2025-11-16@10:34:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6809

«Majalisar Dinkin Duniya»:

    Shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran ya sanar da cewa za a harba tauraron dan adam guda uku zuwa sararin samaniya cikin watanni biyu masu zuwa. Hassan Salarieh, shugaban Hukumar Sararin Samaniya ta Iran, a yayin  jawabi a wani taron fasahar sararin samaniya a Tehran, ya nuna muhimmancin ayyukan da suka shafi bayanai na tauraron...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin...
    Shahararren ɗan wasan wrestling, John Cena, ya samu nasarar lashe kambun Intercontinental a karon farko a tarihinsa. Cena ya lashe kambun ne da yammacin jiya Litinin, bayan ya doke Dominic Mysterio a birnin Boston, ƙasar Amurka. Sanata Jarigbe ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP Da wannan...
    Alƙalin ya jaddada cewa wajibi ne a bi doka da oda domin kare tsarin dimokuraɗiyya, inda ya yi gargaɗin cewa karya doka na iya jefa ƙasa cikin ruɗani. A baya, Mai shari’a James Omotosho, ya taɓa bayar da irin wannan umarni, inda ya dakatar da PDP da INEC daga gudanar ko amincewa da sakamakon taron...
    Sanata Jarigbe Agom Jarigbe, mai wakiltar Arewacin Jihar Kuros Riba, ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Sanatan ya bayyana sauyin shekarsa ne a wasiƙar da Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya karanta a zauren Majalisar ranar Talata. Sauyin shekar ta kara yawan mambobin APC a Majalisar Dattawa zuwa 77
    ’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a. Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro...
    A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro. Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe...
    Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin...
    Ƙungiyar Tsofaffin Sojoji ta Najeriya ta bukaci gwamnati da ta ɗauki matakai na gaggawa wajen inganta rayuwar mata zawarawan sojojin da suka mutu a bakin aiki tare da ba su goyon bayan da ya dace. Sabon shugaban ƙungiyar a Jihar Bayelsa, Mista Baratuaipre Allison-Alamini, ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan rantsar da shi....
    Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa. “Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da...
    An kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na takwas (CIIE) a yau Litinin, inda aka samu daddale kulla cinikin dalar Amurka biliyan 83.49 a cikin yarjejeniyoyi da aka cimma na shekara guda, wanda adadin da aka samu ya karu da kashi 4.4 cikin dari idan aka kwatanta da...
    Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, ta rasu tana da shekaru 89 a duniya. Iyalai sun tabbatar da cewa ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Litinin, bayan fama da doguwar jinya. Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi EFCC na...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa November 10, 2025 Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci...
    Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da yadda aikin hajjin bana zai kasance dangane da abin da ya shafi kudin kujerar aikin da lokacin da za a rufe karbar kudin maniyyata. Wannan dai ya biyo bayan kulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta 2026 da hukumar ta yi a madadin Najeriya da hukumomin...
    Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar,  inda ya bayyana...
    Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka. Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi. Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  Mabiya...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa...
    Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta birnin tarayya (FCT) ta saka ranar 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe da za a biya kuɗin Hajji na shekarar 2026, wanda aka tsara a N7,696,769.76. Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin hukumar a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda jami’in...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025 Manyan Labarai Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya November 8, 2025 Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga...
    Maiyaki ya ce, “Gwamna Uba Sani kwanan nan ya ba da izinin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a karkashin rukunoni daban-daban.   “Za a ci gaba da yin hakan a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin inganta harkar lafiya a jihar.”   Maiyaki ya ci gaba da cewa, Gwamna Sani ya fifita harkar...
    ‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a kauyen ‘Yan Kwada da ke cikin garin Farun Ruwa a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano, inda suka yi awon gaba da mata biyar, ciki har da masu shayarwa. Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kai hari ne a yankin a ranar Lahadi da...
      Mazauna Millennium City a Jihar Kaduna sun zargi kamfanin wutar lantarki na Kaduna Electric da tilasta musu sanya mita da kuma ƙara farashin wuta ba tare da tuntuba ba. Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da MPH Estate, TUC Estate, Urban Shelter Estate, Yardan Allah Estate, Highfield Estate, Rahusa Estate, Danbushiya, Sabon Gari,...
    Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana  mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinawa ta sanar da cewa; sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 44 da suke a cikin sansanonin ‘yan hijira mabanbanta a yankin Gaza. Sanarwar ta ce, wannan adadin, yana a karkashin jumillar ‘yan jarida 254 da su ka yi shahada a tsawon lokacin yakin da ya fara daga watan Oktoba...
    Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.   “A yau, a cikin nuna...
    ’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa. Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa. Wani mazaunin yankin ya...
    Pars Today – Kimanin masu jefa ƙuri’a miliyan 1.3 na Iraki sun je rumfunan zaɓe jiya, Lahadi (9 ga Nuwamba). An gudanar da wannan zaɓen na musamman kwanaki biyu kafin babban zaɓen ‘yan majalisar dokoki na Iraki, wanda za a gudanar a ranar Talata ta wannan makon (11 ga Nuwamba). An ci gaba da gudanar...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi. A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take...
    Allah Ya yi wa Hajiya Ɗayyabatu, mahaifiyar Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abas, rasuwa tana da shekara 93. Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da jinya, a gidanta da ke unguwar Bambale da ke birnin Zariya. Ta rasu ta bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama. Lakurawa sun kashe jami’in...
    A taron CELAC na biyar tare da Tarayyar Turai a Colombia, shugabannin Latin Amurka sun yi Allah wadai da karuwar jibge  sojojin Amurka a yankin Caribbean, suna gargadi game da tsoma bakin kasashen waje da kuma yin kira da a hada karfi da karfe wajen kare ‘yancin kai da zaman lafiya. Shugaban Venezuela Nicolás Maduro...
    Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta,  yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.” A lokacin ziyararsa a birnin Hermel...
    Gwamnan yankin Darfur na Sudan, Bahreldin Adam Karamah, ya bayyana cewa shugabannin mayakan RSF sun aikata laifuka a El Fasher, yana mai jaddada cewa “ba za su iya ɓoye su ba.” A cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA), Karamah ya fayyace cewa shawarar da Majalisar Tsaro ta Sudan...
    A yau Lahadi 9 ga wannan wata, an rufe taron koli na Wuzhen na ayyuka masu nasaba da yanar gizo na duniya na shekarar 2025 mai taken “kirkiro makomar yanar gizo da sadarwa mai bude kofa da hadin gwiwa da tsaro don kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar...
    Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu. Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025 Wasanni Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax November 6, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2,...
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran...
    Wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya ce ya kamata kowane ɗan Najeriya ya damu game da barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa ƙoƙarinsu na yaƙar rashin tsaro, tare da kiran...
    Daga Usman Mohammed Zaria Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Abba Zari Malamawa a matsayin sabon shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Dutse. A jawabinsa yayin kaddamarwar shugaban kungiyar na jihar, Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci sabon shugaban da ya kasance mai gaskiya da rikon amana wajen hulda da...
    Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan,...
    A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa zargin gwamnatin kasar da kauda kai kan kisan da ake wa kiristoci a kasar. Masu zanga-zanga a Kano, dake arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai da barazanar da kuma yin...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su...
    Wasu Karin kasashe takwas sun yi kira da a kama Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila  Benjamine Netanyahu saboda laifukan yakin da ya aikata.  Kasashen Turkiya, Norway, Italiya, Canada, Slovenia da Lithuania, sun bayyana cewa a shriye suke su kama fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila. A kasar Turkiya mai shiga da kara na birnin Istanbul...
    Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi. Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na...