Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu
Published: 12th, November 2025 GMT
Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu.
Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da su mayar da hankali kan yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kana su dakatar da ayyukan da ka iya haifar da tashe-tashen hankula, musamman ma a hana amfani da karfin tuwo da kuma guje wa karuwar rikice-rikice.
Sun Lei ya kara da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, mabudin warware matsalolin kasashen Afirka yana hannun Afirka. Duk wata mafita ya kamata ta kare ikon mulki kan Sudan ta Kudu da shugabancinta, tare da mutunta batutuwan da kasar ta damu da su.
ADVERTISEMENTBugu da kari, Sun Lei ya bayyana cewa Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su kara ba da tallafi don daidaita tattalin arziki da rayuwar jama’ar kasar, da kyautata walwalar jama’arta, da kuma tallafawa Sudan ta Kudu wajen daukar hanyar samun ci gaba mai ’yanci da dorewa. (Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Afrika Ta Kudu Tace Babu Abinda Zai faru idan Amurka ba ta halarci taron G20 ba
Rahotanni sun nuna cewa Afirka ta Kudu ta ce babu abin da zai sauya dangane da rashin zuwan wakilan Amurka taron G20 da take karbar bakuncinsa, bayan da shugaba Donald Trump a karshen makon jiya ya sanar da matakinsa bisa zargin cewa ana take hakkin dan adam a kasar.
Sanarwar da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce, mataimakin shugaban kasa JD Vance, wanda ake sa ran zai halarci taron shugabannin kasashen G20 a Johannesburg tsakanin 22 zuwa 23 ga Nuwamba, an soke ta bisa dalilai masu karfi.
Trump ya ce, abin kunya ne kwarai da gaske cewa za a gudanar da taron G20 a Afirka ta Kudu, kasar da ta kasance tana cin zalin wasu daidaikun mutane, ta hanyar kwace musu filaye da gonaki.
Amma ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta bayyana wannan mataki a matsayin abin takaici tare da ci gaba da yin watsi da ikirarin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Babu Wani Zabi Da Ya Rage Face Amincewa Da Iran A Matsayin Cibiyar Kimiyyar Masana’antar Nukiliya November 10, 2025 Kamaru: Chiroma Ya Bai Wa Gwamnati Sa’o’i 48 Da Ta Saki Wadanda Ta Kama Bayan Zabe November 10, 2025 ‘Yan Jarida 44 Ne Su Ka Yi Shahada A Sansanonin Hijira Na Gaza November 10, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Isra’ila” A Yankin Saida November 10, 2025 Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali November 10, 2025 An Fara Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Sheikha Hind Bint Maktoum November 10, 2025 Zaben Iraki: Gwaji don ‘yancin siyasa da kawo karshen tsoma bakin Amurka November 10, 2025 Iran da Rasha sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa November 10, 2025 Iran ta nuna damuwa kan zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan November 10, 2025 Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa November 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci