Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP
Published: 14th, November 2025 GMT
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ƙaryata jita-jitar ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa YPP.
Rahotanni na yawo a shafukan sada zumunta cewa ya sauya sheƙa, amma mai magana da yawunsa, Gyang Bere, ya ce labarin ƙarya ne, tare da buƙatar jama’a su yi watsi da shi.
Ɗalibar BUK ta samu kyautar motar N35m a gasar MTN Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin TarayyaBere, ya ce labarin ƙarya ne aka shirya domin haifar da rikici.
“Wannan zancen ƙarya ne da wasu ke yaɗawa domin su rikita al’umma,” in ji shi.
Ya bayyana cewa gwamnan yana nan daram a jam’iyyar PDP, kuma yana mayar da hankali kan ci gaban al’ummar jihar.
A baya-bayan nan, APC ta yi iƙirarin cewa gwamnan na ƙoƙarin sauya sheƙa zuwa cikinta, amma Mutfwang, ya ce ba shi da niyyar sauya sheka, duk da matsin lambar da yake fuskanta daga wasu.
Sai dai majiyoyi daga PDP sun ce gwamnan na iya komawa wata jam’iyyar a nan gaba, idan rikicin jam’iyyar ya ƙi ƙarewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnan Mutfwang Sauya Sheƙa Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano
’Yan sanda a Jihar Kano sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ofishin mataimakin gwamnan jihar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wadda aka sace kwanan nan a harabar gidan gwamnati.
Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare, lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, Shafiu Sharp-Sharp a matsayin ɗaya daga cikin ababen zargi.
Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da GabonSai dai wata sanarwa da ofishin mataimakin gwamnan ya fitar, ta ce jami’an tsaro sun gano motar da safiyar wannan Larabar bayan wani aikin haɗin gwiwa na gaggawa da aka gudanar.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargi da satar motar, Ya’u Gezawa, wanda yanzu haka yana taimaka wa jami’an tsaro wajen bincike.
Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya bayyana lamarin a matsayin cin amanar aiki, tare da jinjinawa ’yan sanda bisa gaggawar da suka yi wajen gano motar da kama wanda ake zargi.