa; Ina yin godiya ga dukkanin kasashen da su ka yi tir da harin wuce gona da iri akan Iran,musamman akan cibiyoyinta na Nukiliya, su ka kuma nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Iran.

Haka nan kuma ya bayyana takaicinsa akan wasu kasashe da su ka kame bakinsu ba ce komai ba akan yin tir da wuce gona da irin abokan gaba, duk da cewa abinda aka yi din keta dokokin kasa da kasa ne.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da cewa; Shirin Nukiliyar Iran na zaman lafiya ne,kuma zai ci gaba da zama a hakan.” Arakci ya bayyana yadda Iran take memba a cikin hukumar hana yaduwar makaman Nukiliya, kuma za ta ci gaba da zama a cikinta.

Akan aiki tare da hukumar hana yaduwar makaman Nukiliya, ministan harkokin wajen na Iran ya ce za su ci gaba da aiki a tare da ita, amma da wata siga ta daban.”

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da cewa; A shirye muke mu koma aiki da diplomasiyya, amma ya zama wajibi ga daya bangaren su fahimci cewa diplomasiyya ba abinda za a fake da ita ba ne, a cimma wata manufa ta daban.”

Abbas Arakci ya kuma ce, matukar ba a yarda da batun hakkinmu na tace sanadarin urani’um ba, to babu wata yarjejeniya da za a cimmawa.”

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki.

Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba Putin ya isar da sakonsa ga JMI wanda kuma shi ne wai yana son warware matsalolin sa da JMI cikin lumana da zaman lafiya, ba tare da fito na fito ba.

Akwai jita-jita da dama a cikin yan kwanakin da suka gabata kan cewa HKI da Amurka a wannan karon har da kasashen yammam na shirin farwa kasar Iran da yaki da nufin lalata cibiyoyin makamashin nukliya na kasar don hanata abinda suka kira makaman Nukliya.

Baghaei ya bayyana cewa JMI ta kare kanta daga hare-haren Amurka da kuma da kum HKI a cikin yakin kwanaki 12 da suka dora mata sannan a shirye take ta fuskance yaki wanda ya fi na watan yunin da ya gabata tsanani.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI October 14, 2025 An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia October 14, 2025 Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa October 14, 2025 Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya October 14, 2025  MDD: Mutane 300,000 Su Ka Gudu Daga Sudan Ta Kudu A 2025 October 14, 2025 Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya October 14, 2025 Larijani:  Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa  Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara October 14, 2025 Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta  Ga Kungiyar Red Cross October 13, 2025 Iran: Kakabawa Kasa Mai Makwabta 16 Takunkumi Ba Abu Ne Mai Sauki Ba. October 13, 2025 An Gano Gawarwaki 323 Karkashin Burabutsai Bayan Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata
  • Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI
  • Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya
  • NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Ta Yajin Aiki?
  • Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba
  • ‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Tabbatar Da Masu Sa-kai Kan Sahihiyar Kariya.
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta
  • Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice  
  • Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa