Uwargidan Shugaba Xi Jinping na kasar Sin Peng Liyuan, da Sarauniya Letizia ta kasar Spain, wacce ke rakiyar Sarki Felipe na VI na Spain a ziyarar da ya kawo kasar Sin, sun ziyarci cibiyar gwaji ta kula da nakasassu ta Beijing a yau Laraba.

A cibiyar, Peng da Letizia sun saurari bayanan da aka yi kan ayyukan hidimar nakasassu kuma sun ziyarci wani babban sashen nune-nune na gasar wasannin lokacin hunturu ta nakasassu (Paralympic) ta Beijing da aka yi a shekarar 2022.

Daga nan suka je zauren baje kolin kayayyakin tallafa wa nakasassu da aka kera da manyan fasahohin zamani da kuma sashen karatu na kyauta, inda suka nazarci yadda ake amfani da kayayyakin tallafa wa nakasassu, da ayyukan karatu ga yara nakasassu, da kuma tsarin samar da kayayyakin da ba su da shinge a kasar Sin.

Peng ta ce sha’anin nakasassu yana bukatar hadin gwiwa da goyon baya daga dukkan bangarori domin taimaka musu wajen shiga cikin al’umma.

ADVERTISEMENT

Ta bayyana fatan cewa kasar Sin da Spain za su inganta mu’amala da hadin gwiwa don taimaka wa cimma burin nakasassu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa November 12, 2025 Daga Birnin Sin Ana Ci Gaba Da Raya Kasar Sin Daga Matakin Kasa Mai Sauri Zuwa Kasa Mai Inganci November 12, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Matakin Amurka Na Dakatar Da Ka’idar Fadada Jerin Wadanda Kasar Ta Takaita Fitar Wa Kayayyaki November 12, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a kasar Sin

এছাড়াও পড়ুন:

Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

Zhang Lei, mataimakiyar shugaban sashen yada labaru na kamfanin BaySystems reshen Sin da yankin arewa maso gabashin Asiya, ta kara da cewa, “A cikin shekaru 140 da suka gabata, mu kasance a nan ba mu taba barin ba, ko a lokacin wahala ko a’a. Wannan yana nuna irin kauna da alkawarin da wannan tsohon kamfanin Jamus mai shekaru 100 ke da su ga kasar Sin.”

A game da hakan, Frank Hammes, babban darektan kamfanin IQAir na kasar Switzerland ya bayyana cewa, bikin CIIE tamkar dakin gwaje-gwaje ne a gare mu, inda ban da baje kolin sabbin nasarorinmu, muna kuma iya samun martani daga masu sayayya.

Shi kuma Mr. Yu Feng, babban darektan kamfanin Honeywell da ke kula da harkokin kasar Sin, ya ce, masu sayayya wadanda da wuya a biya bukatunsu, alheri ne ga kamfanonin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, sabo da su ne suke taimakawa wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani.

“Za mu ci gaba da zuba jari a Sin har na karni 1”, “Za mu kara kusan shaguna 100 a Sin”. Nicolas Hieronimus shugaban kamfanin L’Oréal da Sandeep Seth, babban ma’aikacin kamfanin Tapestry sun fadi hakan yayin zantawar da wakilin CMG ya yi musu.

Hieronimus ya ce, “Sin ita ce kasuwa ta biyu mafi girma a duniya gare mu, kuma cibiyar kirkira ce mai karfi.” Seth kuma ya ce, “Kasuwar Sin ta zama filin gwajin sabbin dabaru.”

Wadannan kalamai sun nuna yadda suke amincewa da CIIE, tare da bayyana niyyar su ta ci gaba da fadada kasuwancinsu a Sin. (Lubabatu Lei da Amina Xu)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa November 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa November 10, 2025 Daga Birnin Sin Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin November 10, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa
  • Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
  • Xi Ya Gana Da Sarkin Sifaniya A Birnin Beijing
  • Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
  • Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
  • CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
  • An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 
  • Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo