Aminiya:
2025-11-15@15:35:12 GMT

Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji

Published: 15th, November 2025 GMT

Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP.

Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga.

Rundunar ta ce sojojin sun murƙushe wani harin kwanton ɓauna da ISWAP ta kai musu a yayin da suke sintiri domin kare al’ummomin da ke kewaye da Wajiroko a yankin Azir Multe a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

Ta ce sojojin sun gamu da kwanton ɓauna ne daga ’yan ta’adda yayin da suke dawowa daga aikin sintiri a gefen Dajin Sambisa.

Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja

Rundunar ta jaddada cewa Kwamandan Brigedi ta 25, Birgediya Janar M. Uba, shi ne ya jagoranci tawagar, wacce ta haɗa da mambobin CJTF, kuma sun koma sansaninsu lafiya.

Ta ce sojojin sun fuskanci harin ne cikin ƙwazo, inda suka yi musayar wuta da makiya har suka fatattake su.

Sanarwar rundunar, ta hannun muƙaddashin kakakinta, Laftanar-Kanar Appolonia Anele, ta ce a yayin arangamar, sojoji biyu da mambobin CJTF biyu sun kwanta dama.

Hedikwatar tsaro ta yaba da jarumtakar dakarun, tare da yin ta’aziyya ga iyalai da abokan aikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Waidi Shaibu, ya jinjina wa jarumtar dakarun da ke ci gaba da aiki a ɗaya daga cikin yankunan da suka fi haɗari a ƙasar, yana mai cewa sadaukarwarsu abin karramawa ne a kullum wajen kare Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ISWAP Janar kwanton ɓauna mayaƙan ISWAP Wajiroko

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi

Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar.

Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado.

Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar.

Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar da ake yi yanzu zai taimaka wajen tantance ingancin kulawar da ake bayarwa, da gano wuraren da ake bukatar gyara domin samar da tsarin taimako mai inganci da niyya kai tsaye ga masu bukata.

Ta kuma jaddada bukatar ƙara haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki tare da horar da ma’aikatan cibiyoyin SARC a fannin tattara bayanai da bayar da rahoto domin inganta tsarin tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafin jinsi.

Ali Muhammad Rabiu/Ilorin

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94
  • M D D Ta yi Tir Da Harin Da Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Suka Kai A Masallaci A Yammacin kogin Jodan
  • Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje
  • Mutum ɗaya ya rasu yayin da ’yan sanda da ’yan bindiga suka yi artabu a Kwara
  • Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike
  • Jihar Kwara Ta Jaddada Kudirin Tallafa wa Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafin Jinsi
  • Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle
  • Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana