Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan
Published: 14th, November 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi kira ga kasar Japan da ta janye kalaman baya-bayan nan da firaministar kasar ta furta, dangane da yankin Taiwan na kasar Sin, in ba haka ba, ta shirya girbar sakamakon danyen aikinta.
Lin Jian, ya yi kiran ne yayin taron ganawa da manema labarai na yau da kullum a yau Alhamis, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da kalaman firaministar Japan Sanaen Takaichi, game da yankin Taiwan na kasar Sin, wadanda kuma ta ki ta janyewa.
Lin, ya ce a baya-bayan nan Takaichi ta furta kalaman tayar da husuma, dangane da yankin na Taiwan, yayin da take tsokaci a majalisar dokokin kasarta, inda ta ambata yiwuwar aiwatar da matakan soji a zirin Taiwan. Lin ya ce kalaman na firaministar Japan ba su dace ba, sun kuma yi matukar keta manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da ruhin takardun siyasa hudu, wadanda Sin da Japan suka daddale, da ma yanayin gudanar da alakar kasa da kasa.
ADVERTISEMENTJami’in ya kara da cewa, wadannan kalamai na firaministar Japan, matukar tsoka baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, sun kuma kalubalanci moriyar kasar, tare da keta hurumin ‘yancin kan kasar ta Sin. Don haka Sin ke matukar adawa da su, kuma ba za ta amince da hakan ba. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Ban da wannan kuma, game da batun cewa kasashen kungiyar EU suna shirin cire na’urorin kamfanonin sadarwa na kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin suna aiwatar da ayyukansu bisa doka a nahiyar Turai na dogon lokaci, wadanda suka samar da kayayyaki da hidimomi masu inganci ga jama’ar Turai, tare da samar da muhimmiyar gudummawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da samar da ayyukan yi a nahiyar. Kasar Sin ta kalubalanci kungiyar EU da ta samar da yanayin gudanar da ciniki cikin adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin kasar Sin don magance wargaza amannar da kamfanonin suka yi wa nahiyar Turai kan zuba jari. (Zainab Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA