Aminiya:
2025-07-10@23:37:54 GMT

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya

Published: 11th, July 2025 GMT

Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 24 a wasu sabbin hare-hare da suka ƙaddamar a maɓoyar ’yan ta’addan a yankunan daban-daban a Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Kwamandan haɗakar rundunar Operation Haɗin Kai a Arewa Maso Gabas, Janar Abdulsalam Abubakar ya ce an kai samamen ne bayan tattara bayanan sirri.

A cewarsa, an kuma kashe mutum biyar da suke samar wa ’yan ta’addan kayayyakin amfani, a wani kwanton ɓauna da aka yi musu da daddare.

An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu

An gudanar da waɗannan ayyuka ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli a Dajin Sambisa, da Dandalin Timbuktu da kuma Tsaunukan Mandara da ma wasu wuraren daban.

A yayin samamen, rundunar ta ce an yi nasarar ƙwato muggan makamai da dama da babura da kekuna da kayan abinci da kuma kaki da takalman sojoji.

Manjo Janar Abdulsalam ya ce rundunar hadin gwiwa ta bangaren sojin sama, da Civilian Joint Task Force, da na sojojin Nijeriya ne suka gudanar da aikin.

Shi ma Kakakin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ Kyaftin Reuben Kovangiya, ya bayar da cikakken bayanin ayyukan a cikin wata sanarwa.

A ci gaba da gudanar da jerin hare-hare na hadin gwiwa a fadin Arewa maso Gabas, sojojin Operation HADIN KAI (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunonin sojin sama da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force da mafarauta, sun yi nasarar gudanar da samame a kan ’yan ta’addar Boko Haram/ISWAP daga tsakanin 4 zuwa 9 ga Yulin 2025 inda suka kawar da ’yan ta’adda da dama.

A daya daga cikin samamen da aka kai a Platari a ranar 4 ga watan Yulin 2025, yayin da sojojin suka yi kwanton ɓauna, sun far wa ’yan ta’addar JAS/ISWAP da ke kan babura da ke tafiya daga dajin Sambisa zuwa Dandalin Timbuktu.

Nan take aka fatattaki ‘yan ta’addan ta hanyar buɗe musu wuta, lamarin da ya kai ga halaka ‘yan ta’adda 3.

Kazalika, bayan samun bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan tada kayar bayan a kewayen yankin Komala, sojoji sun sake yi wa ’yan ta’adda kwanton ɓauna, inda suka kashe wani mayakin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa Boko Haram ISWAP yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Amince Iran ta Kai Hare-Hare Kan cibiyoyin Sojojinta Guda Biyar

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojojinta

Wani jami’in sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci a ranar Talata cewa; Hare-haren da Iran ta kai a watan da ya gabata sun afkawa wuraren sojojin mamayar Isra’ila, matakin da tuni duniya ta amince da kai irin wadannan hare-hare kan cibiyoyin sojin mamaya.

Jami’in da ke magana da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ki bayar da karin bayani, ciki har da gano wuraren da abin ya shafa ko kuma irin barnar da harin ya yi ga kayayyakin aikin soja.

Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama  marasa matuka ciki kan haramtacciyar kasar Isra’ila a watan da ya gabata a matsayin mayar da martani ga hare-haren ba-zata da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a ranar 13 ga watan Yuni kan Iran  wanda harin ya auna fitattun shugabannin sojoji da masana kimiyyar makamashin nukiliyar Iran.

Harin na Iran ya sha mai da hankali kan birnin Tel Aviv da Haifa, matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida musamman wuraren da suke dauke da mutane masu yawa da kuma yankin kudancin Falasdinu da aka mamaye kusa da Beersheba, inda ake da cibiyoyin soji.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno
  • ’Yan sanda sun ƙaddamar da samamen “Operation Kukan Kura”, sun kama mutum 98 a Kano
  • Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 30 A Katsina
  • Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Amince Iran ta Kai Hare-Hare Kan cibiyoyin Sojojinta Guda Biyar
  • An kama ɓarayin babura a Gombe
  • Kakakin Rundunar Izzuddeen Qassam ya Bayyana Yadda Suka Yi Kofar Rago Ga Sojojin Mamayar Isra’ila
  • Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen