Ɗalibar BUK ta ci kyautar motar N35m a gasar MTN
Published: 14th, November 2025 GMT
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar.
Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu.
Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi.
Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce kamfanin na son tallafa wa matasa da ke karatu a manyan makarantu.
“Mun yadda da matasan Najeriya. Ba wai magana kawai muke ba, muna tare da su, muna goyon bayansu domin su zama nagartattu,” in ji shi.
Taron da aka yi a Kano ya ƙunshi rawa da waƙoƙi, wasannin kwamfuta da sauransu.
MTN ya kuma bai wa ɗalibai ’yan kasuwa 10 dandalin nuna kayayyakinsu ba tare da biyan kuɗi ba.
Ɗalibai sun bayyana taron a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka faranta musu rai a jami’ar, inda suka gode wa MTN saboda tallafin da suka samu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗaliba Ɗalibai kyauta
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030
Majalisar Wakilai ta umarci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Shirya Jarabawar Afrika ta Yamma (WAEC) da su dakatar da shirin fara amfani da tsarin jarabawa ta kwamfuta a jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2026.
Umarnin ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa da Kelechi Wogu ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a ZariyaKudirin na Wogu mai taken: “Bukatar Daukar Mataki Don Kaucewa Yawan Faduwa a Jarabawar Kwamfuta da WAEC ke Shirin Gudanarwa a 2026,” ya yi gargadin cewa gaggauta amfani da tsarin na iya haifar da yawan faduwa da kuma jefa dalibai cikin damuwa.
Wogu ya nuna damuwa kan yadda Ma’aikatar Ilimi ke da niyyar ci gaba da tsarin jarabawa ta kwamfuta duk da adawar da ke fitowa daga Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa da shugabannin makarantu, musamman a yankunan karkara inda fiye da kaso 70 cikin 100 na masu jarabawar ke zaune.
Ya ce yawancin makarantu, musamman a yankunan karkara, ba su da dakunan kwamfuta masu aiki, babu intanet, babu wutar ingantacciyar lantarki, kuma ba su da malamai masu ƙwarewa a fannin fasahar zamani.
Ya jaddada cewa fara amfani da tsarin a irin wannan yanayi zai zo da matsala, yana ambato matsalolin fasaha da suka shafi shafin sakamakon WAEC na 2025 a matsayin shaidar rashin shiri.
Domin magance waɗannan ƙalubale, Majalisar ta umarci Ma’aikatar Ilimi da ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi domin saka ayyukan daukar malamai masu koyar da kwamfuta, gina dakunanta, samar da kayan intanet da kuma wutar lantarki a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 zuwa 2029.
Majalisar ta kuma yanke shawarar cewa kada a fara amfani da tsarin jarabawar kafin shekarar karatu ta 2030.
Majalisar ta amince da kudirin gaba ɗaya, tare da umartar kwamitocinta kan Ilimi a matakin farko, Fasahar Zamani da Bayani, Hukumomin Jarabawa, da Ma’aikata da su tattauna da masu ruwa da tsaki sannan su gabatar da rahoto cikin makonni huɗu domin ɗaukar matakin dokoki na gaba.
An kirkiro da tsarin jarabawa da kwamfuta ne a Najeriya ne domin rage yawan magudin jarabawa da kuma sabunta tsarin ilimi na ƙasa.