2025-06-03@21:10:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3685

«yan bindiga suka»:

      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Bisa ga hakan ne, Gwamnan jihar, Dakta Nasir Idris ya bayar da wannan tallafin don gudanar da shagalin sallar cikin walwala da Jin dadi”.   Shugaban ya gode wa Gwamnan jihar kan wannan kokarin da yayi na tunanin a zakulo mata uku a kowace rumfar zabe a duk mazabun kananan hukumomin 21 na jihar don basu tallafin N30,000 don gudanar da shagalin sallar Eid-kabir, “muna masa godiya a madadin matan da suka ci gajiyar tallafin”.   Daga karshe, Zuru ya yi kira ga sauran shugabanni da su yi koyi da Gwamnatin jihar Kebbi kan tallafa wa al’umma a jihar musamman a irin wannan lokaci ga wannan lokaci da jama’a ke da bukatar yin layya. Daga kanmu, magana ta ƙare....
     Wata kotun kasar Mali ta kori karar da aka shigar a gabata, don neman soke matakin da majalisar soj0jin kasar ta dauka na rusa jam’iyyun siyasa gaba daya. A ranar 13 ga watan Mayu ne da ya gabata ne majalsiar koli ta sojojin kasar Mali ta fitar da dokar haramta dukkan jam’iyyun siyasa a kasar wadanda yawansu ya kai 300, tare da manusar sake fasalinsu. Wasu lauyoyi da kuma ‘yan siyasar kasar ne dai su ka shigar da karar a gaban kotu, daga cikinsu har da ‘Montagal Tal’ wanda ya kasance jagoran daya daga cikin jam’iyyun da aka majalisar sojojin ta soke. Masu shigar da karar, sun bayyana matakin da majalisar sojan kasar ta dauka da cewa keta hurumin ‘yancin...
    Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba. Jaridar ta kara da cewa: Isra’ila ta ayyana wasu Karin makarantu wadanda Falasdinawa suke samun mafaka a cikinsu domin kai musu hare-hare a nan gaba. A lokacinda HKI ta kasa ganin mayakan Hamas a fili sojojinta sun koma kan kissan Falasdinawa fararen hula, wadanda suke samun mafaka a makarantu. A cikin watanni da suka gabata sojojin mamayar sun kai hare-hare akan wasu gine-ginen 6 wadanda suka kasance makarantu ne, wadanda...
    Daya daga cikin manyan-manyan  jami’an gwamnatin tsohon shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa: “Babu tantama gwamnatin HK Isra’ila ta tafka laifukan yaki a kan Falasdinawa a zirin Gaza da ta killace. Matthew Miller wanda ya yi aiki a matsayin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka tun daga 2023 har zuwa karshen gwamnatin Joe Biden, ya fada wa tashar talabijin ta Sky News kan cewa; Isra’ilan ta tafka laifukan yaki. Da aka yi masa tambaya a kan yakin Gaza a fadar White House, Miller ya ce; An yi ta samun tsabani dangane da yakin, sabani manya-manya wani lokacin kuma kananan sabani, kan yadda za a kare dangantakar  Amurka da HK Isra’ila duk tare da abinda take aikatawa.”. Amma Miller ya...
    Ofishin shugaban kasar Turkiya, ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya a birnin Istanbul, za ta kai ga tsayar da tsagaita budewa juna wuta wanda kuma zai ga, kawo karshen yakin baki daya. Ofishin shugaban kasar Turkiya ya bayyana haka a yau Talata, ta kuma kara da  cewa,; Tattaunawar da aka gudanar a jiya Litinin a tsakanin Rasha da Ukiraniya a kuma fadar shugaban kasar Turkiyya dake birnin Istanbul tana cike da fata na tsayar da yakin. Kamfanin dilalncin labarun “Sputnik” na kasar rasha ya ambato majiyar fadar shugaban kasar ta Turkiya tana cewa; Shakka babu duk wata tattaunawa da bangarori za su zauna akan teburi, tana tattare da kyakkyawan fata, a dalilin haka,...
    A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN.   Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan.   Sanarwar ta jaddada cewa, da zarar an fitar da kudaden, dole ne a aiwatar da duk wasu bukatu da kungiyar ta JUSUN ta gabatar ba tare da bata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
      Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, yace nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru biyu kadai shaida ce ta shugabanci mai hangen nesa da jaruntaka.   Ya bayyana haka ne a yayin taron farko na National Dialogue on Citizen Engagement and National Security da aka gudanar a Abuja, mai taken “One Voice, One Vision: Uniting Perspectives for a Stronger Nigeria.”   A cewar Ministan, wannan taro ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke kokari yi amfani da damamaki da ke gabanta.   Ya jaddada cewa wannan dandali da Voice of Nigeria (VON) ta shirya ba kawai taron tattaunawa kan manufofi bane, sai dai wata kafa ce da aka tanada domin hada ra’ayoyi da...
    Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba da ta gabata da daddare. Ɗaruruwan gidaje sun lalace, inda mutane da yawa suka rasa matsugunansu. Kafar yaɗa Labarai ta BBC ta ruwaito a ranar Litinin cewa yawan mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa sama da 200, kuma an dakatar da ayyukan ceto saboda hukumomi sun yanke ƙauna daga samun wasu da rai. Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya soki rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya yayin ganawa da Grossi a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya soki sabon rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin makamashin nukiliyar kasar Iran yayin ganawarsa da babban darektan hukumar ta makamashin nukiliya ta duniya Rafa’el Grossi a birnin Alkahira. A yayin taron, wanda aka gudanar a babban birnin Masar bisa bukatar Grossi, Araqchi ya tunatar da hukumar ta IAEA da babban daraktan ta game da alhakin da ya rataya a wuyansu na gudanar da ayyukansu cikin kwarewa. Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya soki zarge-zarge marasa tushe da ke kunshe cikin sabon rahoton hukumar ta IAEA...
    Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa da wabi wa fararen hula a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza. Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Shahidan sun fadi ne a lokacin da suke jiran agajin jin kai a titunan Rafah, lokacin da jirage masu saukar ungulu suka bude musu wuta. An tantance biyar daga cikin shahidan, yayin da wasu fiye da 20 kuma...
    Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa. Wannan hauhawan farashin, wana ta zarce abin da aka saba gani a lokutan rani, ya kasaara ƙarfin iyalai yin sayayya domin girki abincin Sallah, wanda hakan ya haifar da damuwa, musamman a jihohin Kano, Taraba, Kwara, da Jigawa. Tsadar da ba a taɓa gani ba a Kano Al’umma a Jihar Kano sun koka bisa mummunan tasirin wannan tsadar rayuwa. Wani ma’aikacin gwamnati mai ’ya’ya biyar,...
    Hukumar ta buƙaci jama’a da su kasance cikin shiri tare da bibiyar sabbin rahotannin yanayi da ta ke fitarwa. Ta kuma ja hankalin hukumomin da ke kula da madatsun ruwa da su saka ido kan matakin ruwa domin gujewa cike-ciken da ka iya haddasa ambaliya. Rahoton ya ƙara da cewa jihohin kudancin Nijeriya da kuma na Arewa ta Tsakiya za su riƙa samun ruwan sama da iska a kai a kai. Sai dai NiMet ta ce jihohin Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa, Benuwe, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Edo, Delta da Abuja ba za su samu ruwan sama da yawa kamar yadda aka saba ba. Hukumar ta buƙaci manoma da su yi amfani da dabarun zamani da ilimin kimiyya wajen...
    Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni.   Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau.   Malam Gusau ya bayyana cewa, duk da cewa ana samun raguna da yawa, amma an samu karancin masu saye.   Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai iya gyaruwa yayin da bukukuwan Sallah ke kara gabatowa.   “Amma idan abubuwa sun ci gaba da haka, to gaskiya, akwai matsala ta gaske,”   “Har yanzu, na yi imani cewa da sauran kwanaki abubuwa za su iya canzawa, in...
    Wata hajiyar Najeriya daga Jihar Filato ta rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya. Hajiya Jamila Muhammad ta rasu ne a yayin da alhazai ke shirin fara gudanar da aikin Hajji gadan-gadan. Sakataren Hukumar Kin Dadin Alhazai ta Jirage Filato, Daiyabu Dauda, ya sanar a ranar Litinin cewa Hajiya Jamila ta rasu ne a asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah, sakamakon tashin cutar suga. Ya ce Amirul Hajj na jihar da wasu manyan jami’ai sun halarci jana’izar marigayiyar, kamar yadda Musulunci ta tanada. Yadda magidanci ya kuɓuta bayan wata 7 a hannun ’yan bindiga NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Hajji ta bayan fage: Saudiyya ta hana mahajjata 269,000 shiga Makka Da rayuwarta, yawan alhazan Najeriya da...
    ’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
    ’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan ke tafiya a kan babban titin zuwa Kontagora a Jihar Neja. A lokacin ’yan bindigar sun buƙaci kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalan mutumin, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne. Ba su sako shi ba sai a ranar Litinin, bayan da suka karɓi ƙarin Naira miliyan 20 daga iyalansa, jimilla Naira miliyan 30 ke nan. A lokacin da suka yi garkuwa da ma’auratan sun buƙaci...
    Ya ƙara da cewa FRSC ta fara bincike kan dalilan da ke jawo hatsarin, kuma za ta gabatar da sakamakon binciken ga hedikwatarta da kuma Gwamnatin Jihar Kano domin ɗaukar matakan da suka dace don hana irin faruwar irin wannan iftila’i a gaba. Hukumar ta kuma sake jaddada ƙudirinta na wayar da kan al’umma kan amfani da hanya yadda ya dace da kiyaye lafiyar masu amfani da hanya. A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Gwarzo, ya wakilta, ya gode wa FRSC bisa ziyarar. Ya bayyana damuwarsa cewa wajen da hatsarin ya faru ya daɗe yana haddasa mummunan haɗura, inda ya bayyana cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya kamata don hana...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na ci gaba da raba dubban mutane da matsugunansu, tare da lalata dukiyoyi a faɗin Najeriya. Ko a makon da ya gabata, wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja sun fuskanci irin wannan ambaliya da ta yi sanadiyyar rasa ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi masu yawa. NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Ko waɗanne hanyoyi za a bi domin kauce wa ɓarnar ambaliya a Najeriya? Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Kasar Sin ta yi hasashen cewa an yi balaguro miliyan 657 a tsakanin yankunan kasarta lokacin hutun bikin Duanwu, wato Dragon Boat, daga ranar 31 ga watan Mayu zuwa ranar 2 ga watan Yuni, inda matsakaicin adadin tafiye-tafiyen da aka samu lokacin hutun bikin a kowace rana ya kai miliyan 219. Ma’aikatar sufuri ta kasar ta bayyana cewa, an samu karuwar kaso 3 bisa dari na adadin tafiye-tafiyen da ake samu lokacin bikin a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Ya ce an kai farmakin ne a kudancin yankin Mai-Galma a karamar hukumar Maru, domin dakile wani gagarumin farmaki da ‘yan bindiga suka shirya kai wa wasu al’ummomi.   Bayan harin ta sama, sai aka tura sojojin kasa domin bin sahun ‘yan ta’addan da aka tarwatsa.   “Sun tabbatar da lalata babura tare da kashe ‘yan ta’adda sama da 20.   “Abin takaici, a yayin harin ta sama, ‘yan banga biyu a yankin, an kuskure su yayin da wasu kuma suka samu raunuka,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
     Gwamnan Babban Bankin Iran ya wanda yake Ziyara a kasar China ya gabaatr da shawarar a kafa bankin hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobi a kungiyar Shangai. Muhammad Riza Farzin ya isa kasar ta China ne domin halartar taron gwamnonin manyan bankunan kasashen da suke mambobi a cikin wanann kungiya, domin yin nazarin hanyoyin aiki tare a tsakaninsu da kuma musayar kudade. Muhammad Riza Farzin ya kuma kara da cewa; Daga cikin ajandar taron kungiyar a China, akwai tattauna batun kafa bankin hadin gwiwa wanda daga cikin ayyukansa a akwai aiwatar da hada-hadar kudade da mu’amala a tsakanin Bankuna.” Gwamnan babban bankin na Iran ya bayyana cewa, wannan kungiyar tana da matukar muhimmanci, domin tana kunshe da kasashe goma daga...
    Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan ya jaddada goyon bayan da kasarsa take bai wa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya, ya kuma kara da cewa; Ana yin nazarin yadda za a gana, a kuma tattauna tsakanin shugabannin kasashen biyu.” Fidan ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa tattaunawar da aka bude a yau ta kai ga haifar da daa mai ido. Haka nan kuma ya ce, kasarsa za ta yi duk abinda za ta iya, domin ganin cewa kasashen biyu sun kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu.  Kafar watsa labaru ta Axios; ta ambato majiyar Ukiraniya na cewa, Rasha ta gabatar da tsarin zaman lafiya wanda ya kunshi yadda za a kawo karshen yaki....
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin Tinubu ta kaddamar ta ofishin mataimakin shugaban kasa a cikin shekaru biyu da suka gabata: Noma Ta bayyana karara tun farkon shekarar 2025, lokacin da Shugaba Tinubu ke neman mukamin shugaban kasar nan, cewa noma ne zai zama babban abin da gwamnatinsa za ta sa a gaba. Ba abin mamaki ba ne ganin shugaban kasa ya cika wannan alkawari. Gwamnatin ta tsara wani tsari na zaburar da sake inganta harkar noma, kamar yadda a cikin shekaru 60 lokacin da Nijeriya ke da dala na gyada a Arewa, da koko a yamma da kuma dabino a gabas. Sannan Nijeriya ta samu isashshen abin da za ta ciyar da al’ummarta da kuma fitar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ranar Laraba, ruwan sama da hazo za su afkawa jihohin Zamfara, Adamawa, Kaduna, Sokoto, Kebbi da Taraba. Daga baya kuma, za a samu ruwan sama a jihohin Katsina, Bauchi da Sakkwato. Arewa ta rsakiya za ta fuskanci ruwan sama a Abuja, Nasarawa, Neja da Binuwe da safe, yayin da yamma za ta shafi Nasarawa, Filato, Kwara da Kogi. A Kudu, ana hasashen ruwan sama da safe a Ogun, Ondo, Oyo, Edo, Enugu, Ebonyi, Cross River, Rivers da Akwa Ibom, sannan daga bisani a rana, za a sami ruwan sama a fadin yankin. NiMet ta gargjama’a su ɗauki matakan kariya, musamman inda hadari zai faru, domin iska mai ƙarfi na iya gabatar da haɗari. An shawarci mutane su guji tuƙi a...
    Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ta cafke wasu gungun masu satar motoci tare da dawo da wata mota da aka sace. A cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, SP Ramhan Nansel ya fitar, ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a cikin wannan aika-aika, a kan hanyar Doma zuwa Lafia, bisa sahihan bayanan sirri. Sanarwar ta kara da cewa, ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗa kai wajen satar mota da bindiga a Jihar Enugu, inda suka kwace wata mota kirar Toyota Venza mai launin baki da karfin bindiga. Sanarwar ta bayyana cewa, saboda saurin tattara bayanan sirri da haɗin gwiwar jihohi ba tare...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa, an shirya wannan rahoton ne karkashin tasirin wasu kasashen Turai. Ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen yammacin duniya ke cutar da martabar wata kungiya ta duniya ta hanyar siyasantar da ayyukanta. A farkon taron manema labarai na mako-mako, Baghaei ya yi la’akari da zagayowar ranar wafatin Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) da shahidan juyin juya halin Musulunci. Ya kara da cewa: Ma’aikatar harkokin...
    Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya tabbatar da cewa dakarun kasar Yemen ne suka kaiwa jirgin Truman mai dakon jiragen sama hari Wani shafin yanar gizo na sojojin Amurka ya amince da cewa: Dakarun kasar Yemen ne suka lalata jirgin Truman. Shafukan yanar gizo na rundunar sojin Amurka Stars and Stripes sun watsa rahoton a yau Litinin cewa: Jirgin dakon jiragen sama USS Harry S da Truman sun dawo Amurka bayan da rikici ya yi tsanani a yankunan da suke shawagi. An lura cewa manyan bangarorin jirgin dakon jiragen saman Amurka a teku sun samu matsalolin fashe-fashe wanda hakan ke bayyana cewa; Jirgin Ruwan Truman da ma’aikatansa sun samu matsalolin ne a cikin tekun Bahar Maliya. Shafukan Stars...
    Ma’aikatan shari’a a Kotun Koli da sauran kotuna sun jinginr shirinsu na fara yajin aiki daga yau Litinin 2 ga watan Yuni domin matsa lamba kan aiwatar da sabbin albashi. Ma’aikatan, a karkashin kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya (JUSUN), sun ce sun janye shiga  yajin aikin ne bayan wani taro da suka yi da Alkalin Alkalan Najeriya, Kudirat Kekere-Ekun inda aka ba su tabbaci mai ƙarfi. Haka zalika, ma’aikatan Hukumar Shari’a ta Kasa (NJC) da Kotun Koli ta Tarayya (FHC) sun kuma yanke shawarar ba za su ci gaba da yajin aikin ba. A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na reshen NJC na JUSUN, Joel Ebiloma, ya bayar, ya ce kungiyar ta ba hukumomi wa’adin makonni biyu...
    Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne. Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti,  Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Ado-Ekiti. Ya bayyana cewa manomin ya daɗe yana fama da hare-haren birai a gonarsa kuma ya kai bindiga domin kare amfanin gonarsa. Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Binciken farko ya nuna cewa mahaifin ya lura...
    Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne. Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti,  Joseph Eribo, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau a Ado-Ekiti. Ya bayyana cewa manomin ya daɗe yana fama da hare-haren birai a gonarsa kuma ya kai bindiga domin kare amfanin gonarsa. Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a Zamfara An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Binciken farko ya nuna cewa mahaifin ya lura...
    Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa. Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti. Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da ɗaukar ɗan wasan gaban ƙasar Brazil Matheus Cunha daga Wolverhampton Wanderes akan kuɗi fam miliyan 62.5, Cunha zai zama ɗan wasa na farko da Ruben Amorim zai saya a wannan bazarar yayin da yake ƙoƙarin sake gina ƙungiyar da ta ƙare a mataki na 15 a gasar Firimiya, Manchester United za ta kammala yarjejeniyar ɗaukar Cunha da zarar an buɗe kasuwar saye da sayarwar yan ƙwallo a ƙasar Ingila. Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a United tare da zaɓin ƙarin shekara, Cunha ya bar Wolves a matsayin ɗan wasa mafi tsada da ta taɓa sayarwa a tarihinta bayan da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan ta...
    Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara. Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar Maru. Jiragen sojin sun kai hare-haren ne domin fatattakar ’yan bindiga da suka kai wa manoma hari a kan babura da rana tsaka. Mazauna yankin sun ce bayan ’yan bindiga sun sace manoma sama da 50 ne jirgin sojin ya amsa kiran gaggawa, amma aka samu kuskure ya kashe wasu ’yan sa-kai da ke ƙoƙarin fatattakar maharan. Bom ɗin Boko Haram ya kashe fasinjoji 9...
    Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara. Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar Maru. Jiragen sojin sun kai hare-haren ne domin fatattakar ’yan bindiga da suka kai wa manoma hari a kan babura da rana tsaka. Mazauna yankin sun ce bayan ’yan bindiga sun sace manoma sama da 50 ne jirgin sojin ya amsa kiran gaggawa, amma aka samu kuskure ya kashe wasu ’yan sa-kai da ke ƙoƙarin fatattakar maharan. Bom ɗin Boko Haram ya kashe fasinjoji 9...
    Mutane tara sun mutu wasu da dama sun jikkata sakamakon tashin wani abu mai fashewa da ’yan Boko Haram suka dasa a ƙauyen Mairari da ke Ƙaramar Hukumar Guzamala ta Jihar Borno. Lamarin ya faru a wata tashar mota a kauyen, wanda ke da nisan kilomita 18 daga Karamar Hukumar Monguno da kuma kilomita 119 daga Maiduguri. Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, mai wakiltar yankin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin “rashin imani.” Abdulkarim Lawal ya bayyana cewa waɗanda lamarin ya shafa mazauna yankin ne masu juriya da ke komawa gonakinsu a Mairari. NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa Layya da hukunce-hukuncenta a Musulunci Kafin yanzu,...
    Ministocin shari’a na Burkina Faso, Mali da Nijar sun amince da kafa kotun hukunta laif  uka da kare hakkin bil’adama ta kungiyar tarayyar kasashen Sahel. Haka kuma za a gina wani gidan yari mai cikakken tsaro a yankin, mai alaka da wannan kotun, domin karfafa hanyoyin yaki da ta’addanci da aikata laifuka a yankin. Sun bayyana hakan ne bayan taron da suka gudanar a birnin Bamako a ranakun 29 da 30 ga watan Mayu. Kotun hukunta manyan laifuka da kare hakkin bil’adama a yankin Sahel A cewar shafin labarai na APANews, za ta dauki nauyin “duba laifukan cin zarafin bil’adama, laifuffukan yaki, kisan kiyashi da ta’addanci, halatta kudaden haram da kuma cin zarafi mai tsanani na ‘yancin dan adam da...
    Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa...
    Iran ta gargadi kasashen yamma aka daukar duk wani irin mataki kan ta a daidai lokain da ake shirin gudanar da taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a mako mai zuwa. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya yi watsi da rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, yana mai gargadin daukar matakin da ya dace. Kazem Gharibabadi ya yi wadannan kalamai ne, bayan da hukumar ta IAEA ta yi zargi a cikin wani rahotonta na sirri ga kasashe mambobinta cewa Iran ta gaza bayar da rahoton ayyukanta na nukiliya a wasu wurare uku da ba a bayyana ba, tare...
    Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon mutuwa. Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata cibiyar rarraba kayan abinci da gidauniyar agaji ta Gaza (GHF) ke gudanarwa, wani kamfani mai zaman kansa da ke samun goyon bayan Isra’ila da Amurka da kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka yi suka. Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zohri yayi Allah wadai da gwamnatin Isra’ila kan harin da ta aikata a rabon kayan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin wanne ya fi zafi – takaicin rasa matsuguni ko alhinin rashin sanin halin da ɗan uwa na jini yake ciki? Wannan ne halin da wasu al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja suke ciki, bayan da suka tsinci kansu tsamo-tsamo a tsakiyar wata mummunar ambaliyar ruwa. Wasu mutanen da dama dai sun yi batan dabo a wannan ibitila’i, wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen da adadinsu ya haura 150. NAJERIYA A YAU: Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu? DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda wadannan dubban...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mahukunta a tarayyar Najeriya sun sanar da kama wasu sojoji  da ‘yan sanda 30 bisa tuhumarsu da sace makaman gwamnati da sayar da su ga kungiyoyi masu dauke da makamai, daga cikinsu har da kungiyoyin da suke ikirarin jihadi. Sanarwar da rudnunar sojan kasar ta Najeriya ta fitar ta kunshi cewa; Farmakin da rundunar sojan kasar ta fara kai wa a cikin watan Ogusta na 2024 tana a matsayin mayar da martani ne akan satar makamai da alabarusai na gwamanti da ake yi, kuma ya zuwa yanzu bincike ya sa an kama sojoji 18 da kuma ‘yan sandan 15 sai kuma wasu fararen hula 8 da su ka hada da sarkin gargajiya daya. Wannan sanarwar dai ta zo ne adaidai...
    Mataimakin shugaban kungiyar Iraniyawa masu bayar da kyautar gabban jikinsu ga mabukata, Umid Qabadi, ya bayyana cewa; A cikin shekaru 25 da su ka gabata, yadda ake kyautar gabban jiki domin yin dashe a duniya ya karu da kaso 70%, kuma Iran ce ta farko wajen yin dashen koda, har ma ana yi ma ta kirari da; Sarauniyar dashen koda.” A yayin wani taro na girmama masu bayar da kyautar gabban jikin nasu domin yi dashe ga mabukata a gundunar Qazwin, mataimakin shugaban kungiyar Umid Qabadi ya ce; Iran ce ta farko a duniya wajen yin dashen gabobi ga marasa lafiya mabukata. Qabadi ya yi ishara da wajabci ganin an bunkasa wannan al’ada ta bayar da gabobin jiki domin yin...
    Sanatocin Arewa sun bayyana alhini da jimami kan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin ‘yan wasan Jihar Kano da ke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala a Jihar Ogun. A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Musa Yar’adua ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da kuma Gwamnatin Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. ‘Yan Wasan Da Tauraruwar Ronaldo Da Messi Ta Hana Su Haskawa Gwamnatin Kano Ta Ba Iyalan Mamatan Wasanni Tallafin Naira Miliyan Ɗaya Kowane Sanata Yar’adua ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin...
    Haka kuma an yi zaratan ‘‘yan kwallo irin su Johan Cruyff da Eusébio da Gerd Müller mahaifin Muller na yanzu da Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil da sauransu amma tabbas ba a samu zazzafar muhawara ba saboda bbau kafafen sadarwa na zamani wadanda yanzu kusan su ne suka hura wutar zazzafar muhawarar a sassa daban-daban na duniya da ake Kallon kwallon kafa. A yanzu dai Messi ne ya fi lashe Ballon d’Or, inda yake da guda takwas: 2009, 2010, 2011, 2012, 2015, 2019, 2021 da 2023, sai Cristiano Ronaldo mai guda biyar: 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017. Sannan Messi ya zo na biyu sau biyar, shi kuma Cristiano Ronaldo ya zo na biyu sau shida, sannan dukkansu sun...
    Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho. A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan sabon ci gaban da aka samu a shawarwarin nukiliyar da kuma dage takunkumin. Sun kuma tattauna rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan Iran. Haka nan kuma yayin da yake ishara da yadda Iran ke ci gaba da ba da hadin kai ga hukumar ta IAEA, da aiwatar da...
    Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka yi a baya, yana mai jaddada cewa Iran za ta dauki natakin da ya dace daidai ayyukan da sauran bangarori suka dauka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a na kasa da kasa ya mayar da martani a jiya Lahadi kan rahoton babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi kan wasu batutuwan kariya da suka shafi Jamhuriyar...
    Yanzu haka, akalla ana iya karbar sama da Naira miliyan 100 daga wannan PAYE a kowane wata. Wasu hanyoyin samun kudaden shiga, sun hada da haya na kasa (ground rent), harajin haya (tenement rate), da harajin wuraren kasuwanci. Har ma da noma, ana sa wa haraji a Suleja, duk da cewa; gwamnan jihar manomi ne. Ya dace gwamnati ta tabbatar da cewa; ana samar da kayayyakin more rayuwa masu inganci a Suleja, ko da don a samu karin haraji ne. Idan har gwamnatin tarayya ba ta yaba da sadaukarwar da Suleja ta yi ba, to akalla Gwamnatin Jihar Neja; ya kamata ta fi mayar da hankali wajen samar da ci gaba a Suleja, domin karrama gudunmawar da garin ke bayarwa...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake yi kutse cikin garin Al-Qunaitra na kasar Siriya tare da kafa wurin bincike lamarin da ya fusata al’ummar yankin Sojojin mamayar Isra’ila da suka sake yin Kutse cikin yankunan kasar Siriya sun gudanar da sintiri a yankunan tare da kafa shingen binciken ababan hawa tsakanin Khan Arnabeh da kauyen Jaba da ke lardin Quneitra. Sintirin ya kunshi yahudawan sahayoniyya goma masu magana da harshen Larabci na ka’ida kuma suna sintirin ne a motoci kirar Hummer. A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya, sojojin mamayar Isra’ila biyu kuma sun kutsa kai a tsakanin garuruwan Jaba da Khan Arnabeh, kusa da tsohon wurin binciken ababan hawa na Al-Saqri. Sun samu rakiyar motocin sojoji dauke masu rakiya...
    Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin. Sannan ma’aikatar lafiya ta Sudan da kungiyoyi da dama suna ci gaba da kokarin shawo kan cutar don kada ta zama annoba wadda za ta yadu zuwa jihohi da dama. Wakilin gidan...
    A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya. Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu. Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Sam-sam hakan ba shi da wani alfanu domin yana kawo matsaloli da dama wanda babu lokacin lissafosu. Kalubalen da ka iya afkuwa kuwa shi ne; wadansu ‘yan matan ba sa tan-tance wadanda za su sa da wadanda ba za su saka ba, har da masu saka ‘yan’uwan miji, kawaye da ‘yan’uwa na cikin dangi duk a bi a cakuda su guri guda, kuma ba sa yin komai a lissafance ba sa tunanin a cikin yawan al’umman da ke ciki har da shaidani ciki ba, dan akwai wacce abu ya faru da ita daga bude group na biki (sabe the date) abu ya dawo babbar rigima har ta kai ga ‘police station’ kuma ba komai ya kawo hakan ba sai rarrabuwar...
    Iran ta tabbatar da cewa ta samu shawarar da Amurka ta gabatar mata daga hannun kasar Oman game da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya da ake tattaunawa a kai. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ta samu wani bangare na shawarwarin daga Amurka daga Oman mai shiga tsakani kan batun a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X. Ya karbi sakon ne daga hannun takwaransa na Oman Badr Albusaidi, wanda ya gudanar da wata gajeriyar ziyara a Tehran. Saidai ministan harkokin wajen Iran din bai bayyana abinda shawarwarin ke kunshe da ba, amma ya jaddada cewa za a duba su a kuma mayar da amsa wacce ta yi daidai da muradin...
    Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah. Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa. Wani jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta CNN a ranar Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ba za ta hada kai da hukumar Falasdinu ta PA ba da ke neman karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya. Jami’in ya bayyana ziyarar a matsayin tsokana, yana mai...
    Wani rahoto da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya nuna cewa Gaza na fuskantar bala’i mafi muni tun soma yaki a Zirin a watan Oktoban 2023. Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan hakkin bil adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye ya zargi gwamnatin Isra’ila da yin amfani da batun agajin jin kai da gangan domin ci gaba da aiwatar da munanan laifukan da take aikatawa a Gaza. Francesca Albanese a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: “Dukkan wadannan matakan an boye su ne a karkashin sunan agaji don karkatar da hankulan kasashen duniya.” A wani labarin kuma Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya shaida wa manema labarai a...
    Iran ta soki sabon rahoton da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya fitar, tana mai cewa rahoto ne dake kunshe da tuhume-tuhume mara tushe kan shirin nukiliyar kasar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Tehran za ta mayar da martani ga duk wani matakin da bai dace ba daga kasashen Turai da Amurka. Faransa, Jamus da kuma Ingila, tare da goyon bayan Washington, suna son yin amfani da wannan rahoto don aiwatar da wani tsari da zai ba da damar maido da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran. A cikin rahoton nasa, Rafael Grossi ya bayyana...
    Ta hanyar da za ki gano kuwa ita ce, ki kai mata ziyara ta wuni daya kuma idan kin je ki kula da yaya yanayin huldodinta da kuma gyaran jikinta suke a cikin gidanta, ta nan ne za ki fahimci matsalar rashin jituwarta da mijin na ta. Domin ita matsalar rashin kulawa da gyaran jiki wani namiji ba zai iya bude baki ya fada ba. Koda ita matar ma ba zai iya fada mata ba sai dai kurum ka ga ana rigima ita tana ta ganin yana yi mata wulakanci shi kuma ga abin da yake gani daban, don haka yana da matukar muhimmancin ga ma’aurata da su himmantu wajen gyara jiki ba su kadai ba, har da wanda ba...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwaman ya umarci mai rikon mukamin Shugaban ma’aikata, Hukumar bada tallafin karatu ta Jihar, ma’aikatar ilimi,da kuma kungiyar APWEN reshen Maiduguri cewar wadanda suka cika sharuddan da ake bukata ya dace a basu tallafin na karatu. Lokacin taron ya taya Shugabnnin kungiyar amsu barin gado da kuma wadanda za su gaje su kan jajircewar da suka nuna wajen daukakalamarin da ya shafi kwararru ta bangaren Injiniya. Da take gabatar da kasida mai taken, “Muhimmancin daukar nauyin da jawo hankalin’ ya’ya mata su yi karatun Injiniya da daukar abin a matsayin aiki a Nijeriya, ”Uwargidan gwamnan Borno,Dakta Habiba Babagana Zulum, ta lura da cewar daukar nauti wani lamari ne na yadda ake bunkasa ci gaban kwararru,inda ta yi nunu da cewa...
    Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup ta bana da ta kunshi kasashen Ghana, Trinidad And Tobago, Jamaica da Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Abin da ake cewa Layya shi ne duk wata halastacciyar dabba da aka yanka domin neman kusanci ga Allah. Layya tana da asali a cikin Kur’ani da Hadisin Annabi (SAW). A cikin Kur’ani Allah (TWT) Yana cewa: “Ka yi Sallah ga Ubangijinka kuma ka yi yanka.” (Kausar: 2). A Hadisi kuwa Anas bin Malik (RA) ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi layya da raguna biyu bakake, masu kahonni. Ya yanka su da hannunsa, ya yi bisimillah ya yi kabbara, ya kwantar da su ta gefen wuyansu” (Muslim ya ruwaito). Za a yi Huɗubar Ranar Arfa a harsunan Najeriya 3 Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno Akwai Hadisai masu yawa...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah Al-khomaini (q) wanda ya kafa JMI. Ministan da sauran manya-manyan ma’aikata a ma’aikatar harkokin wajen kasar sun je hubbaren Imam ne don jadda bai’a ko alkawali da shi kan tafiya a kan tafarkin da ya barsu a kai. A cikin wani wuri a Jawabinsa Ministan ya kara da cewa a cikin kundin tsarin mulkin JMI ya zo kan cewa Iran ba zata danne wata kasa...
    “Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da suka kamata tun lokacin da aka kaddamar da dokar ta bacin.An horar da Malaman makarantun gwamnati,ana kuma ci gaba dayin hakan. “Saurin biyan kudaden bashi da Hukumomin WAEC da NECO ya kawo kwanciyar hankali ga daliban da suka kammala makaranta da rubiuta jarabawa, sai dai basu samu ci gaba da karatu ba saboda Hukumomin jarabawar sun rike masu sakamakon jarabawar da suka yi. Daga...
    Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana alhininta bisa rasuwar wasu ‘yan wasa daga jihar Kano a wani hadarin mota. A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya fitar, ya ce hadarin ya faru ne yayin da tawagar jihar ke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala a jihar Ogun. Kungiyar ta NGF ta mika ta’aziyyar ta ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano,da ma kasa baki daya. Kungiyar ta roki Allah Madaukakin Sarki da Ya ji kan ‘yan wasan, Ya kuma ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi. Ali Muhammad Rabi’u 
    A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun da farko, jami’an Indiya sun yi ta musanta duk wata asarar jiragen sama a cikin wannan arangama, wanda aka fara ne bayan wani hari da aka kai wa masu yawon bude ido a yankin Kashmir da Indiya ke mulka a watan Afrilu, wanda Indiya ta dora alhakinsa kan Pakistan. Ita kuwa Pakistan, ta yi ikirarin cewa ta harbo jiragen Indiya da dama, ciki har da...
    Masu zanga zanga kimani makunni uku da suka gabata a kasar Libya sun bukaci firai ministan kasar Abdulhamid Dubba ya sauka saboda shi ne ya haddasa rikicin da ya faru a cikin yan makonnin da suka gabata a kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa masu zanga zanga kimani 200 sun taro a tsakiyar birnin Tripoli sun rera takin Dole Dubah ya sauka, wanda kuma suna rera wasu taken. Tun shekara ta 2011 ne a lokacinda kungiyar tsaro ta nato ta goyi bayan yantawaye suka kashe shugaba Kaddafi ne kasar Libya ta rabu gida biyu, bangaren da MDD ta amince da ita a birnin Tripoli da kuma wacce Khalifa Haftar yake jagoranta daga gabacin kasar.
    Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Naija na tarayyar Najeriya NSEMA ya basa sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ranar Alhamis data gabata a karamar hukumar Mokwa ya kai 151 bayan an sake gano karin gawakin mutane 36. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Abdullahi Arah yana cewa banda wadanda suka rasa rayukansu mutane 11 ne suka ji rauni. Sannan mutane 3018 suka kauracewa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa bayan ruwan sama na sa’oii masu yawa. Arah yace gidaje 503 ne suka rushe a jihar sannan wasu 265 suka lalace. Banda haka akwai gadoji biyu da hanyoyi biyu wadanda ruwan ya sharesu.
    Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin  karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, da yin “amfani da talauci a matsayin makami” domin juya ’yan Najeriya. Da yake jawabi a Abuja ranar Asabar a wajen lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, mai taken “Amfani da Talauci a Najeriya,” Atiku ya yi zargin cewa gwamnati tana amfani da matsalar tattalin arziki don sarrafa ’yan kasa. Ya ce, “Abin da muke fuskanta a halin yanzu a Najeriya shi ne gwamnati tana amfani da talauci a matsayin makami.” Atiku ya yi nuni da bambancin yanayin rayuwa a yanzu da lokacin ƙuruciyarsa, inda ya  ce a lokacin Kano...
    A ganin kasar Sin, kafuwar hukumar za ta ba da damar kara shigar da kasashe masu tasowa cikin aikin kula da al’amuran duniya, da tabbatar da daidaita rikici ta wata hanya mai adalci, da bai wa kasashe masu tasowa karin ikon fadin albarkacin bakinsu.   A shekarun baya, kasar Sin ta taimaka wajen tabbatar da samun sulhu tsakanin kasar Saudiyya da ta Iran, da ganin yadda bangarorin siyasa daban daban na Falasdinawa suka kulla yarjejeniyar sulhu a birnin Beijing na Sin. Kana a wannan karo, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a kokarin kulla yarjejeniyar kafa hukumar shiga tsakani. Duk wadannan abubuwa sun nuna yadda Sinawa suke darajanta sulhu da zaman lumana a duniya. (Bello Wang)   Daga kanmu,...
    Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin ciki da alhini kan mummunan haɗarin mota da ya yi ajalin wasu ‘yan wasa daga jihar Kano, yayin da suke dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a jihar Ogun. Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fitar da wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a yau Asabar, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Kano. Mutane 21 Sun Mutu A Tawagar Ƴan Wasannin Kano A Hatsarin Mota Ahmed Musa Ya Angwance Da Matarsa Ta 4 A Kano “Muna miƙa ta’aziyyar ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano da kuma ɗaukacin ma’abota wasanni a faɗin kasar nan,” in ji sanarwar. Gwamna AbdulRazaq ya...
    Karatu, rubutu,da kuma dabarun lissafi wasu dabaru ne da ake samu ta hanyar iulimi. Wadannan dabarun suna bada dama ta dogaro da kai da kuma samarwa kai aiki. Karatu yana bude hanyar sanin ilimi da labarin duniya. Saboda mutane suna fara kasuwanci ne idan har za su iya kasafi,da kuma gane abubuwan da aka kashe a kalla. Ilimin iya karatu da rubutu,da kuma iya samar da hanayar da za aji ra’ayoyi,hakan na kara iya dogaro da kai da kuma samun a rika jin babu wata kasala ko faduwar gaba. Ilimi yana taimakawa mutane wajen yadda wasu daga zama Sanuwar ware. Yin makaranta yana koyawa mutane duk wani matakin da za su dauka ya kasance mai ma’ana, wannan kuwa yana sa...
    Aƙalla mutum 20 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da tawagar Jihar Kano da ke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa (NSF) da aka kammala a Jihar Ogun. Lamarin na ban tausayi ya faru ne a ranar Asabar a garin Dakatsalle, kimanin kilomita 50 daga Kano, yayin da tawagar ke gab da isa gida. Rahotannin farko daga masu bada agajin gaggawa da shaidun gani da ido sun nuna cewa waɗanda suka rasa rayukansu a hatsarin sun haɗa da ’yan wasa da ɗan jarida, ma’aikatan lafiya da jami’an gudanar da harkokin wasanni. Shugaban ƙungiyar marubutan wasanni ta Najeriya (SWAN) reshen Kano, Zahraddeen Saleh, ya tabbatar da wannan mummunan lamari. Ya kuma ƙara...
    Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata,  sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa motar da ke ɗauke da ‘yan wasan, wadda ke ɗauke da mutane 30, ta faɗa gadar ta Dakatsalle da ke jihar ta Kano. “Yayin da nake magana da ku yanzu, mun kirga gawarwaki 19,” ya fada cikin tashin hankali. Ado Salisu, tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida da ke kula da lamuran Wasanni ta Najeriya (SWAN), ya ce an kai...
    Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya Ahmed Musa, ya auri matarsa ta 4, Asmau Moriki, a wani biki na sirri da aka gudanar a jihar Kano, Musa da amaryarshi Asmau sun zama mata da miji watanni kadan bayan haduwarsu, Musa ya bar sansanin tawagar Super Eagles dake birnin Landan domin ya halarci bikin wanda aka gudanar a birnin Kano. Dan wasan dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ya shiga wasan da Nijeriya ta doke Ghana da ci 2-1 a minti 60 na wasan, Musa na daya daga cikin yan wasan da sukafi taka leda a tarihin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya inda kuma ya zamo wanda yafi jefawa Nijeriya kwallaye a gasar kofin Duniya a...
    A kwanan baya, tsohuwar firaministar kasar New Zealand, Madam Jennifer Shipley, ta yi hira da wakilin CMG, inda ta ce, ya dace a koyi ingantattun dabarun kasar Sin a fannin raya kasa. Ta ce yadda kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya, da bai wa sauran kasashe dabaru da fasahohin da ta samu na da ma’ana matuka. Saboda kasar tana kan gaba a duniya, a fannin raya al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. A cewar Madam Shipley, ya kamata a dora muhimmanci kan basirar kasar Sin, saboda an samu isassun shaidun dake nuna cewa, idan an yi amfani da dabarun Sin yadda ya kamata, to, za a samu nasarar raya aikin ilimi, da samar...
    A wancan lokacin, sojojin Nijeriya sun musanta batun Shehun Borno, amma wasu na ganin cewa akwai kashan gaskiya dangane da wannan al’amari, sakamakon irin yadda ‘yan ta’addan ke cin karensu babu babbaka a wadannan yankuna. Shi ma a nasa bangaren, mai sharhi kan kungiyoyin ta’addanci a Cibiyar Tony Blair, Barista Bulama Bukarti, ya ce, “A binciken da muke da shi, mun gano yadda Boko Haram suke amfani da jirage marasa matuka wajen kai wasu hare-hare a sansanonin sojojin Nijeriya.” Idan an yi la’akari da wadannan bayanan sun nuna cewa kungiyar Boko Haram tana ci gaba da fadada ayyukanta a fannoni daban-daban ba tare da an taka mata birki ba. Bisa ga wannan ne, Sanata Mohammad Ali Ndume, mai wakiltar kudancin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan shi ne babban abin alfahari da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ke jagoranta. A yayin tattaunawar manyan jami’an biyu a Berlin tare da ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul, Tuggar ya nuna bajinta. “Ba manufar Nijeriya bace ta fitar da mutane zuwa wasu kasashen waje ba, sai don nuna gwanayenta,” in ji shi, tare da sake sanya haske a manufinta. A cikin shekarun baya-bayan nan, yawan al’ummar Nijeriya sun kasance ana sanya su a matsayin wadanda ke cikin rikici, miliyoyin matasa marasa aikin yi, masu karatun digiri, da kwararru an nuna musu halin ko-in-kula. Amma Tuggar, gogaggen jami’in diflomasiyya kuma mai tunani na Afirka, yana ganin abin da mutane da yawa ke watsi da shi dama ce....
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya soki tsarin shugabanci na Najeriya na yanzu, inda ya bayyana cewa ‘’yan bindigar birni’ sun karɓe ragamar mulkin ƙasar. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar a Abuja, yayin taron lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, mai taken ‘Amfani da Talauci a Matsayin Makami a Najeriya.’ El-Rufai ya bayyana cewa a yanzu ne Najeriya take fuskantar matsalolinta mafiya muni tun bayan samar da ita da matsayin ƙasa ɗaya a shekarar 1914. “Shi ya sa muke tare muna aiki tare da shirya wani haɗin gwiwa don dawo da Najeriya kan turbar da ta dace saboda ta riga ta kauce hanya,” in ji shi. Mutanen da...
    Wadanda ake zaton mawallafin wasikar sun yi jayayya cewa ya kamata a janye tuhumar da ake yi wa Giwa saboda “adalci, daidaito, da aiki mai kyau.” Giwa, tare da mai kula da kadarorin Cecil Osakwe da sauran su, za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda tara da suka hada da fitar da mutane ba bisa ka’ida ba, cin zarafi, barazana ga rayuwa, da barnar dukiya da suka kai Naira miliyan 300. Laifukan da ake tuhumar Giwa da Bukola sun hada da hada baki wajen aikata jabun takardu da aikata laifuka (wanda za a hukunta shi a karkashin sashe na 97 na dokar Penal Code Act, 2004), da rashin gaskiya da aiwatar da takardar damfara (Sashe na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503. Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a...
    Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar. Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503. Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba. Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa. A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada cewa al’ummar ƙasar nan suna tare da su a wannan lokaci na jimami, kuma ba za a yi ƙasa a gwiwa wajen tallafa masu ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Ba za su taba yin watsi da ‘yancin su na mallakar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Iran ba ta neman mallakar makamin nukiliya, kuma ba za ta yi watsi da hakkinta na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana ba. Ya kara da cewa: Iran tana inganta sinadarin Uranium kuma za ta ci gaba da yin hakan domin bunkasa harkokin ci gaban kasarta musamman harkar lafiya, wutan lantarki, likitanci, noma da sauransu. Limamin Juma’ar Ayatullah Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Hakika dogaro da...
    Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa a yayin bikin nasarar da aka yi na aikin tiyatar dashen na’urar magance matsalar Rashin ji da rauninsa sau 1,500 a lardin Khuzestan dake kudu maso yammacin ƙasar. Wadannan tiyata sun bayyana kwarewar aikin likita da basirar likitoci a lardin, wajen maido da ji da magana ga wadanda suka rasa jin tun da fari. Bikin dai ya samu halartar likitoci da ma’aikatan jinya da yara...
    Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen. Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa. Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga...
    Haka zalika, ya kara da cewa; gwamnatinsa ta bayar da kimanin Naira biliyan biyu, domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani mai amfani da hasken rana a garin Baga. Gwamna Zulum ya ci gaba da cewa, kwanan nan ya tura wata tawagar bincike, don yin bincike tare da gano gaskiya zuwa Gamborun Ngala, sannan kuma tawagar ta tabbatar mana da samun albarkatun ruwan karkashin kasa, wadanda za mu iya amfani da su wajen noman rani ta hanyar ban-ruwa. Kazalika, ya sanar da cewa, an kuma kebe karin wasu Naira biliyan 1.5, domin gudanar da irin wadannan ayyuka a garuruwan Gamborun Ngala da Marte, wadanda a halin yanzu an kusa kammala su baki-daya. Bugu da...
    Maƙabartar Kuka Bulukiya maƙabarta ce mai daɗaɗɗen tarihi a cikin ƙwaryar birnin Kano, wadda bayanai suka nuna an shafe sama da shekara 500 ana binne mamata a cikinta. Wannan daɗaɗɗiyar maƙabarta tana da matuƙar muhimmanci musamman la’akari da yawan unguwannin da suka kewaye ta da yawan mutanen da aka binne a cikinta da kuma fitattun mutanen da suke kwance a cikinta. Maƙabartar Kuka Bulkiya ta yi iyaka da unguwannin Dala da Madabo da Yalwa da Kwanar Taya da kuma Gwammaja, sa’annan akan kawo gawarwaki hatta daga unguwanni irin su Gwauron Dutse da Ƙulƙul da Dogon Nama da Madigawa da Sanka da Makafin Dala da dai sauran su. Asali dai an sanya mata sunan Bulukiya ne saboda wata bishiyar kuka mai...
    A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar. Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin. A cewarsa, za su tabbatar da aiki da ka’idojin duniya wajen tsafta, yanka da kuma sarrafa nama. Jami’in ya kuma yaba wa gwamnan na Jihar Gombe, Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa na kokarin kyautata samar da kayan more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Shi kuwa a nasa jawabin, shugaban gudanarwa na kamfanin Arch. Yunusa Yakubu, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci, sannan...
    Sojoji sun yi nasarar cafke wani mutum da ake zargi dan ta’adda ne tare da gano ma’adanar makamai a yayin wani samame da suka yi a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato. Binciken farko ya nuna cewa wanda aka kama ɗin yana da alaƙa da wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da alhakin kisan wani makiyayi da satar shanu 1,250 a ƙauyen Tomborong, Ƙaramar Hukumar Riyom, a ranar 27 ga watan nan na Mayu. A safiyar ranar Juma’a, sojoji suka kama wanda ake zargin, bayan samun rahoto game da inda ake zargin ɗan bangar yake ɓoye a ƙauyen Hura. Yayin wani bincike da aka yi a maboyar wanda ake zargin, jami’an tsaro sun gano bindigar AK-47 guda daya, tare...
    Akasari kafin a girbe ta, tana kaiwa kwanaki 60 zuwa 100 bayan an shuka ta. Kazalika, cikin sauki ake mallakar gonar da ake shuka Masara a Nijeriya, ana kuma shuka Irinta sannan a sayar da ita ga makwabta. Dankali: Dankali na dauke da sinadarin ‘calories’ dan kadan, sannan mutane da dama na kasar nan na sarrafa shi a matayin abinci tare da yin amfani da shi. Yana daukar watanni biyu zuwa uku bayan an shuka shi. Bugu da kari, ana iya shuka shi a kowacce irin kasar noma. Tumatir: Ana matukar amfani da tumatir a Nijeriya, ko danyensa ko kuma busasshe. Yana dauke da sanadarin ‘bitamin C’, yana kuma taimakawa wajen rage kamuwa da cututtuka kamar wadanda ke yi wa...
    Shugaban na Faransa ya ce Faransa za ta iya sanya takunkumi ga gwamnatin Isra’ila matukar ba ta kawo karshen killace Gaza ba, inda kuma ya bukaci kasashen duniya da kada su jajirce wajen tunkarar matsalar karancin abinci a Gaza. A wani taron manema labarai a Singapore a ranar Juma’a, Macron ya ce dole ne Turawa su “tsaurara matsayinsu na hadin gwiwa” kan Isra’ila, “idan babu wani mataki da ya dace da yanayin jin kai, a cikin sa’o’i da kwanaki masu zuwa” a zirin Gaza. Macron ya ce, “Katange ayyukan jin kai yana haifar da yanayi mara kyau,” yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Firaministan Singapore Lawrence Wong. Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da gwamnatin...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kirayi babbar mai kula da harkokin kasar Ostiriya da ke birnin Tehran domin nuna rashin amincewa da zarge-zargen data danganta da na ‘’tsokana” da hukumar leken asirin cikin gidan kasar ta Turai ta yi dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Shugaban ofishin sashen yammacin Turai na ma’aikatar harkokin wajen Iran Alireza Molaqadimi ya gayyaci Michaela Pacher a ranar Juma’a, inda ya nuna bacin ran kasar iran game da zarge-zargen. A cikin rahotonta na shekara-shekara kan barazanar da duniya ke fuskanta, hukumar leken asiri ta kasar Ostiriya (DSN) ta yi ikirari a ranar Litinin cewa Iran na ci gaba da aiwatar da shirin kera makaman nukiliya tare da fadada karfinta na makamai masu...
    Kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hari kan dakarun gwamnatin Hayat Tahrir al-Sham (HTC) na kasar Siriya, wanda shi ne irinsa na farko a kan tsoffin kawayenta tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce ta sanya “bama-bamai” kan motar dakarun da HTC ke jagoranta a lardin Suwayda da ke kudancin kasar. Wannan dai shi ne harin farko da Daesh ta yi ikirarin doka kan sabuwar gwamnatin ta Siriya. Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) ta bayar da rahoton cewa, a yayin harin, wasu mambobi uku na runduna ta 70 na rundunar HTC sun jikkata, a yayin da suke sintiri yayin...