Hukumar Tsara Birane ta Kano Ta Fara Horar da Ma’aikata Kan Dokokin Aiki
Published: 12th, November 2025 GMT
Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka.
Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne domin haɓaka inganci a ayyuka da ƙarfafa ƙwararru da tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata.
A jawabinta, Manajiyar Darakta ta KNUPDA, Arc. Hauwa Hassan Tudun-Wada, ta bayyana horon a matsayin muhimmiyar hanya ta gina al’adar ladabi da biyayya da nagarta a cikin ma’aikatan gwamnati.
Ta yaba da jajircewa da himmar ma’aikata wajen halartar shirin, inda ta jaddada cewa fahimta da bin dokokin aikin gwamnati na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantaccen aiki, gaskiya, da kuma ɗaukaka darajar hukumar.
Daraktan kula da Ma’aikata, Alhaji Salihi Yusuf, wanda shi ne ya jagoranci zaman horon, ya jaddada muhimmancin kiyaye ƙwarewa da gaskiya a aikin gwamnati. Ya shawarci mahalarta su aiwatar da ilimin da suka koya domin ci gaban hukumar da kuma jihar gaba ɗaya.
Shirin ya ƙunshi gabatarwa ta hanyar tattaunawa da ayyukan gwaji, waɗanda suka nufi ƙara fahimtar mahalarta game da ƙa’idojin aiki, ladabi, da kuma yadda ake ƙara haɓaka ƙwarewa da ƙwazo a wurin aiki.
Rel/Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: aikin gwamnati
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin da aka aikata a El-Fasher
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da mummunan ta’addancin da aka aikata kan fararen hula a yankin El-Fasher na Sudan.
Ofishin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ya yi gargadin cewa El-Fasher ya zama birnin makoki a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare masu muni, wanda hakan ya haddasa wahalhalu marasa misaltuwa.
A cikin wani bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X, Li Fung, Wakiliyar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ta ce: “A cikin kwanaki goma da suka gabata, yankin El-Fasher ya kasance wurin da ake samun karuwar hare-haren ta’addanci.
A cewarta, “an kashe daruruwan mutane, ciki har da mata, yara, da wadanda suka jikkata wadanda suka nemi mafaka a asibitoci da makarantu.
Ta kuma nuna cewa an kama dubban mutane, ciki har da ma’aikatan lafiya da ‘yan jarida.
“Abin da muke gani ba rikici ba ne, hari ne kan rayuwar dan adam, wanda galibi ya dogara ne akan kabilanci.”
A ranar 26 ga Oktoba, Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta kwace iko da El-Fasher kuma ta yi kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa, wanda hakan ya haifar da fargabar raba kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump bisa zargin kisan Kiristoci November 9, 2025 Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila November 9, 2025 An Kafa Mutum-mutumin Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran November 9, 2025 Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati November 9, 2025 Wasu Kasashe Takwas Sun Bukaci Ganin An kama Benjamine Netanyahu November 9, 2025 WFP: Ana Fama Da Matsananciyar Yunwa A Gabashin DRC November 9, 2025 Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro November 9, 2025 Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa November 9, 2025 Martanin Iran ya haddasa wa Isra’ila hasarar fiye da Dala Miliyan 200 November 9, 2025 Biden Ya Caccaki Trump Bisa Tuhumarsa Da Kawo Barna November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci