Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-09@16:49:43 GMT

Kungiyar ‘Yan Dako Reshen Jigawa ta Kaddamar da Sabon Shugaba

Published: 9th, November 2025 GMT

Kungiyar ‘Yan Dako Reshen Jigawa ta Kaddamar da Sabon Shugaba

Daga Usman Mohammed Zaria

Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Abba Zari Malamawa a matsayin sabon shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Dutse.

A jawabinsa yayin kaddamarwar shugaban kungiyar na jihar, Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci sabon shugaban da ya kasance mai gaskiya da rikon amana wajen hulda da ya’yan kungiyar tare da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki domin cimma nasarar da ake bukata.

Malam Nasiru Idris Sara, ya bukaci masu sana’ar dako a karamar hukumar Dutse da su nuna cikakken goyon baya ga sabon shugaban, tare da mutunta ‘yan kasuwa a matsayin su na jigo wajen ciniki da kasuwanci wanda ke bude kofar samu ga ‘yan dako.

Ya kuma yi addu’a ga marigayi mai martaba sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammadu Sanusi, inda ya bukaci sarki Muhammad Hameem Nuhu Sanusi ya ci gaba da aiki da kyakkyawan tarihin da tsohon sSarkin  bari wajen mu’amala mai kyau da shugabanci nagari da kuma adalci ga talakawansa.

Ya kuma bayyana kudurin kungiyar na aiki tare da masu ruwa da tsaki domin inganta harokokin saye da sayarwa a jihar Jigawa, inda ya bukaci gwamnatin jihar da ta bada kulawa ta musamman wajen bunkasa ciniki da masana’antu domin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar jihar.

A jawabinsa, Malam Jamilu Maimasara, ya bayyana cewa kafa kungiyar ‘yan dako reshen karamar hukumar Dutse zai karfafi harkokin kasuwanci, inda ya yi addu’ar Allah ya yi masa jagoranci domin samun nasarar aikin da ke gaban sa.

A nashi tsokacin, sabon shugaban kungiyar ‘yan dako reshen karamar hukumar Dutse Malam Abba Malamawa ya ce kofarsa a bude take don karbar shawarwari da kuma gyara, yayin da zai yi aiki da kowa da kowa domin cimma nasarar da ake bukata.

A nasa bangaren, Sarkin Dakon Dutse Malam Nasiru Manya, ya bayyana kafa reshen kungiyar a matsayin wani muhimmin ci gaba da ya samu sana’ar dako a karamar hukumar.

Kazalika, ya yi fatan hakan zai kawo karin cin moriya ga masu sana’ar dako da harkokin kasuwanci.

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Yan Dako Jigawa karamar hukumar Dutse

এছাড়াও পড়ুন:

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Tun da farko, Daraktan DSS na Jihar Kaduna, Mr. Hakeem Abiola, an shirya taron ne domin nazarin ƙalubalen aiki da kuma karfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa hukumar DSS a ƙarƙashin jagorancin Mr. Oluwatosin Adeola Ajayi tana amfani da dabaru biyu – na ƙarfi da na sulhu – domin tabbatar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai da na al’umma kamar JNI da CAN ya taimaka wajen shawo kan rikice-rikice kafin su zama tashin hankali.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025 Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  November 7, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar Hadin Kai Ta Kafin Hausa Ta Horas Da Matasa 160 Sana’o’in Hannu
  • Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
  • Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala
  • Nigeria: Za A Ci Gaba Da Zaman Shari’ar Shugaban Kungiyar “IPOB” A ranar 20 Ga Watan Nan Na Nuwamba
  • Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma
  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
  • GORON JUMA’A
  • Genoa ta naɗa Daniele De Rossi sabon kociya
  • Ajax ta kori kocinta John Heitinga