2025-11-14@12:08:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7845

«da dabino a duniya»:

    Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take samar da tan miliyan 1.5 a kowace shekara. Bayannin ya zayyana Kasashe goma mafiya samar da dabino a duniya wadanda su ne Masar, Saudiyya, Iran, Aljeriya, Pakistan, Iraki, Sudan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman, da Tunisiya, wanda ya nuna Iran na cikin kasashe na uku na farko. Kuma a yadda Iran ke fitar da tan 430,000 na dabino a kowace shekara, hakan ya sa ta kasance ta farko wajen fitar da dabino a duniya, sai Saudiyya da tan 390,000 sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da tan 330,000. Fitar da dabino daga Iran an kiyasta yana samar...
    Rasha, China, da wasu kasashen Larabawa da dama sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yaki da kuma rashin wani muhimmin matsayi ga Hukumar Falasdinu bayan yakin Gaza da aka gabatar a daftarin kudirin shirin tsagaita wuta na Shugaba Donald Trump na Amurka. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar kasashen sun yarda cewa tattaunawa ta kai ga cimma yarjejeniyar, amma rarrabuwar kawuna tsakanin Washington da wasu membobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, bayan fiye da shekaru biyu na kisan kare dangi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ya kamata a amince da kudurin nan take, yana mai jaddada bukatar gaggauta amincewa da shirin. Daftarin farko na Amurka, wanda aka rarraba a makon da ya gabata, ya yi...
    Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. Duk da shakkun da Amurka ta yi, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsawaita wa’adin aikin tawagar ta MINUSCA, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa ranar 15 ga Nuwamba, 2026. Duk da haka, Majalisar ta nuna yiwuwar rage wa’adin saboda shiryen shiryen zaben da ake yi a shekarar 2026. An amince da kudurin da kuri’u 14 sai kuma kin amincewa daga Amurka. An samar da tawagar ta MINUSCA a watan Afrilun 2014 don kokarin kawo karshen yakin basasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan...
    Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya. A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Ministocin Harkokin Wajen Iran da Turkiyya sun yi nazari kan dangantakar kasashen biyu kuma sun jaddada muhimmancin karfafawa da bunkasa dangantaka a dukkan fannoni masu amfani. Yayin da yake yaba wa kokarin rage tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada muhimmancin karfafa shawarwari don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a...
    Portugal ta shiga wasan ne da kwarin gwiwar cewa nasara za ta tabbatar mata da gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka, Kanada da Mexico. Sai dai kwallaye biyu na Troy Parrott suka tarwatsa burinsu a Dublin. Duk da haka, Portugal har yanzu tana saman rukunin F da maki biyu a gaban Hungary, kuma za ta iya kammala tikitin shiga gasar idan ta doke Armenia a ranar Lahadi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025 Wasanni Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25 November 13, 2025 Wasanni Nijeriya Za...
    Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta yi gargadi cewa yanayin da tattalin arzikin da kasar nan ke ciki ya jefa kafofin yada labarai cikin wani mawuyacin hali. Kungiyar ta kuma yi kira da a soke dokokin da ke takura ‘yancin ‘yan jarida. Shugaban NGE, Mista Eze Anaba, ya bayyana haka ne a jawabin maraba da ya yi a Taron Editocin Nijeriya Gabadaya (ANEC) mai taken “Dimokuradiyya, Gudanarwa da Hadin Kan Kasa: Rawar da Editoci ke Takawa,” wanda aka gudanar a dakin taro na Tarayya, Abuja. Ya yi nanata cewa halin tattalin arziki a kasar ya tilasta wasu gidajen jarida rufewa, yayin da wasu da ke kokarin ci gaba da aiki ba sa iya biyan albashin ma’aikata. A cewarsa, wannan lamari ne...
    Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na tsawon shekaru biyar masu zuwa. Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labaru, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a. An kama ’yan Najeriya 3 a Kenya kan zargin aikata damfara Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 An fara nada Marwa a watan Janairu 2021 ta hannun Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Buba Marwa a muƙamin a watan Janairun 2021, bayan ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi daga shekarar 2018...
    Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bayyana jin daɗinta da wannan hukunci, inda Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Maude Kabir, ta bakin mai taimaka masa a fannin yaɗa labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim, ya ce hukuncin ya tabbata ne don tabbatar da adalci kamar yadda doka ta tanada. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025 Manyan Labarai Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya November 14, 2025 Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025
    An kama ’yan Najeriya uku a rukunin gidaje na Mwaliko da ke garin Mwea a ƙasar Kenya, bisa zargin su da damfara ta intanet. Rahoton da wata kafar labarai a Kenya mai suna Tuko News ta fitar ya ce Hukumar Binciken Laifuka ta ƙasar (DCI) ce ta kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba. Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan Waɗanda aka kama sun haɗa da Peter Chukwujekwu, Alazor Chukulute Sunday, da Nnalue Chiagozie Samwe. A cewar rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, an kama su a gidansu bayan jama’a sun kai ƙorafi kan take-takensu musamman da daddare a cikin ginin. DCI...
    Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai. Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin...
    Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis. WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin yankin, da safiyar ranar. HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ce rubuce-rubucen da aka fesa da fenti sun haɗa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci. Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan zargin. Babu rahoton rauni...
    A bisa wannan dalilin, ya kuma zama waji, manyan hafsohin tsaron su mayar da hankali, wajen ingnata jin dadi da walwalar dakarun sojin, musamman duba da cewa, manyan hafsoshin tsaron, su ba baki ne, kan wadannan kalubalen ba, domin kuwa kafin nada su, a baya an nada su kan makamai da ban da ban. Kwarewar da kuma ilimin da suke da shi, a aikin soji, abu ne da zai taimaka masu wajen sauke nauyin da aka dora masu. Abu na biyu shi ne, akwai bukatar a tsakaninsu, su hada karfi da karfe, domin su samu nasarar tunkarar aikin da ke a gabasu na tabbatar da tsaro a kasar, ba wai su rinka yi aiki, a daidaikunsu ba. Kazalika, dole na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani.   Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a duk lokacin da aka ce damina ta tattara inata intat. Shin ko wadanne kalubale ne ke hana manoma shiga noman rani bayan damuna ta wuce? NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi kira ga kasar Japan da ta janye kalaman baya-bayan nan da firaministar kasar ta furta, dangane da yankin Taiwan na kasar Sin, in ba haka ba, ta shirya girbar sakamakon danyen aikinta. Lin Jian, ya yi kiran ne yayin taron ganawa da manema labarai na yau da kullum a yau Alhamis, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da kalaman firaministar Japan Sanaen Takaichi, game da yankin Taiwan na kasar Sin, wadanda kuma ta ki ta janyewa. Lin, ya ce a baya-bayan nan Takaichi ta furta kalaman tayar da husuma, dangane da yankin na Taiwan, yayin da take tsokaci a majalisar dokokin kasarta, inda ta ambata yiwuwar...
      ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana November 13, 2025 Daga Birnin Sin Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya November 13, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu November 13, 2025
    Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kaduna, ta ƙone fiye da tan 52,000 na miyagun ƙwayoyi a bainar jama’a a ƙauyen Karofi da ke Kufena, a kan tsohuwar hanyar Birnin Gwari da ke Zariya. An gudanar da bikin ƙone kayan ne a wannan Alhamis ɗin, inda Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd.), Shugaban NDLEA kuma Babban Jami’in Gudanarwa, ya jaddada cewa hukumar ta duƙufa domin kawar da barazanar miyagun ƙwayoyi daga cikin al’umma. Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe ya rasu Ya bayyana cewa, “Miyagun ƙwayoyi suna lalata tarbiyyar matasa a hankali, ba tare da an farga ba. Kowace tan ɗaya da aka ƙone, an ceto rayukan mutane da...
    Shugabar kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya (IOC), Kirsty Coventry, ta halarci bikin bude gasar wasannin kasa ta Sin karo na 15 a lardin Guangdong da yammacin ranar 9 ga Nuwamba. A ranar 12 ga wata kuma, Coventry ta yi wata hira ta musamman da ‘yar jarida daga babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a nan birnin Beijing. Yayin hirar, Coventry ta bayyana cewa, gasar wasannin kasar Sin ta wannan karo tana da babbar ma’ana. Ta ce yayin da take ziyarar aiki a Sin, ta yi tattaunawa da dama, ciki kuma har da ganawa da shugaba Xi Jinping. Shugaba Xi ya ce mokamar bunkasuwar yankin gabar tekun Guangdong-Hong Kong-Macao, ba tsara manufofin da za a iya...
    Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya musanta zargin cewa yana da wani saɓani da rundunar sojin Najeriya, yana mai cewa batun rikicin fili ne ya haɗa jami’ansa da wasu sojoji sa-in-sa da a yanzu ake faman cece-kuce a kai. Wike ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, inda ya nanata cikakkiyar girmamawar da ya ce yana yi wa sojoji, kuma babu wata gaba a tsakaninsu. Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe ya rasu Nijeriya ta doke Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya Ya ce abin da ya faru dai rikici ne da ya shafi wani mutum ɗaya mai fili da ake rigima a kai saboda mallakarsa ba bisa ka’ida ba, saboda ba rikici...
    Allah Ya yi wa Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe, rasuwa a daren nan na Alhamis. Wakilimu ya ruwaito, basaraken ya amsa babban kiran ne a yayin da ake gudanar da sallar Isha’i. Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne Hakimin Kusada, kuma suruki ne ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman. Haka kuma, shi ne kakan Magajin Garin Katsina, Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir. Ana sa ran za a bayyana lokacin da za a yi jana’izarsa nan gaba. Karin bayani zai biyo baya…
    Da wadannan shaidu na zahiri, muna iya cewa himmar kamfanonin kasar Sin ta fuskar kirkire-kirkiren fasahohi, ya sanya hajojin kasar zama masu tafiya da yanayin zamani, wanda har kullum ake ta kokarin daidaita ci gabansa da bangaren kare muhalli, da aiwatar da matakai na inganta yanayin duniya. Tun daga yankin kudu maso gabashin Asiya zuwa Turai, daga Latin Amurka zuwa gabas ta tsakiya har Afirka, ana ta ganin karuwar ababen hawa masu aiki da lantarki kirar kasar Sin, a wani yanayin dake shaida kwarewar kamfanonin kasar a fannin kirkire-kirkire fasahohi na zamani, wanda daga karshe ke dacewa da samar da hajoji irin wadanda kasuwannin duniya ke alfahari da kuma bukatar su. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin...
    Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles ta doke tawagar ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka fafata a yammacin wannan Alhamis. Wasan wanda aka soma da ƙarfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat a Morocco, ya bai wa Super Eagles damar lallasa The Panthers har ci 4-1. Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya Wannan sakamakon ya bai wa Nijeriya nasarar kaiwa zagayen ƙarshe a wasan cike gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026. Akor Adams ne ya fara ci wa Super Eagles ƙwallo a minti na 78, amma...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2 November 13, 2025 Wasanni Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25 November 13, 2025 Wasanni Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau November 13, 2025
    An gudanar da taro mai taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa”, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya dauki nauyi, a Johannesburg dake Afirka ta Kudu a ranar 11 ga wata. Jigon taron shi ne, “Matasa su tattauna kan tsarin shugabancin duniya, kuma su hada kai don samar da makoma irin ta zamani ga Sin da Afirka.” A gun taron, shugaban CMG, Shen Haixiong ya gabatar da rubutaccen jawabi, inda ya bayyana cewa, bai kamata matasan Sin da Afirka su shiga cikin harkokin shugabancin duniya kawai ba,matasa na da muhimmanci matuka wajen tsara tsarin shugabancin duniya. Ya kara da cewa, a ko da yaushe, CMG yana mayar da hankali kan hada kan matasan duniya, kuma yana...
    Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya buƙaci jam’iyyar PDP da ta ɗage babban taronta da ta shirya gudanarwa tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo. Saraki ya ce ci gaba da shirin gudanar da taron duk da irin umarnin dakatarwa da kotuna suka bayar zai ƙara ta’azzara rikicin jam’iyyar sannan ya jefa ta cikin matsaloli a nan gaba. An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya Ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan karɓar baƙuncin ’yan kwamitin amintattun jam’iyyar ƙarƙashin shugabancin Ambasada Hassan Adamu, a gidansa. Tawagar ta...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karfafawa matasa masanan harkokin kasar Sin gwiwar zama manzonni domin inganta fahimtar juna tsakanin al’ummomin Sin da na sauran sassan duniya. Xi ya bayyana haka ne cikin amsar wasikar matasa masanan harkokin Sin 61 daga kasashe 51, wadanda za su halarci babban taron duniya kan harshen Sinanci da za a yi daga gobe Juma’a zuwa Lahadi, a birnin Beijing. Xi Jinping ya bayyana farin cikin cewa ba Sinanci da al’adun Sin kadai wadanan matasa ke kauna ba, har da inganta fahimta game da harkokin Sin da koyi da juna tsakanin al’ummomi. Ya kuma karfafa musu gwiwar ci gaba da gabatar da ainihin kasar Sin daga bangarori daban daban ga sassan duniya, tare da bayar...
    Adai dai lokacin da bikin cika shekaru 55 na kulla hulda diplomsiya tsakanin Iran da China ke kara karatowa ta , dukkan kasashen biyu suna kokarin ganin sun kara karfafa alakar dake tsakaninsu , Ambasado Ahmad Fazli ya jaddada game da muhimmancin karfafa dangantaka a mataki na kasa da kasa, bisa hangen nesa da girmama juna. Ganawar da aka yi tsakanin jakadan kasar iran a bejin Rahmani Fazli da Miao Deyu matakimakin ministan harkokin wajen kasar china ta nuna aniyar kasashen biyu na kara karfafa dangantakarsu ta dogon lokaci. A lokacin ganawar da mataimakin ministan harkokin wajen kasar china rahmani ya jadda muhimmancin kara dankon zumunci tsakanin iran da china, musamman ma yin muhimmacin aiki tare a yankin,  don haka...
    NDLEA ta bayyana cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar wannan matsala, tare da wayar da kan jama’a da kula da masu fama da shan ƙwayoyi, domin kare tsaron rayuka da zaman lafiya a ƙasar nan. Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilin shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammadu Buba Marwa (mai ritaya), wato Kwamanda Muhammadu Tukur; wakilin Gwamnan Jihar Kaduna, da wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, wato Alhaji Umar Muhammad Fagacin Zazzau. Haka kuma, Kwamandan NDLEA na Jihar Kaduna da wakilai daga ‘yansanda, sojoji, DSS, da sauran hukumomin tsaro sun halarta. Masu jawabi a wajen taron sun nuna farin ciki da wannan nasara, tare da yabawa jami’an tsaro, alƙalai, da jama’ar gari bisa...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa November 12, 2025 Daga Birnin Sin Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing November 12, 2025 Daga Birnin Sin Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa November 12, 2025
    A yammacin wannan Alhamis ce tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles za ta fafata da ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026. Wasan da za a buga da karfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat, Morocco, zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0. Wannan wasan dai shi ne zai tabbatar da nasarar Nijeriya na samun tikitin shiga gasar kafin haɗuwar ta da Kamaru ko Dimokuraɗiyyar Congo a ranar Lahadi.
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa Abuja da wasu sassan ƙasar da ma ƙetare. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Atiku ya karyata ba sojan da ya yi takaddama da Wike kyautar motar SUV Sanarwar ta bayyana cewa “an tari hanzarin ababen zargin ne da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar 12 ga watan Nuwamba. “A wannan lokaci ne jami’an sashen Ɗan Magaji da...
    Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila da Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ziyarci zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis domin shaida sauya sheƙar ƴan majalisa biyu daga NNPP zuwa APC. Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon. Abdulmumin Jibrin, wanda ke wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, da Hon. Sagir Koki, wakilin Kano Municipal. A cikin wasiƙunsu da Kakakin Majalisar Abbas Tajudeen ya karanta, sun bayyana rikici mai sarƙakiya da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar NNPP a matsayin dalilin barin jam’iyyar zuwa APC. ADVERTISEMENT Duk da jayayya da Hon. Kingsley Chinda daga bangaren marasa rinjaye, wanda ya dage wajen ɗaga batun sanarwar a lokacin...
    Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa. Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin...
    1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo  Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba. Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara. Wanda hakan yake nuna rashin ‘yan wasa masu ƙwarewa da zasu ci kwallon, wanda ya sa ake dogaro da wanda suka kwana biyu kamar Rabiu Ali, yana iya kokarinsa amma ba aikinsa ba ne kuma tsufa...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa na X a ranar Alhamis, Atiku ya bayyana labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsagwaronta ba tare da wata hujja ba. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal Ibe ya bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labari da...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa na X a ranar Alhamis, Atiku ya bayyana labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsagwaronta ba tare da wata hujja ba. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal Ibe ya bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labari da...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa Refael Grossy, Iran din ta yi aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Grossi ya rubutawa Iran wasika a ranar 7 ga watan Nuwamba na 2025 yana mai cewa; Bayar da dama ga hukumar domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin Iran, yana...
      “Mun yi imani cewa ‘yan wasanmu tare da kwarewar da suke da ita, zai janyo wa Nijeriya abin alfahari, ba kawai a ranar Alhamis ba, har ma a duk tsawon wasannin share fagen da zamu buga”, hakan yasa muke da kwarin gwuiwar cewar kasarmu za ta iya samun tikitin shiga gasar cin kofin Duniya,” in ji Gusau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle November 13, 2025 Manyan Labarai Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su November 13, 2025 Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da...
    3.LukaModrić (Croatia) 4.ManuelNeuer (Jamus) 5.VirgilvanDijk (Netherlands) 6.HarryKane (Ingila) 7. RobertLewandowski (Poland) 8.SonHeung‑min (Koriya ta Kudu) 9.MohamedSalah (Masar) 10.Luis Suárez (Uruguay)   Tasirinsu a kungiyoyi da ƙasa na da matukar muhimmanci, kuma 2026 na iya zama damarsu ta ƙarshe ta haskakawa a babban kofin ƙwallon ƙafa mafi daraja.   Biyu da suka yi fice acikin 10, sun hada da Cristiano Ronaldo (Portugal). Yana da shekaru 41, ya tabbatar da cewa wannan zai zama gasarsa ta ƙarshe, yana da niyyar ƙara Kofin Duniya a cikin jerin kofunan da ya taɓa lashewa.   LionelMessi (Argentina). Bayan ya lashe gasar cin kofin duniya ta 2022, ɗan wasan mai shekaru 39 ya nuna cewa gasar 2026 a Arewacin Amurka na iya zama damarsa ta ƙarshe...
    Gidauniyar  fadakar da al’umma akan dokoki da ka’idoji ta Nijeriya ta kaddamar da kwamiti a jihar Nasarawa domin aiwatarwa da sa ido kan shirin mata, zaman lafiya da tsaro, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen gina zaman lafiya a cikin jihar. Daraktan gudanarwa na gidauniyar, Mista Peter Maduoma, ne ya bayyana hakan a Lafia yayin taron horarwa na kwanaki uku da aka shirya ga masu ruwa da tsaki kan batun mata, zaman lafiya da tsaro, wanda gidauniyar ta shirya. Mista Maduoma, wanda Jami’in Shari’a da Albarkatun Ƙasa na Gidauniyar, Mista Ifeyinwa Akwiwu, ya wakilta, ya ce shirin wani ɓangare ne na aikin gidauniyar mai taken “Ƙarfafa tsarin adalci ta hanyar kare haƙƙin ɗan adam da bunƙasa zaman lafiya a Najeriya.”...
    LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ministan FCT ya je filin mai lamba 1946 a ranar Litinin inda ya zargi sojoji da hana jami’ai daga Ma’aikatar Kula da Ci Gaban FCT aiwatar da umarnin dakatar da aiki a filin.   Ana zargin cewa, filin yana da alaka da tsohon Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo (mai ritaya). Don haka, sojojin da ke wurin suka hana ministan shiga wurin, wanda hakan ne ya haifar da saɓanin. Daga baya, Wike ya yi ikirarin cewa, masu ginin ba su da takardu masu inganci ko izinin doka don gina wurin.   Da yake mayar da martani ga lamarin, Matawalle ya ce, ya kamata a magance lamarin ta hanyoyin da suka dace maimakon ta...
    Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.   Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na Ƙasa da Ƙasa na Nijeriya, Suleja, Jihar Neja; Millennium Tower, Abuja; Ginin Hukumar Haraji ta Tarayya a Jihar Abia; Hedikwatar Dakin karatu na Ƙasa, Abuja; Kamfanin Masana’antar buga Labarai na Nijeriya, Kaduna; Ginin Masaƙa ta Kaduna; da Kamfanin Narka Alluminium na Nijeriya, Jihar Delta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule...
    Wani kamfanin hakar ma’adinai na Biritaniya ya sanar a jiya Laraba cewa, an gano tarin zinari a karkashin kasa a gundumar Kakamega da ke yammacin kasar Kenya, wanda darajarsa ta kai sama da dalar Amurka biliyan 5.28 kwatankwacin shilin kasar Kenya biliyan 683, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi ga fannin hakar ma’adinai na kasar. Kamfanin ShantaGold Kenya Limited ya sanar da cewa, an gano hakan ne a hanyar Lerehanda, wanda ya ratsa cikin kananan hukumomin Kakamega da Fihiga, bayan kwashe tsawon shekaru ana bincike. A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce aikin yana da nufin samun lasisin da ya dace don hakar albarkatun zinare a mahakar Isolo-Bushiangala don...
    Hamas ta tabbatar da cewa tana aiki da alƙawarinta na amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma nauyin da ke kanta na ƙasa da na jinƙai ga al’ummar Falasɗinu. Ta yi kira ga masu shiga tsakani, ƙasashe masu garantin, da kuma al’ummar duniya da su ɗauki mataki nan take da muhimmanci don tilasta wa mamaya ta dakatar da take haƙƙoƙinta, ta ɗage killacewar, ta ba da damar shigar da agaji, da kuma tabbatar da haƙƙin al’ummar Falasɗinu na tsaro, ‘yanci, da mutunci. Ƙungiyar ta buƙaci kawo ƙarshen kisan kiyashi da take haƙƙoƙin al’ummar Falasɗinu a Gaza, da bin layin janyewa na ɗan lokaci da aka amince da shi, da kuma hana duk wani ƙarin kutse ko keta haƙƙoƙi. Ta kuma...
    Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
    Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun yi gargadi a jiya Laraba cewa, miliyoyin mutane a yankuna akalla 12 da ke fuskantar rikici a duniya, ciki har da Sudan da zirin Gaza, na fuskantar barazanar yunwa, tare da gabatar da bukatar gaggawa na samar da kudade don magance gibin tallafin abinci, sakamakon raguwar tallafin da kasashen duniya ke bayarwa. A cikin wani rahoto na hadin gwiwa, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) sun sanya kasashen Haiti, Mali, Sudan ta Kudu, da Yemen cikin kasashen da ke fuskantar barazanar yunwa. Rahoton ya kuma bayyana halin da ake ciki na yunwa a wasu kasashe shida wato Afganistan, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Myanmar, Najeriya, Somaliya, da Syria, a...
    A kwanakin nan ana samun raguwar kujerun maniyyata aikin Hajji daga Najeriya, abin da ya jawo fargaba ga masu shirin zuwa kasa mai tsarki da kuma masu hidimar su. A da, Najeriya na samun kujeru sama da dubu casa’in daga gwamnatin Saudiyya, amma cikin shekaru kadan da suka gabata adadin ya ragu zuwa kusan dubu sittin da biyar.   Kazalika a yanzu gwamnatin na saudiyya ta bayyana cewa idan har maniyyatan Najeriya basu biya cikakken kudaden hajjin bana ba, to akwai alamun sake rage yawan kujerun zuwa dubu hamsin. NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Ko yaya...
    Kungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta bukaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Najeriya. Aminiya ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne sananne cewa ana aikata laifuka a ƙarƙashin dokokin kasa da kasa a Najeriya, musamman laifukan da suka shafi cin zarafin bil’adama, laifukan yaki da kuma kisan kare dangi.” Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano Ya kara da cewa: “Kalma guda da hukumomin Najeriya da masu bincike na kasa da kasa...
    Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025. Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar. Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana Super Falconets ta lashe gasar WAFU ta ’yan ƙasa da shekaru 20 Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 na Naira tiriliyan 59.99 ya bar giɓin naira tiriliyan 1.15 wanda dole ne a cike ta hanyar nemo rancen a cikin gida. Sanatoci sun amince cewa rancen ya zama dole domin ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati da tabbatar da nasarar kasafin kuɗin 2025,...
    Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar SDP da Wilson Iliya Yange na jam’iyyar PDP, da Honarabul Simon Na Allah na jam’iyyar LP, sai Ibrahim Musa na jam’iyyar ADC daga shiyya ta biyu shi ne Sakataren kwamitin.   Da yake jawabi bayan kaddamar da kwamitin, Shugaban jam’iyyar na jihar, Elder Patrick Ambut, ya shawarci mambobin da su kasance masu jajircewa tare da tabbatar da adalci da gaskiya a cikin aikin da aka...
    Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe.   Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma Turanci ya kamata ya zama babban harshen koyarwa tun daga firamare har zuwa makarantun gaba da sakandare don inganta fahimta da gogayyar ilimi a tsakanin Daliban Nijeriya da takwarorinsu na duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi November 12, 2025 Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya...
    Uwargidan Shugaba Xi Jinping na kasar Sin Peng Liyuan, da Sarauniya Letizia ta kasar Spain, wacce ke rakiyar Sarki Felipe na VI na Spain a ziyarar da ya kawo kasar Sin, sun ziyarci cibiyar gwaji ta kula da nakasassu ta Beijing a yau Laraba. A cibiyar, Peng da Letizia sun saurari bayanan da aka yi kan ayyukan hidimar nakasassu kuma sun ziyarci wani babban sashen nune-nune na gasar wasannin lokacin hunturu ta nakasassu (Paralympic) ta Beijing da aka yi a shekarar 2022. Daga nan suka je zauren baje kolin kayayyakin tallafa wa nakasassu da aka kera da manyan fasahohin zamani da kuma sashen karatu na kyauta, inda suka nazarci yadda ake amfani da kayayyakin tallafa wa nakasassu, da ayyukan karatu...
    Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi da kuma samar da nagartattun hanyoyin warkarwa ta yadda jami’an lafiya za su nakalci sahihin zabin da za su yi amfani da shi wajen magance matsalolin rashin haihuwa mabambanta, da kuma tabbatar da cimma muradun samun haihuwar.” Tabbas, kamar yadda kasar Sin take da sa kwazo cikin abubuwan da take yi, ina da yakinin za a zurfafa wannan bincike domin cike gibin da aka gano...
    Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata. An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi da Ramotalahi Kareem suka zura ƙwallaye uku da suka bai wa Najeriya nasara. An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Super Falconets ke lashe wannan kofin tun lokacin da aka fara gasar. Ghana, wadda ta lashe kofin a shekarar...
    Wakil ya ce, bayan samun rahoton, tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin jami’in ‘yansanda na sashin, CSP Holman Simon, sun ziyarci wurin nan take domin tantance irin barnar da aka yi.   Ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Alhassan Jibrin, wanda aka fi sani da Babani Biri, matashi mai shekaru 20 mazaunin yankin Danjuma Goje, Bauchi, ya jefar da wayarsa ta Android a wurin da aka yi fashin.   “Binciken ya kai ga kama wasu mutane uku: Lawan Adamu, da Lawan Idris, mai shekaru 20, da Muhammad Yau, wanda aka fi sani da Madugu, mai shekaru 22, duk mazauna Bauchi ne” in ji CPRO ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko biyu masu zuwa. Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da Gabon Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro “Eh, tabbas wannan shi ne Kofin Duniya na ƙarshe da zan halarta. Zan kai shekara 41, kuma ina ganin wannan ne lokacin da ya dace na ajiye takalmi,” in ji shi a wata tattanawa...
      A jawabinsa, ministan ya bayyana cewa, binciken jin ra’ayin ‘yan kasa a fannin kiwon lafiya da aka gudanar a shekarar 2023, 2024, da 2025 ya nuna sakamako mai karfafa gwiwa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025
    Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya gargaɗi ’yan wasan ƙasar da su guji tafka kura-kurai a wasan da za su buga da Gabon a ranar Alhamis. Ekong ya yi wannan gargaɗi ne kafin fara atisayen ’yan wasan a safiyar Talata, a yayin da suke ci gaba da shirin fafatawar neman gurbin shiga Kofin Duniya na 2026. Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro ’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa Super Eagles za ta kece raini da Panthers of Gabon a wasan da ake sa ran zai kasance mai matuƙar muhimmanci wanda shi zai tabbatar da matsayin Najeriya na samun tikitin...
    Daga Bashir Meyere Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025. Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje. Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wanda mataimakinsa Sanata Haruna Manu ya wakilta, ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 59.99 da Majalisar ta amince da shi, ya karu da Naira tiriliyan 5.25 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 54.74 da gwamnatin tarayya ta fara gabatarwa. Ya ce an riga an amince da Naira tiriliyan 12.95 a cikin kasafin, wanda hakan ya...
    An umarci shugaban karamar hukumar da ya mika harkokin majalisar ga mataimakiyarsa, Mrs Victoria Okolo, har sai an kammala binciken.   Majalisar ta bai wa kwamitin binciken wata daya don kammala aikinsa tare da bayar da rahoto kan matakin da ya dace. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
    Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji  don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba. Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin bakin jini da Isra’ila ta yi a duniya bayan kisan kare dangi da ta yi a yankin Gaza, da ta fara tun daga watan Oktoban shekara ta 2023, wannan yasa telaviv ta bukaci abokiyarta ta ci gaba da aiwatar da aniyarta. Ana sa bangaren jami’an gwamnatin falasdinu sun yi gargadin cewa duk wani mataki da zaa dauka na kokarin canza wani dan mamaya da wani,...
    Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya  Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan. Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma  kara yin aiki tare tsakanin Riyadh da Tehran, bisa la’akari da irin tattaunawa da aka yi a shekarar bara, diplomasiya ta addinin dake kewaye da aikin hajji na shekara –shekara ta kasance mai muhimmanci don samar da zaman lafiya . Ali reza Rashidiyan shugaban hukumar aikin hajji ta kasar iran ya kai ziyara kasar saudiya ne domin rattaba hannu kan shirye- shiryen jerjejeniyar aikin hajji da zaa yi a...
    Ministan Tsaron nageriya, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa tare da shugabancin rundunar soji za su kare kowane jami’i da ke bakin aikinsa bisa doka. Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ma’aikatar tsaro kan bikin tunawa da Sojojin Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanarwa a Cibiyar Tsaron Ƙasa (National Defence College), Abuja, a ranar Laraba. Kalamansa na zuwa ne bayan rikicin da ya barke a bainar jama’a tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima, kan wani fili da ke Abuja da ake zargin mallakar tsohon Shugaban Rundunar Sojan Ruwa, Vice Admiral Zubairu Gambo (mai ritaya) ne. Ya ce: “A Ma’aikatar Tsaro,...
    Kasashen Iran da Pakistan sun yi kira da a yi aiki tare da ya hada da kara dankon zumunci tsakanin yan majalisar domin tunkarar babban makiyinsu, kuma sun yi tir da matakin kai hare-hare da Isra’ila ke yi da kuma ta’adanci a yankin A wani bayani da suka fitar a wata ganawa da suka yi a bayan taron yan majalisu da aka gudanara a yau laraba a birnin Islam Abad, mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar iran Ali Nikbad da takwaransa na kasar Pakistan sardar ayaz sadiq sun jadda game da matsayin kasashen na irin gudunmawa da suke badawa a yankin dakuma lammuran da suka shafi kasashen musulmi Nikbad ya bayyana gamsuwarsa game da sanin ya kamatan kasar Pakistan kuma yayi...
      Kafin ganawar ta su, shugaba Xi ya shiryawa sarki Felipe VI bikin maraba da zuwa. Kana bayan tattaunawar, shugaba Xi da sarki Felipe VI, sun halarci bikin sanya hannu kan takardun hadin gwiwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu November 12, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam November 11, 2025 Daga Birnin Sin Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa November 11, 2025
    Babban abin lura a nan shi ne irin alfanun da Nijeriya za ta samu tare da sauran kasashen Afrika daga wannan bikin baje koli. Na farko dai Nijeriya da sauran kasashen Afirka za su kara kaimi wajen noman irin waɗannan amfanin gona domin fitar da su zuwa Sin, hakan kuwa zai kara samar da aikin yi ga dubban ‘yan Nijeriya, abin da zai habaka kudaden shiga ga kasa. Alfanu na biyu kuma shi ne fadada damar ingantawa da kara daga darajar irin wadannan amfanin gona da Nijeriya ke samarwa. Sannan kuma akwai batun bunkasa dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka. Sabo da haka wannan irin lamari na bude kofar cudanya tsakanin Sin da sauran kasashen...
    Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tare da shugabannin Rundunonin Sojin Najeriya, za su ci gaba da kare duk wani jami’i da ke gudanar da aikinsa bisa doka. Badaru, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a taron da aka shirya domin bikin tunawa da Sojojin Najeriya na shekarar 2026 a Abuja. ’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa Wannan na zuwa ne bayan ce-ce-ku-cen da ya faru ranar Talata tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima. An yi taƙaddama ne kan wani...
    A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.”   “Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira da kwarewa,” in ji sanarwar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12,...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum 14 da ake zargi da ta’amali da miyagun ƙwayoyi da kuma aikata wasu laifuka daban. Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar. MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu A cewar SP Shiisu, jami’an rundunar sun kama mutanen ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Dutse, Guri, Babura, Kanya Babba, Bulangu da kuma ‘Yankwashe. Ya ce rundunar ta ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri da suka haɗa da Exol guda 8,271, D5, Tramadol, Diazepam,...
    “Muna bincike wannan lamari, kuma muna tabbatar da cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka, za a kare shi. Ba za mu bari wani abu ya same shi (Yerima) ba matuƙar yana aikinsa yadda ya kamata kuma yana yin aikinsa sosai.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025
    Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta ayyana Najeriya ɗaya daga cikin jerin ƙasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa. Ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarin mutane a duniya na iya fuskantar yunwa saboda ƙarancin kuɗin tallafi. Rahoton da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da WFP suka fitar, ya nuna cewa rikice-rikice da tashin hankali ne ke jawo matsananciyar yunwa a ƙasashen da ke cikin hatsari. DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP Rahoton ya bayyana ƙasashen Haiti, Mali, Falasdinu, Sudan ta Kudu, Sudan da Yemen a matsayin waɗanda ke cikin mafi munin...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ruwan sha. Sauran sun hada da kewaye asibitocin domin inganta yanayin aiki da al’amuran tsaro. Dakta Kabiru Ibrahim ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa kokarinta na tallafawa harkokin kiwon lafiya a jihar.  
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
    Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya. Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu An shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/ABJ/CR/610/2025, dangane da wasu rubuce-rubuce da matashin ya wallafa a shafinsa na X a watan Oktoban 2025. A cewar DSS, waɗannan rubuce-rubuce sun nemi a kifar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki tare da nuna goyon baya ga sojoji su karɓi mulki a ƙasar. Lauyan...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  Babban Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda mai kula da shiyya ta 8, da ke Lokoja, AIG Abubakar Zubairu, ya bukaci jami’an ‘yan sanda a Jihar Kwara da su ninka kokarinsu wajen karfafa hadin kai da kuma zurfafa dangantaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma. A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ta fitar, ta ce AIG Zubairu  ya yi wannan kira yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kwara da ke Ilorin. Sanarwar ta yaba wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar ‘yan sanda da kuma kudaden da gwamnatinsa ke fitarwa domin inganta tsaro. Haka kuma, ta yi kira...
    Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu . Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu. Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Jihar Nasarawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai...
     A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011. Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An sami tsaiko a yadda kungiyar take tafiyar da ayyukan nata, saboda bullar Korona, amma ta ci gaba da aiki a karkashin wani tsari na musamman  ( IranDoc.). Aikin wannan cibiyar shi ne tsara gudanar da nazarori da bincike na ilimomi mabanbanta da kuma hana yin maimaici akansa. A halin yanzu da akwai mutane 20 da suke aiki a karkashin wannan kungiyar daga asalin su 20...
    Ya ƙara da cewa rundunar ta samu nasarar ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka ceto daga hannun masu safarar mutane, inda aka miƙa su ga iyalansu. Kayan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargi sun haɗa da bindiga AK-47 guda ɗaya, bindiga ta gida guda ɗaya, alburusai 183, motoci uku, babur mai ƙafa uku da keke napep ɗaya, da kuma dabbobi sama da 200 na sata. Haka kuma, ‘yansanda sun ƙwato tarin miyagun ƙwayoyi irin su Fentalin, Exol, Tramadol, da wiwi, tare da wayar wutar lantarki. Abubakar ya sake tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro, inda ya ce, “Duk da waɗannan nasarori,...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025 Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump November 3, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025
    Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kano da Kewaye, Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi, ya bayyana ficewarsa a hukumance daga jam’iyyar NNPP. Ƙoƙ8 inda ya danganta hakan da rikicin shugabanci da ke kara tsananta a cikin jam’iyyar. PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2025, wacce aka aika wa Shugaban jam’iyyar a Unguwar Zaitawa a Karamar Hukumar ta Birni, Koki ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa hakkin sa na kundin tsarin mulki na ’yancin shiga ko ficewa daga kowace jam’iyya. “Bisa ga hakkin da kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025
    Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya. Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin. Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona. A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura...
    Hukumar Kula da jin dadin mahajjan Jihar Taraba ta bayyana 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe ga masu niyyar yin hajji don kammala biyan kuɗin tafiyar hajji ta shekarar 2026. A cewar wata sanarwa da Sashen Bayani na Hukumar ya fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Hamza Baba Muri, an ƙayyade sabon kuɗin hajjin 2026 a Naira miliyan 7,630,000, kamar yadda Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON) ta amince. Hukumar ta yi kira ga duk masu shirin yin hajji ta wannan tsari su tabbata sun biya kuɗin gaba ɗaya kafin ƙarshen wa’adin domin samun tabbacin shiga cikin masu sauke farali shekara mai zuwa. Mai magana da yawun Hukumar ya jaddada cewa dukkan biyan kuɗi dole ne a yi su ta...
    A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma. Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha. Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa...
    Pars Today – Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, yana Allah wadai da fashewar da ta faru a babban birnin Pakistan, ya ce ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin kuma fuskantar wannan mummunan lamari yana buƙatar haɗin gwiwa, ƙuduri, da haɗin kai daga dukkan ƙasashe. Reza Amiri-Moqaddam, Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, a ranar Talata, yayin da yake Allah wadai da fashewar ta’addanci a birnin Islamabad – wanda ya kashe mutane 12 tare da raunata aƙalla wasu 30 – ya ce: “Ta’addanci makirci ne na matsorata waɗanda ke neman wargaza yankinmu da kuma sanya cikas a hanyarsa ta zuwa ga ci gaba mai ɗorewa.” A cewar jaridar Pars Today, jakadan Iran a Pakistan ya jaddada cewa: “Wannan...
    Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana kudurinta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na kasa da aka tsara a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba. Hakan na zauwa ne duk da sabon umarnin kotun tarayya da ke hana ta ci gaba da shirya taron. Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Mataimakin Sakataren Yada Labarai na kasa na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa hukuncin kotun da ke dakatar da taron “bata lokaci ne kawai,” yana mai jaddada cewa jam’iyyar na bin hukuncin da kotun koli ta yanke a baya wanda...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban. Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace  uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban na rayuwar mutane, ciki har da maguguna, fannin kiwon lafiya, muhalli, noma, da masana’antu a cibiyoyin Makamashin Nukiliya ta Iran. A lokacin ziyarar da ya kai wa Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Araghchi ya jaddada cewa fasahar nukiliya tana nan a dukkan fannoni tana ba da gudummawa ga ci gaban fannoni daban-daban. Ya kara da cewa wannan ilimi da fasaha suna hanzarta ci gaban kimiyya...
    Shugaban Majalisar Saukar da Mulkin Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya tabbatar da zurfin dangantakar Sudan da Masar, yana mai nuni da dadadden zumunci da tarihi da ke tsakanin al’ummomin biyu. A lokacin ganawarsa da Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty, Burhan ya bayyana ” godiyarsa ga Masar, gwamnati da jama’a, saboda goyon bayan da suke bai wa Sudan a dukkan dandali na yanki da na duniya, da kuma jajircewarsu ga tsaro,  kwanciyar hankali da kuma ‘yancin kan Sudan,” yana mai jaddada “ra’ayin da kasashen biyu suka cimma na ci gaba da hadin gwiwa a dukkan fannoni.” A nasa bangaren, Abdel-Aty ya tabbatar da “cikakkiyar goyon bayan Masar, ta jagoranci da kuma ta jama’a, ga Sudan ‘yan uwantaka, bisa...
    Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya sanya hannu kan dokar kafa cikakkiyar rundunar tsaro ta kasa a wannan Laraba. Maduro ya jaddada bukatar kafa cikakkiyar rundunar tsaro, wacce ta hada dukkan cibiyoyin soja na gwamnati da kuma dakarun sa kai najama’a a safiyar yau Laraba. Dokar na da nufin tsara da kuma hada dukkan cibiyoyin gwamnati, kamar sojoji da ‘yan sanda, da kuma al’umma wajen  fuskar barazanar waje ko ta ciki, a karkashin ka’idar kare cikakken tsaro” na Venezuela daga duk wata barazana ga kasar. Mahimmancin wannan doka ya ta’allaka ne kan karfafa ikon shugaban kasa da na sojoji a cikin mawuyacin hali. Yana nuna yanayin da ake ciki na mayar da hankali kan ayyukan soja ga gwamnati da al’umma, kuma...
    An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi. “An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya. “An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.” Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bai amsa kiran waya da saƙonnin da aka tura masa ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025 Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya,...
    “Dukkanin bayanan da ake da su sun nuna cewa babu wani kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya… Wannan labarin ƙarya ne da ƙungiyoyi suka ƙirƙira, wanda Shugaba Trump ke ƙoƙarin yaɗawa. “Wannan magana za ta iya ƙara tayar da hankali a Nijeriya… ‘Yan ta’adda suna kai hare-hare a kasuwanni, coci-coci, da masallatai, kuma suna kashe kowa ba tare da bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba,” in ji Bukarti yayin wata hira da gidan talabijin na Al-Jazeera. Masana da dama sun yi gargaɗin cewa irin wannan kalamai daga shugabanni na iya haddasa tashin hankali a ƙasar. Martanin Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Tarayya ta kuma mayar da martani ta hanyar ƙaryata batun cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar. A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu. Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga...
    Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa, bayanin da ya yi wa Shugaban Kasa, ya yi ne kan sakamakon rangadin aikinsa na yankin Arewa maso Gabas da kuma sabbin bayanai kan yanayin tsaro a fadin kasar.   “Na zo ne domin in yi masa bayani kan sakamakon ziyarar da na kai yankin Arewa maso Gabas sannan da kuma bitar wasu yanayin tsaro a fadin kasar, wanda hakan ya gamsar a wannan lokacin,” in ji Babban Hafsan Sojan Kasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina November 11, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa November 11, 2025 Manyan...
      Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Ya...
    Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa...
    Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da niyyar haɗa kai da hukumar wajen inganta jin daɗin ‘yan sanda da kyautata yanayin ayyukansu.   Ya ce, “Gwamnatina na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an kula da walwala da jin daɗin ‘yan sanda. Wannan ne dalilin da ya sa muke gyaran hedikwatar ‘yan sanda ta Zamfara a halin yanzu.   “Haka kuma, muna gina wasu muhimman gine-gine a hedikwatar rundunar ‘yan sanda na Moble. Mun samu nasarori da dama a wajen, kuma muna da ƙarin shirye-shirye na gaba.   “Na ji daɗin yadda sakataren hukumar ya ambaci batun ginin sabon unguwar ma’aikatan ‘yan sanda. Idan ka duba halin da barikin ‘yan sanda ke ciki yanzu, za...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15 November 11, 2025 Daga Birnin Sin Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa? November 11, 2025 Daga Birnin Sin Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako November 11, 2025
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu...
    An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.   Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.   Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.   Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da...
    Kungiyar kasashe da cibiyoyin kasa da kasa ta fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ta yi Allah wadai da manyan laifukan da aka aikata a ƙasar Sudan bayan kwace El Fasher daga dakarn (RSF) suka yi, da kuma ƙaruwar tashin hankali a yankin arewacin Darfur da Kordofan. Wannan sanarwar, wadda ministocin harkokin waje da manyan jami’ai daga Australia, Belgium, Kanada, Denmark, Estonia, Hukumar Tarayyar Turai, Jamus, Iceland, Ireland, Luxembourg, New Zealand, Netherlands, Norway, Slovakia, Slovenia, Spain, Sweden, da Birtaniya, tare da goyon bayan Austria, Croatia, Cyprus, Czechia, Finland, Latvia, Poland, Romania, da Switzerland suka yi, ta nuna damuwa sosai game da rahotannin ta’asar da aka aikata a kan fararen hula. Wannan sanarwar haɗin gwiwa ta yi nuni da...