Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2
Published: 13th, November 2025 GMT
Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila da Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ziyarci zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis domin shaida sauya sheƙar ƴan majalisa biyu daga NNPP zuwa APC.
Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon. Abdulmumin Jibrin, wanda ke wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, da Hon. Sagir Koki, wakilin Kano Municipal.
A cikin wasiƙunsu da Kakakin Majalisar Abbas Tajudeen ya karanta, sun bayyana rikici mai sarƙakiya da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar NNPP a matsayin dalilin barin jam’iyyar zuwa APC.
ADVERTISEMENTDuk da jayayya da Hon. Kingsley Chinda daga bangaren marasa rinjaye, wanda ya dage wajen ɗaga batun sanarwar a lokacin karanta wasiƙun da karɓar sauya shekarun, Kakakin Majalisar bai amince da buƙatarsa ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Matar tsohon Shugaban Ƙasa Shagari ta rasu
Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, ta rasu tana da shekaru 89 a duniya.
Iyalai sun tabbatar da cewa ta rasu ne da misalin ƙarfe 3:00 na ranar Litinin, bayan fama da doguwar jinya.
Ina son komawa Barcelona kafin na yi ritaya — Messi EFCC na neman tsohon Gwamnan Bayelsa ruwa a jalloƊan marigayi tsohon shugaban ƙasa kuma Hakimin Shagari, Kyaftin Bala Shagari (mai ritaya), shi ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da aka fitar daga Sakkwato.
Sanarwar ta ce: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna baƙin cikin sanar da rasuwar Hajiya Sutura Shehu Shagari, mata ɗaya tilo da da ta rage wa tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, GCFR, Turakin Sakkwato.”
Sanarwar ta ƙara bayyana cewa: “Ta kasance mace mai kamala, tawali’u da nutsuwa, uwa mai kulawa, kakarmu kuma jagorar gida wadda rayuwarta ta cika da mutunci da jinƙai.
“Rasuwarta babban rashi ne ga iyalan Shagari da duk wanda ya san ta. Za a sanar da cikakkun bayanai game da jana’izarta a nan gaba. Allah Ya jiƙanta da rahama.”
Shi ma a shafinsa na Facebook, ɗan marigayi shugaban ƙasa kuma jikan Hajiya Sutura, Bello Bala Shagari, ya tabbatar da rasuwar da bayyana a matsayin babban rashi.
Ya bayyana cewa “Mun yi rashi ba ƙarami ba. Ita ce mata ɗaya tilo da ta rage a cikin matan marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Allah Ya haɗa su a Aljannah.”
Rasuwar Hajiya Sutura ta kawo ƙarshen wani babi a tarihin gidan Shagari, gidan tsohon shugaban ƙasa na farko da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya a Jamhuriyar ta Biyu ta Najeriya.