Associated Press: Harin Iran Akan Sansanin Amurka Dake Kasar Qatar Ya Lalata Wata Cibiyar Sadarwa
Published: 11th, July 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun “Associated Press” wanda ya sami hotunan tauraron dan’adam na cibiyar sojojin Amurka dake “al-udid” a kasar Qatar, ya nuna yadda harin ya sami wata Qubba, da a cikinta akwai na’urorin sadarwa da Amurka ke amfani da su.”
Hotunan tauraron dan’adam na ” Planet Labs” sun nuna yadda Qubbar ta sansanin Amurka a Qatar take sa’o’i kadan gabanin a kai harin a ranar 23 ga watan Yuni.
Rundunar Amurka ta 379 mai aikin ttatara bayanai ta kafa wannan Qubbar ne tun a 2016 da kudin da sun kai dalar Amurka miliyan 15.
Haka nan kuma tauraron dan’adam din ya nuna yadda qubbar ta bace, da kuma yadda ginin da yake kusa da ita ya illata.
Kamfanin dillancin labarun na “AP” ya kuma ce; Abu ne mai yiyuwa baraguzan makami mai linzami ne su ka shafi qubbar, amma kuma zai yiyu Iran ta yi amfani ne da jirgin sama maras matuki wajen kai harin.
A gefe daya, kamfanin dillancin labarun na “Associated Press” ya ambato Ahmad Alamul-Huda, mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara, yana cewa, bayan kai harin na Iran, an sami yankewar hanyoyin sadarwa a cikin sansanin na Amurka.
A ranar 23 ga watan Yuni ne dai dakarun kare juyin musulunci na Iran su ka sanar da kai wa sansanin Amurka dake kasar Qatar hari, a matsayin mayar da martani na kai wa cibiyoyinta na Nukiliya hari.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliya Kasar Idan Tanaso
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin Amurka da JMI sun lalace ne saboda zagon kasar HKI da farwa kasar da yaki. Yace gwamnatin Amurka idan tana so zata farfado da shi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani rubutun da yi wa jaridar ‘Financial Times ta Amurka. Inda y ace : Har yanzun JMI tana bukatar hanyar Diblomasiyya, amma kuma hakkinta ne mu yi shakku a kan ninyar Amurka niyyar Amurka a tattaunawa da ita. Idan Amurka da gaske take ta nuna cewa ta warware wannan matsalar to tana iya yin haka da adalci.
Sai dai, inji ministan, yakamata Amurka ta san cewa al-amura sun sauya kuma bayan wannan yaki na kwanaki 12 da HKI da ita suka kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar har guda uku ta kuma kashe manya-manyan Janaral na sojojinmmu sannan ta kashe masana fasahar nukliyammu da kuma wasu Iraniyawa.
Aragchi ya ce: Iran ba zata mika kai kamar yadda Amurka take riyawa ba. Iran kasashe wacce tayi shekaru dubbai a duniya, kuma ta kutsa yake-yake da dama a baya ta kuma sami nasara. Sannan yace: Muna son zaman lafiya a ko yauce, amma mune muke iya tabbatar da ita ko mu hanata tabbata.
Yace: A halin yanzun kuma ba zamu taba amincewa da kissam mutanemmu ba.