’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu
Published: 15th, March 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ƙara haƙuri kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin kawo ci gaba a ƙasar.
Tinubu ya ce duk da cewa gwamnatinsa mai sauraron koken jama’a ce, amma yana so a ƙara haƙuri domin akwai haske nan gaba.
Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a KatsinaWata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ruwaito Tinubu yana wannan furuci ne a ranar Juma’a, yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar fastocin Cocin Katolika ta Catholic Bishop’s Conference of Nigeria (CBCN) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya bayyana wa malaman cocin cewa ya ɗauki matakai masu tsauri bayan ya karɓi mulki a shekarar 2023, ciki har da cire tallafin man fetur.
“Lallai cire tallafin man fetur mataki ne mai tsauri, amma ya zama dole ne domin ba za mu ci gaba da jinginar da ƙasarmu ba,” in ji shi.
“Sai dai akwai alamun nasara da sauƙi a gaba. Ana bayyana abubuwa masu kyau game da Nijeriya, kuma ina alfahari da haka. Matakan nan masu tsauri yanzu sun fara nuna alamomi masu kyau.”
Ya ce damina ta yi albarka wanda hakan ya sa farashin kayan abinci yake sauka, sannan farashin man fetur ma yana sauka.
A game da batun hare-haren ta’addanci, Tinubu ya ce rashin tsaro yana shafar musulmi da kirista, inda ya ƙara da cewa matarsa kirista ce, don haka ba zai zama mai yi musu kisan mummuƙe ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250 ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi.
Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar.
Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki.
Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa wajen gina ta Kofar-Mata.
Ya ce cibiyoyin za su samar da daruruwan ayyukan yi tare da rage matsalolin zaman kashe-wando da ta’addanci a tsakanin matasa.
A nasa jawabin, Ali Musa Kofar-Mata na ƙungiyar IKMA ya gode wa gwamnati bisa wannan gudummawar da ya kira mai sauya rayuwa.
Ya ce cibiyar ta fara ɗaukar matasa maza da mata, kuma horon zai ɗauki watanni uku kafin a shiga sabon zagaye.
Abdullahi Jalaluddeen