Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Published: 14th, November 2025 GMT
Da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Juma’a ne farkon matsakaicin jirgin ruwan yaki dankon jirage masu saukar ungulu na yaki samfurin 076 na kasar Sin, wato jirgin ruwa na Sichuan, ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta kamfanin kera jiragen ruwa na Hudong-Zhonghua a Shanghai, zuwa wani yankin teku don gudanar da gwajin sufuri a karon farko.
An bayyana cewa, tun lokacin da aka sanya jirgin cikin ruwa a watan Disamban shekarar 2024, an ci gaba da ginin jirgin ruwan na Sichuan bisa tsari, an kuma kammala gwajin tsayawa, da kuma daidaita kayan aiki, wanda ya ba da damar fara gwajin zirga-zirgarsa a cikin teku. (Amina Xu)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: jirgin ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko November 14, 2025
Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand November 14, 2025
Daga Birnin Sin Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya November 14, 2025