An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya
Published: 13th, November 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya.
Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa Abuja da wasu sassan ƙasar da ma ƙetare.
Sanarwar ta bayyana cewa “an tari hanzarin ababen zargin ne da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar 12 ga watan Nuwamba.
“A wannan lokaci ne jami’an sashen Ɗan Magaji da ke Zariya suka kai samame bayan samun rahoton cewa wasu mutane na shirin safarar yara da ke tafe a ƙarƙashin gadar Ɗan Magaji da ke unguwar Wusasa.
Ya bayyana cewa “waɗanda ake zargin sun haɗa da Musa Shu’aibu, mai shekara 21 daga Funtua, Jihar Katsina; Sani Mamman, mai shekara 23 daga Ingawa, Jihar Katsina; da Mubarak Ismail, mai shekara 20 daga Unguwa Uku ta Jihar Kano.
Kakakin ya ce, yayin bincike waɗanda ake zargin sun amsa cewa su ne suka tattaro yaran daga wurare daban-daban da zummar kai su Abuja kafin jami’an ’yan sanda su damƙe su.
DSP Hassan ya ƙara da cewa, yaran duk ƙanana ne, kuma suna cikin ƙoshin lafiya da yanzu haka suna hannun rundunar, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano iyayensu ko masu kula da su.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yaba da bajintar jami’an sashen Dan Magaji, inda ya nanata cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in safarar yara ko cin zarafin su ba.
Ya kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su ci gaba da lura da lafiyar da walwalar ’ya’yansu, tare da faɗakar da su kan haɗarin safarar yara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jihar Kaduna Safarar Yara Zariya safarar yara
এছাড়াও পড়ুন:
Farfesa na Farko a fannin Ilimi a Arewa, Adamu Baikie, ya rasu yana da shekara 94
Allah Ya yi wa Farfesa Adamu Baikie, wanda ya kasance Farfesa na farko a fannin Ilimi daga Arewacin Najeriya, rasuwa.
Farfesa Adamu Bakie ya rasu yana da shekaru 94 ne a daren Jumma’a a gidansa da ke Zariya, Jihar Kaduna.
Babban ɗansa, Manjo Muhammad Adamu (Ritaya), ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a sanar da jama’a cikakkun bayanai da lokacin da za a gudanar da jana’izarsa daga baya.
Baikie ya shahara sosai wajen gina fannin ilimi a Najeriya, inda ya yi aiki a manyan makarantu da dama.
Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEA Gwamnatin Kano ta haramta kafa hukumar Hisbah mai zaman kantaYa taɓa zama Shugaban Jami’a a wasu jami’o’in Najeriya, kuma ya jagoranci wata jami’a a Kudancin Afirka a lokacin aikinsa.
An haifi Farfesa Adamu Baikie ne a Wusasa, Zariya a 1931 saidai ya girma ne Sabon garin Kano, inda ya yi karatun firamare kafin daga baya ya dawo makarantar middle a Zaria a shekarar 1948.
Ya zama farfesa na farko a ɓangaren ilmi daga Arewacin Najeriya a 1971.
Ana kallon da a matsayin jigo wajen kafa tsare-tsaren koyar da malamai, tare da samar da gudummawar da ta ɗore a bangaren ilimi na Najeriya.
Ya rasu ya bar ’ya’ya biyar.