ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027
Published: 14th, November 2025 GMT
El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa.
Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.
Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar November 14, 2025এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Wamban Shinkafi Ta Amince Da Tinubu a 2027
Jam’iyyar (APC) a ƙarƙashin kungiyar Wamban Shinkafi ta jihar Zamfara, ta bayyana goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasa guda ɗaya na jam’iyyar a zaben 2027.
Wannan sanarwar ta fito ne daga wanda ya kafa kungiyar kuma jigo a jam’iyyar APC a Zamfara, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, yayin taron masu ruwa da tsaki na kungiyar da aka gudanar a birnin Gusau, babban birnin jihar.
A cewar Shinkafi, amincewar da aka bayar ta biyo bayan wani motsi da Yushau Mada, kwamandan kungiyar, ya gabatar, wanda kuma Asma’u Gusau, shugabar mata ta amince da shi ta biyu.
Dakta Shinkafi ya ce, gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu na tafiya kan turbar sauyi, ci gaba da gina ƙasa, tare da tabbatar da cewa yana da cikakken goyon bayansa ga jam’iyyar mai mulki. Ya kuma yi alkawarin ba da gudunmuwarsa wajen tabbatar da nasarar APC a dukkan matakai.
Ya bayyana cewa jam’iyyar APC a Zamfara ta kasance ɗaya mai haɗin kai, inda ya gargadi mambobi su guji ayyukan da za su cutar da jam’iyyar kafin da lokacin zaɓe.
Ya sake jaddada kudirinsa na kare ka’idojin dimokuraɗiyya da kyakkyawan shugabanci, yana mai cewa jagorancin Shugaba Tinubu ya kawo ci gaba mai ma’ana da gyare-gyare a fannoni daban-daban na ƙasar.
Shinkafi ya kuma yi alkawarin ci gaba da goyon baya ga shugabancin jam’iyyar APC a matakin ƙasa da jiha ƙarƙashin Tukur Danfulani, tare da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin mambobi.
Wannan amincewar da kungiyar Wamban Shinkafi Democratic Front ta bayar ga Shugaba Tinubu, na zuwa ne kwanaki goma bayan sashen jam’iyyar APC na Jihar Zamfara ya yi irin wannan sanarwa.
AMINU DALHATU/Gusau