Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi
Published: 10th, November 2025 GMT
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa.
Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan dawo in sake taka leda a nan gaban masoyana kafin in yi ritaya.”
A shekarar 2021 Messi ya bar Barcelona bayan matsalolin kuɗi da suka dabaibaye kulob ɗin, inda ya koma Paris Saint-Germain (PSG) ta Faransa, kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa Inter Miami ta Amurka bayan shekaru biyu.
Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau takwas, ya ƙara da cewa ziyarar da ya kai Camp Nou ta sake jaddada masa irin farin cikin da yake ji a duk lokacin da yake wannan fili.
“Camp Nou wuri ne da yake sa ni farin ciki matuƙa. Ina fatan zan dawo ba wai kawai don yin bankwana ba, har ma don sake taka leda a matsayin ɗan wasa.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barcelona
এছাড়াও পড়ুন:
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025
Wasanni Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax November 6, 2025
Wasanni Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba November 2, 2025