Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya
Published: 15th, November 2025 GMT
Haka zalika, a 2025, an samu kararraki 28 na ‘yan Nijeriya da suka kashe kansu. Shari’ar ta shafi mutane daga kowane jinsi da kuma masu matsayi daban-daban, ciki har da dalibai da kuma ‘yan kasuwa.
Da yake zantawa wani dan jarida, masanin ilimin halayyar Dan’adam, kuma kwararre a kan lafiyar kwakwalwa, Dakta Shuab Waidi ya ce; batun kisan kai a halin yanzu, na bukatar da kulawar gaggawa ga mahukuntan kasa.
Ya ce, “Kididdigar na nuna cewa, a kowane minti 33; ana asarar rai a Nijeriya sakamakon kashe kai, don haka, akwai bukatar cikin gaggawa a bude tattaunawa game da kashe kai ta hanyar gwajin lafiyar kwakwalwa.
“Cutar tabin hankali, wani bangare ne na kisan kai da kai, amma kashe kai ba cutar tabin hankali ba ce, domin kuwa tana da alaka da yanayin dabi’a mai rikitarwa da kuma yanayin zamantakewa.
“A yayin da sama da mutum 720,000 ke mutuwa a duk shekara daga masu kashe kansu a duk duniya, Nijeriya ba za ta iya daukar wannan batu a matsayin gazawar dabi’a ko kuma sakamakon shan muggan kwayoyi kawai ba.
Har ila yau, shugaban sashen kula da masu tabin hankali na cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Keffi a Jihar Nasarawa, Dakta Hassan Galadima ya ce; yanayin kashe kai a halin yanzu, na nuna matukar halin damuwa da ake ciki.
“An fi samun maza fiye da mata wajen yunkurin kisan kai, ta yadda suka mayar da al’amarin tamkar wata gasa. Har ila yau, ana samun yukurin afkawa cikin teku, wanda a halin yanzu ya zama ruwan dare fiye da rataye kai ko shiga gaban motoci,” in ji shi.
Ya kuma alakanta hakan da abubuwa da dama da suka hada da matsin lamba na ilimi, tabarbarewar arziki da ramuwar gayya da asiri da sauran makamantansu da suka zama ruwan dare a tsakanin matasa.
Dalilan Da Ke Haifar Da Matsalar Kisan Kai
A nasa ra’ayin, Shugaban Kungiyar Likitocin Iyali na Nijeriya (SOFPON), shiyyar Kudu-maso-Kudu, Dakta Iyang Aniete ya ce; Nijeriya na fuskantar matsalar kunar-bakin-wake da ta barke, aka kuma yi shiru, ba a magana a kai.
Ya kara da cewa, “Tare da kiyasin mutuwar mutane 15,000 a duk shekara da kuma aikata laifin yunkurin kashe kai a kasar, inda kuma ake hana mutanen da ke cikin wahala neman taimako.
Kashi 77 cikin 100 na kashe-kashen da ake yi, na faruwa ne a kasashe na masu karamin karfi da matsakaita, Nijeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 200, na daya daga cikin wuraren da ake samun masu kashe kawunansu a duniya, inda aka kiyasta masu kashe kansu da kashi 17.3 cikin 100,000, wanda ya zarce na duniya (10.5 cikin 100,000) da kuma Afirka (10.00) da kuma Afirka (10.00).
Ya ci gaba da cewa, yawan kunar bakin wake a Nijeriya ya zarce 10.5/100, 000 a duniya, sai kuma na Afirka 12.0/100,000, yayin da Lesotho ke kan gaba a 72.4/100,000. A shekarar 2023, an samu rahoton kashe mutane kusan 83 a Jihar Legas kadai.
Kashi 15 cikin 100 na wadanda suke kashe kansu, mutanen da ba a kula da su ne.”
A cewarsa, a wani bincike da aka gudanar a Nijeriya, kashi 80.6 cikin 100 na wadanda abin ya shafa maza ne, kashi 51.8 cikin 100 sun yi aure, kashi 33.6 cikin 100 dalibai ne, kashi 2.3 cikin 100 kuma suna tsakanin shekaru 25 zuwa 34.
“Mutuwar kashe kai, ana ganinta a matsayin wani babban zunubi, kuma haramun; wanda mugaye ne kadai ke iya yi, don haka; iyalan da abin ya shafa, galibi ana kyamar su tare da kin sakin jiki da su ta hanyar zamantakewa, don haka; sun gwammace su boye mutuwar ’yan’uwan nasu, domin kuwa suna bayyana irin wannan kisan kai a matsayin mutuwar ganganci.
“Yawancin shari’o’in da aka ruwaito, sun dogara ne da bayanan ‘yansanda da kuma na asibiti.
“Shaidar bincike kan halin kashe kai a Nijeriya sun hada da amfani da sinadarai, yanka kai, kona kai da kananzir, rataye kai da kuma amfani da bindigogi a matsayin hanyoyin kashe kai,” in ji shi.
A cewar wata mai ilimin sanin halayyar Dan’adam, Charity Dogo, “Daga cikin manyan abubuwan da ke jawo kashe kai, akwai abubuwa masu hadari na mutum, ciki har da matsalolin kudi, tarihin iyali na wani ya kashe kansa, rashin lafiya, rashin lafiyar jiki da shaye-shaye da sauran makamantansu.”
Ta kara da cewa, “Yayin da alakar da ke tsakanin kashe-kashe da tashe-tashen hankula, musamman bakin ciki da matsalar shan barasa ya samu wurin zama sosai a Nijeriya, yawancin kashe-kashen kuma na faruwa ne da gangan a lokutan rikici tare da rashin iya magance matsalolin rayuwa, kamar matsalolin kudi, rabuwar dangantaka ko ciwo mai tsanani da kuma rashin lafiya.
“Bugu da kari, fuskantar rikici, bala’o’i, tashin hankali, cin zarafi ko asara da kuma kebewa wuri guda na da alaka da wadannan kashe-kashe na kai, kai tsaye.”
Ta ci gaba da cewa, “Akwai alaka tsakanin yadda ake yada shafukan sada zumunta, ba tare da wata ka’ida ba; da kuma karuwar kashe-kashen da matasa ke yi.”
Charity ta kara da cewa, “Matsakaitan matasa a duniya a yau, suna kokawa game da matsalolin yau da kullum, wadanda ka iya taimakawa wajen fadawa wannan mummunan hali.
“Yanayin zama na yau da kullum, shi ma na taimakawa. Don haka, yawancinsu suna kokarin sarrafa shi tare da wuce gona da iri a kafofin watsa labaru, sannan muna da yawan cin zarafin juna a wadannan kafofi na watsa labaru.
“Wani abu da amfani da kafofin watsa labaru ke yi shi ne, yana bude wasu kofofi ko hanyoyi masu matukar cutarwa.”
Wata likitan mahaukata, Abimbola Owoeye, a nata ra’ayin, ta bayyana tabarbarewar zamantakewa a tsakanin iyalai a matsayin abin da ke matukar taimakawa.
Sannan ta lura cewa, yawancin matasa ba sa yin hulda tare da danginsu, suna zabar yin hulda ko abota da fasahar sadarwa (AI), a kan su yi alaka da dan’uwansu Dan’adam.
“Wannan rashin kyawawan dabi’u a tsakanin iyali da kuma hadin kai,” in ji ta, “na iya haifar da rashin matsaloli, musamman a kan lafiyar kwakwalwa.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe ’yanga 16 sun sace mutane 42 a Neja
’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.
Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla.
“Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.”
Ya ce daga baya ’yan bindiga suka kawo sabon hari da asuba, ranar Alhamis a yayin da ake Sallar Asuba a ƙauyen Magama, suka yi garkuwa da mutane 20.
“Nan ma da ’yan bindiga suka bi su, ashe sun yi kwanton ɓauna, suka kashe ’yan banga 13, suka jikkata wasu da dama.”
Sakataren Yaɗa labaran Shugaban Ƙaramar Hukumar Mashegu, Isah Ibrahim Bokuta, ya tabbatar da hare-haren, tare da jinjina wa ’yan bangar bisa yadda suka sadaukar da ransu domin kare al’umnarsu.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Neja, Wasiu Abiodun, amma ya ce zai tuntuɓe shi daga baya, idan ya bincika.
A gefe guda, mazauna yankin sun shaida mana cewa tun ranar Litinin al’ummomi da dama sun yi gudun hijira zuwa Mashegu, Kawo-Mashegu, Manigi da wasu wurare. Wasu kuma sun fake a gidajen ’yan uwansu a nesa domin tsira.
Majiyoyi sun ce cikin ƙauyukan da aka watse har da Dutsen Magaji, Borin Aiki, Gidan Ruwa da Magama.
Hakazalika har yanzu masu garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Neja, Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ba su sake shi ba, makonni bayan rahoton cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa na Naira miliyan 70.
An yi garkuwa da Niworo ne a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025, tare da Kwamishina na Dindindin II na Hukumar Zaɓe ta Jihar Neja (NSIEC), Barrister Ahmad Mohammed, direbobinsu da wasu matafiya a kan titin Mokwa–New Bussa, a Karamar Hukumar Borgu.