Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu.
Published: 15th, November 2025 GMT
Shugaban kasar iran Msud pezeshkiyan ya kira prime ministan Iraqi mohammad shia al-sudani ta wayar tarho domin taya shi murnar kammala zaben yan majalisar dokoki da aka yi a kasar cikin gagarumar nasara da kuma kwanciyar hankali da tsaro.
Kasashen iran da Iraqi kasashe ne masu makwabtaka da juna kuma sakamakon da aka fitar na zaben yan majalisa da aka gudanar zai taka muhimmiyar rawa wajen kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu,
Ana sa bangaren Al-sudani ya jaddada cewa zaben ya nuna irin yadda alummar iraki suka yi riko da demukuradiya, kuma sakamakon zaben zai taimakawa kasar wajen gudanar da ayyukan ci gaba da gina kasar da gwamnatin tasa a gaba,
Shi ma shugaban iran pezeshkiyan ya jinjina game da yadda aka gudanar da zaben kuma ya bayyana shi a matsayin babbar nasara,da ya kare mutuncin mutanen iraki, kuma yayi fatan cewa dangantakar dake tsakanin za ta kara zurfi a sauran shekaru masu zuwa.
Dukkan shuwagabannin sun nuna aniyarsu ta kara fadada dangantaka dake tsakanin da kuma yin aiki tare a yankin ,kuma sudani ya yi fatan ganin an kara karfafa dangantaka a bangarorin daban-daban a tsakaninsu
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka M D D Ta yi Tir Da Harin Da Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Suka Kai A Masallaci A Yammacin kogin Jodan November 15, 2025 Mali ta Dakatar da Tashoshin Talabijin na Faransa TF1 da LCI November 15, 2025 Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin Trump November 15, 2025 AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro November 15, 2025 Iran ta bukaci duniya ta gaggauta daukar mataki a Sudan November 15, 2025 EU ta nemi Isra’ila ta dauki mataki kan tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan November 15, 2025 Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin November 14, 2025 Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire November 14, 2025 Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza November 14, 2025 Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi kira ga jami’an diplomasiyyar kasar Iran da su kai karar shugaban kasar Amurka Donald Trump a kotunan kasa da kasa, bayan da ya yi furuci da cewa shi ne ya jagroanci harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kawo wa Iran.
Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma kara da cewa, ya kamata a fitar da bayani na yin tir da wannan maganar sannan kuma a kai kara a cibiyoyin duniya.
Da ya koma yin Magana akan hijabi kuwa, limamin na Tehran ya bayyana cewa, sanya hijabi ga mata,hukunici ne da addini da kuma doka, sannan ya ambato wani marubuci dan Amurka da yake cewa: Idan har matan Iran su ka cire suturar hijibi to sun fada cikin tarkon makarkashiyar kungiyar leken asirin Amurka ( C.I.A) wacce ke nufin kifar da tsarin musulunci da rusa Iran.
Limamin ya kuma yi kira ga matan da su sake tunani akan kare addininu da kuma kasarsu, wadanda ba su sanya suturar hijabi su sauya tunani.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka November 14, 2025 Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu November 14, 2025 Abdoulaye Diop: ‘Yan Tawaye Ba Za Su Iya Mamaye Dukkan Kasar Mali Ba November 14, 2025 Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg November 14, 2025 MDD ta nuna damuwa game da rahotannin kisan gilla a El Fasher November 14, 2025 Rasha Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka November 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci