Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA
Published: 16th, November 2025 GMT
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da tsokaci dangane da daftarin da Amurka ta gabatar, game da bukatar tsawaita ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a yankin Abyei na ko UNISFA a takaice. Sun, wanda ya yi tsokacin a jiya Juma’a, bayan jefa kuri’a a zaman kwamitin tsaron MDD kan daftarin, ya ce kasarsa ta damu game da yadda Amurka ta ingiza daftarin, wanda da ma ita ce ta gabatar da shi.
Ya ce a matsayin kasar dake sahun gaba wajen tallafawa tawagar ta UNISFA, Sin ta shiga an dama da ita a shawarwarin da suka shafi daftarin, to sai dai kuma daftarin ya fitar da wasu ma’aunai masu alaka da yanayin gudanar da harkokin siyasa a yankin na Abyei, tare da hade hakan da makomar tsawaita wa’adin aikin tawagar UNISFA. Kasar Sin ba ta gamsu da hakan ba, don haka ta kauracewa jefa kuri’a kan daftarin.
Sun Lei ya kara da cewa, yayin tattaunawa kan daftarin, da dama daga membobin kwamitin tsaron MDD sun gabatar da shawarwari masu ma’ana domin sake nazari. Kana a yayin shawarwarin ranar Alhamis a zauren kwamitin tsaron, dukkanin sassa sun amince kasar da ta gabatar da daftarin, ta shigar da shawarwarin dukkanin bangarori, maimakon rufe ido da ingiza shi yadda ta ga dama.
ADVERTISEMENTYa ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran membobin kwamitin tsaron MDD, wajen wanzar da hadin kai, da kawance tsakanin sassan kwamitin na tsaro, ta yadda za a kai ga tabbatar da tawagar ta musamman ta cimma nasarar sauke alhaki da nauyin dake wuyanta, da ma kara azamar wanzar da zaman lafiya, da tsaro a matakin kasa da kasa da na shiyyoyi. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: kwamitin tsaron
এছাড়াও পড়ুন:
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026
A nasa jawabin, Kwamishinan PPMF, Prince Aliyu Abdulrazaq, ya shawarci kwamitin da su gudanar da aikinsu da amana, gaskiya, da ƙwarewa, yana mai cewa dole ne amincewar da Hukumar ta yi musu ta bayyana a sakamakon aikinsu.
Da yake magana a madadin kwamitin, Jagoran Kwamitin, Dr. Haruna Danbaba, ya tabbatar wa Hukumar cewa za su bi dukkann ka’idojin da Ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa, tare da tabbatar da cewa ba’a samu jinkirin wajen gudanar da aikin kwamitin ba.
Ƙaddamar da kwamitin na daga cikin manyan matakai na farkon shirin NAHCON domin Hajjin 2026, kuma ana sa ran fara aiwatar da muhimman ayyuka nan take.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA