Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
Published: 16th, November 2025 GMT
An zaɓi tsohon Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa a yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Asabar.
PDP ta ce Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya yi nasarar ce akan Sanata Lado Ɗan Marke da ƙuri’u sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, da wakilai 3, 131 suka halarta.
Hakan dai na zuwa ne yayin da jam’iyyar ta PDP ta dakatar da Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar, yayin da gwamnonin Adamawa da na Fulato suka ƙalubalanci matakin suna masu cewar matakin ka iya ƙara rura wutar rikicin da jam’iyyar ke ciki.
Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya samu ƙuri’u 1,516 daga cikin ƙuri’u 1, 834 da aka kaɗa a yayin zaɓen.
A kujeru biyu ne dai aka yi zaɓe a babban taron jam’iyyar na ƙasa, yayin da dama daga sauran kujerun shugabancin jam’iyyar kuma aka yi maslaha a tsakanin ’yan takara wanda daga bisani aka kira wakilai daga jihohi suka kaɗa ƙuri’unsu kamar yadda dokar hukumar zaben Najeriya ta tanada.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kabiru Tanimu Turaki
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki
Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya buƙaci jam’iyyar PDP da ta ɗage babban taronta da ta shirya gudanarwa tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Saraki ya ce ci gaba da shirin gudanar da taron duk da irin umarnin dakatarwa da kotuna suka bayar zai ƙara ta’azzara rikicin jam’iyyar sannan ya jefa ta cikin matsaloli a nan gaba.
An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin DuniyaYa bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan karɓar baƙuncin ’yan kwamitin amintattun jam’iyyar ƙarƙashin shugabancin Ambasada Hassan Adamu, a gidansa.
Tawagar ta ziyarci Saraki ne domin neman tabarrakinsa da shawarwari kan yadda za a cimma haɗin kai a jam’iyyar da ta samu rarrabuwar kai.
Tsohon shugaban da ya jagoranci Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019, ya ce umarnin kotuna kusan huɗu masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala kan halascin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.
Zuwa yanzu, akwai ƙararraki uku a gaban kotuna daban-daban waɗanda suka bayar da umarnin dakatar da shirin taron, yayin da PDP ta ce tana ci gaba da shirin gudanar da shi a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba.
Daga cikin waɗanda suka kai jam’iyyar kotu kan taron akwai Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido.