Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin
Published: 15th, November 2025 GMT
Jakadan kasar Sin a Japan Wu Jianghao, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen Japan Takehiro Funakoshi a jiya Juma’a, inda ya bayyana matukar adawar kasarsa, da korafi a hukumance, dangane da kalamai marasa dacewa da firaministar Japan Sanea Takaichi ta furta dangane da kasar Sin.
Jakada Wu, ya ce munanan kalamai masu tayar da husuma na Takaichi, dangane da yankin Taiwan na Sin, wadanda aka jiyota tana yi kwanan baya, a majalissar dokokin kasarta sun sabawa hankali, sun tsallaka jan-layin kasar Sin, kana barazanar nuna karfi ne da neman takalar yaki.
Har ila yau, jakada Wu ya ce kalaman na Takaichi sun kasance matukar tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Sin, da keta dokar kasa da kasa, da ka’idojin cudanyar kasashen duniya, da manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da keta hurumin takardun siyasa hudu, wadanda Sin da Japan suka daddade, tare da matukar illata odar kasa da kasa bayan yakin duniya na 2, da tushen siyasa na dangantakar Sin da Japan.
ADVERTISEMENTDaga nan sai jakadan na Sin ya bayyana matukar bacin rai, da kin amincewar kasar Sin da hakan, da kuma mika kakkarfan sakon korafi, da adawa da matsayar firaminista Takaichi. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya
Da wadannan shaidu na zahiri, muna iya cewa himmar kamfanonin kasar Sin ta fuskar kirkire-kirkiren fasahohi, ya sanya hajojin kasar zama masu tafiya da yanayin zamani, wanda har kullum ake ta kokarin daidaita ci gabansa da bangaren kare muhalli, da aiwatar da matakai na inganta yanayin duniya.
Tun daga yankin kudu maso gabashin Asiya zuwa Turai, daga Latin Amurka zuwa gabas ta tsakiya har Afirka, ana ta ganin karuwar ababen hawa masu aiki da lantarki kirar kasar Sin, a wani yanayin dake shaida kwarewar kamfanonin kasar a fannin kirkire-kirkire fasahohi na zamani, wanda daga karshe ke dacewa da samar da hajoji irin wadanda kasuwannin duniya ke alfahari da kuma bukatar su. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA