2025-11-10@18:17:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8894

«Gwamna Namadi»:

    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya. Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar,  inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba. Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban. Hukumar kula da makamashin nukiliya...
    Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka. Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi. Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya “Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaron Nijeriya daga duk wata barazana da zata kawo ruɗani, da kuma gyara duk wani tarnaki a dangantakar mu da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa, don haka, ƴan Nijeriya su samu nutsuwa,” in ji Idris. Ministan ya ziyarci...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Argentina, Lionel Messi, wanda yanzu haka yake taka leda a ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bayyana burinsa na sake komawa Barcelona kafin ya yi ritaya daga tamaula, domin yin bankwana da masoyansa. Messi ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai filin wasan Camp Nou da aka yi wa gyare-gyare, inda ya ce ya yi matuƙar kewar filin da kuma magoya bayan ƙungiyar ta Catalonia. An kashe mayaƙa 200 a rikicin Boko Haram da ISWAP ’Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Litinin, ɗan wasan mai shekaru 38 ya ce: “Na yi kewar wannan fili ƙwarai. Ina fata wata rana zan...
    Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta birnin tarayya (FCT) ta saka ranar 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe da za a biya kuɗin Hajji na shekarar 2026, wanda aka tsara a N7,696,769.76. Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin hukumar a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda jami’in hulɗa da jama’a, Muhammad Lawal Aliyu, ya buƙaci duk masu niyyar zuwa Hajji daga Abuja su bi ƙa’idojin da aka shimfida. An bayyana cewa tabbataccen kuɗin Hajjin ya samu ne bisa ƙayyadadden tsari daga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), sannan duk biyan kuɗin za a yi ne ta hanyar Banki, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, ba tare da karɓar kuɗi a hannu...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da aikin gina hanya da kudinta ya kai Naira Biliyan 14 a Karamar Hukumar Malam Madori, wanda ke nuna jajircewar gwamnatinsa wajen bunkasa ababen more rayuwa1 karkashin shirin sabunta kudurori na gwamnatin tarayya wato “Renewed Hope Agenda.” A yayin taron kaddamarwar, an kuma gabatar da sabbin motoci ga shugabannin jam’iyyar APC guda takwas da masu tallata jam’iyyar a mazabar Arewa maso gabashin jihar, wanda Sanata Ahmed Abdulhamid Malam Madori ya dauki nauyi. Wannan mataki na da nufin karfafa hadin kai a jam’iyyar da kuma tallata hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadin jihar. A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yaba da jajircewar Sanata Ahmed Malam Madori...
    Maiyaki ya ce, “Gwamna Uba Sani kwanan nan ya ba da izinin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a karkashin rukunoni daban-daban.   “Za a ci gaba da yin hakan a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin inganta harkar lafiya a jihar.”   Maiyaki ya ci gaba da cewa, Gwamna Sani ya fifita harkar kiwon lafiya a gwamnatinsa, inda take gaba-gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5 November 10, 2025 Labarai Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta  November 10, 2025 Labarai Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC November 10,...
      Mazauna Millennium City a Jihar Kaduna sun zargi kamfanin wutar lantarki na Kaduna Electric da tilasta musu sanya mita da kuma ƙara farashin wuta ba tare da tuntuba ba. Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da MPH Estate, TUC Estate, Urban Shelter Estate, Yardan Allah Estate, Highfield Estate, Rahusa Estate, Danbushiya, Sabon Gari, Keke da Doka. Mazauna sun bayyana cewa an katse musu wuta na makonni saboda ƙin karɓar mitocin da kamfanin ya kawo. Sun ce matakin Kaduna Electric ya saba da umarnin Hukumar Kula da Lantarki ta Ƙasa (NERC), wadda ta tanadi cewa dole a tattauna da al’umma kafin a yi canjin mita ko a sauya tsarin biyan kuɗin wuta. Mazauna sun kuma yi ƙorafi cewa kamfanin...
    Shugaban ‘yan hamayyar siyasar kasar ta Kamaru Chiroma Bakary wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya fitar da wani sakon bidiyo da aka watsa a kafafen sada zumunta, da a ciki ya bayyana  mahukuntan kasar da ‘yan daba masu aikata ta’addanci.” Haka nan kuma ya kira yi mahukuntan kasar da su daina abinda ya kira       ” Nuna wariya ta kabilanci.” Har ila yau Chiroma ya fada wa mahukuntan kasar cewa; “Al’ummar Kamaru ba su son su, kuma sun dawo rakiyarsu.” A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar, Chiroma ne ya zo na biyu bayan Paul biya a bisa kididdigar hukumar zaben kasar. An bayyana cewa Biya ya sami kaso 53.66%, yayin da Chiroma ya sami kaso 35.19%. Shi dai...
    Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya ambaci cewa,  Mutum daya ya kwanta dama, sadaniyyar harin wani jirgin sama maras matuki na HKI akan wata mota a garin al-yasariyyah,dake gundunar Saida, a kudancin kasar. Majiyar tsaro ta fada wa kafafen watsa labaru cewa, jirgin saman maras matuki ya harba makamai masu linzami guda 3 ne akan motar da hakan ya yi sanadiyyar konewarta baki daya. Dama dai ma’aikatar lafiya ta Lebanon din ta sanar da shahadar wasu mutane biyu sanadiyyar hare-hare biyu da Isra’ilan ta kai a kudancin kasar, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata. Tun da aka tsagaita wutar yaki a watan Nuwamba 2024, HKI take ci gaba da keta ta, ya kai dubbai. A wani labarin daga...
    Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum. Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro. Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe. Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya. Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin”...
    Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.   “A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025...
    ’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa. Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane. “Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar. Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2...
    Pars Today – Kimanin masu jefa ƙuri’a miliyan 1.3 na Iraki sun je rumfunan zaɓe jiya, Lahadi (9 ga Nuwamba). An gudanar da wannan zaɓen na musamman kwanaki biyu kafin babban zaɓen ‘yan majalisar dokoki na Iraki, wanda za a gudanar a ranar Talata ta wannan makon (11 ga Nuwamba). An ci gaba da gudanar da zaɓen har zuwa ƙarfe 6 na yamma agogon ƙasar, bayan haka aka rufe akwatunan zaɓe ta hanyar lantarki. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar da cewa an shirya cibiyoyin zaɓe 809, ciki har da akwatunan zaɓe 4,501, a faɗin ƙasar don ranar zaɓen musamman. A wannan zagayen zaɓen, ‘yan takara sama da 7,744 daga ƙungiyoyin zaɓe 31 sun tsaya takarar kujeru...
    Pars Today – Jakadan Iran a Rasha ya sanar da cewa Tehran da Moscow sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Kazem Jalali, jakadan Iran a Rasha, ya rubuta a ranar Lahadi a dandalin sada zumunta na X cewa an cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Rasha don kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Ya kara da cewa wannan yarjejeniya ta samo asali ne daga tarurrukan da aka gudanar a ranakun 6-7 ga Nuwamba a Makhachkala tsakanin shugabannin tashoshin jiragen ruwa da na ruwa, manyan jami’an gwamnati, da daraktocin manyan kamfanonin kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen biyu. A cewar Pars Today, ya kara da cewa a lokacin wannan taron, an amince da tsarin da tsarin hadin...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi. A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a zaɓen 2027. Abdulmumin Jibrin ya sanar ta shafinsa cewa sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa. “Na samu kyakkyawar tarba daga dubban al’ummar mazaɓata ta Kofa, Bebeji, da ke Jihar Kano. “Taron ya yi ittifaƙin ficewa daga NNPP/Kwankwasiyya, mu koma APC, tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi wa’adi na biyu. An ƙara rage kuɗin aikin Hajjin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ta damu da ci gaba da karuwar zaman tankiya tsakanin Afghanistan da Pakistan bayan karuwar fadan kan iyaka tsakanin makwabtan biyu. A wata tattaunawa ta wayar tarho da Ministan harkokin wajen Afghanistan Mawlawi Amir Khan Muttaqi a wannan Lahadi, Araghchi ya ce Iran a shirye take ta taimaka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu na musulmi. Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya kuma jaddada muhimmancin inganta hulda da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da rabon ruwa daga kogin Harirud. Sojojin Pakistan da Afghanistan sun gwabza a watan da ya gabata, inda aka kashe mutane da dama  a tashin hankali mafi muni tun bayan da Taliban ta kwace iko...
    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar a ranar Lahadi cewa adadin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen da aka gudanar ya kai kashi 82.42%, wanda ya tabbatar da sahihanci da kyakkyawan tsarin gudanar zaɓen, a cewar hukumar. Shugaban Hukumar  Omar Ahmed, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa hukumar ta nuna daidaito da adalaci ga dukkan ‘yan Takara. Ahmed ya bayyana cewa hukumar ta sa ido kan tsarin zaɓe a duk faɗin jihohin ƙasar ta hanyar ƙungiyoyin da ke aiki, yana mai jaddada cewa sakamakon ya nuna jajircewar masu kaɗa ƙuri’a da kuma tafiyar da harkokin zaɓe cikin sauƙi da kuma sahihin tsari. A cikin wannan yanayi, mai ba da shawara kan harkokin shari’a na hukumar...
    Ministan Lafiya na Lebanon Rakan Nasser Eddine ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon, musamman a kudancin kasar, sunakara tsananta,  yana mai jaddada cewa rikicin ba wai kawai ya takaita ga wani yanki ɗaya ba ne, lamari ne da ya shafi kowace gida a Lebanon.” A lokacin ziyararsa a birnin Hermel da ke arewa maso gabashin Lebanon, Nasser Eddine ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi shahada ya karu daga 23 zuwa 28 a cikin watan da ya gabata, yana mai jaddada cewa waɗannan shahidai suna da iyalai da dangi da ‘yan uwa, kuma dole ne  ƙasa ta tsaya musu. Ya ƙara da cewa: “Dangane da wannan hari na  Isra’ila a kan ƙasarmu, sojojin Lebanon ba...
    Gwamnan yankin Darfur na Sudan, Bahreldin Adam Karamah, ya bayyana cewa shugabannin mayakan RSF sun aikata laifuka a El Fasher, yana mai jaddada cewa “ba za su iya ɓoye su ba.” A cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA), Karamah ya fayyace cewa shawarar da Majalisar Tsaro ta Sudan ta yanke, wacce shugabanninta suka goyi bayanta baki daya, ta tabbatar da cewa “babu wani sulhu da masu kisan gillar al’ummar Sudan.” Ya kara da cewa, “Ba za mu yi sulhu a kan wannan kasa ba, kuma ba za mu bari a sauke tutarta ko a lullube ta a cikin laka tare da ta wulakanta ta ba.” Gwamnan Darfur ya nuna cewa rikicin da ake...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma.   Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
    Babban jigo a jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Alhaji Sani Adamu Yarin Fika, ya sauya sheƙa zuwa APC da ke mulki a jihar. Yarin Fika, ya sanar da sauya sheƙarsa a wani biki da aka gudanar a Damaturu, inda ya ce ya yanke shawarar shiga APC ne saboda irin ƙoƙarin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi wajen ci gaban jihar. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya ce zai ba da gudunmawa wajen ganin Gwamna Buni ya ci gaba da nasarorin da yake samu a jihar. Tsohon ɗan takarar PDP, ya kuma bayyana cewa, dukkanin magoya bayansa a yankin sun bi sahunsa wajen...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin. Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics. Ya ce, gasar wasanni ta kasa ita ce babban bikin wasanni mafi girma a kasar Sin. Kuma yankunan Guangdong, Hong Kong da Macao ne suka hada hannu wajen shirya gasar wasannin ta kasa karo na 15. Ana kyautata zaton cewa, wannan gasar wasannin ta kasa ba wai kawai za ta bayyana sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu a sabon zamani ba ne, har...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji November 9, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15 November 9, 2025 Daga Birnin Sin Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba November 9, 2025
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin jihar Jigawa ta yi kira ga hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ta ba da kulawa ta musamman ga yan asalin jihar wajen daukar aiki. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin da babban likitan asibitin Dr. Salisu Mu’azu Babura da ma’aikatan asibitin suka kai masa ziyarar a gidan gwamnati dake Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar jihar Jigawa tana da kwararru da kuma masana da za su iya cike gibin guraben ayyukan lafiya a asibitin na Rasheed Shekoni. Gwamnan ya kuma bada tabbacin ci gaba da tallafawa asibitin don cimma nasarorin da aka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar za ta kari...
    ’Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari sansanin Hukumar Kwastam da ke Maje, a Ƙaramar Hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi, inda suka kashe wani jami’i guda ɗaya. Wani mazaunin yankin ya ce ’yan ta’addan sun zo da yawa, inda suka fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, sannan suka ƙone sansanin jami’an kwastam. Gwamna Kebbi ya gargaɗi manoma da makiyaya kan su zauna lafiya ko su fuskanci hukunci Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Ya ce, “Lakurawa sun zo da yawa, suna harbe-harbe ta ko ina. Sun ƙone sansanin kwastam tare da kashe wani jami’i.” Mai magana da yawun hukumar Kwastam a Jihar Kebbi, Muhammad Tajudeen, ya tabbatar da faruwar harin. Ya ce jami’an hukumar suna asibiti suna...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya gargaɗi manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Arewa, da su daina faɗa tare da zama lafiya, ko kuma su fuskanci hukunci a kotu. Gwamnan, ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon rikici, waɗanda yanzu ke zaune a harabar sakatariyar Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Kangiwa. Ya kamata duk ɗan Najeriya ya damu da barazanar Trump– Jigon APC Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga “Na zo ne don jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a dalilin wannan rikici, amma dole ne mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu,” in ji shi. Gwamnan, ya ce gwamnati ta fara bincike don gano musabbabin rikicin,...
    Iran ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin da ke tsakanin Pakistan da Afghanistan wanda ya kara ta’azzara kwanan nan bayan fadan kan iyaka mai muni da ya faru. Abass Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, yau Lahadi, inda suka tattauna dangantakar kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin. Mista Araghchi ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yanzu tsakanin Afghanistan da Pakistan, yana mai jaddada bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, tare da taimakon kasashen yankin masu tasiri, don sasanta takaddamar da rage tashin hankali. A watan da ya...
    Ministocin tsaro na kasashen Burkina Faso, Nijar, da Mali sun yunkuri anniyar kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa, wacce zata tunkari magance barazanar ta’addanci mai nasaba da kungiyoyin JNIM da ISIS a yankin Sahel. Kasashen sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a Niamey karkashin jagorancin shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani da ministocin tsaron kasashen da ke kungiyar kawacen sahel ta (AES). Ministocin tsaro na Mali, Sadio Camara; Burkina Faso, Célestin Simporé; da Nijar, Salifou Mody, sun sanar da shawararsu ta hanzarta aiwatar da aikin rundunar hadin gwiwa ta AES. Shawarwarin da aka amince da su sun tanadi musayar bayanan sirri, da kuma hadin guiwa ta fanin ayyukan soji. Kasashen na fuskantar barazanar kungiyoyin ta’addanci da suka...
    Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da mummunan ta’addancin da aka aikata kan fararen hula a yankin El-Fasher na Sudan. Ofishin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ya yi gargadin cewa El-Fasher ya zama birnin makoki a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare masu muni, wanda hakan ya haddasa wahalhalu marasa misaltuwa. A cikin wani bidiyo da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X, Li Fung, Wakiliyar Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ta ce: “A cikin kwanaki goma da suka gabata, yankin El-Fasher ya kasance wurin da ake samun karuwar hare-haren ta’addanci. A cewarta, “an kashe daruruwan mutane, ciki har da mata, yara, da wadanda suka...
      Shugaban reshen Akure na NBA, Mr. Friday Umar, wanda ya yi wannan kira, ya lura cewa “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi.   Ya ƙara da gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa shigar da ƙara a inda aka yi laifi don kiyaye mutuncin shari’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Labarai Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9,...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ce, kamfanon jiragen sama sun dakatar da zirga-zirga 1330 a jiya Asabar saboda ci gaba da rufe ayyukan gwamnatin tarayyar kasar dalilin rashin cimma matsaya akan kasafin kudi a Majalisun kasar. Masu sanya idanu akan kai da komowar jiragen sama ne su ka dakatar da aiki saboda ba za su karbi albashi ba, idan su ka yi aiki alhali ayyukan gwamnati suna a rufe. Hukumar filayen jiragen sama ta tarayyar Amurka ce ta sanar da cewa masu aikin kula da zirga-zirgar jiragen sama a hasumiyoyin dake cikin filayane jiragen sama 25 sun dakatar da aiki. Daga cikin garuruwan da tsaikon aikin ya shafa da akwai Chicago, Sanfarancisco, New York, New Rock da kuma Atalanta. Tashar...
    Wasu Karin kasashe takwas sun yi kira da a kama Fira ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila  Benjamine Netanyahu saboda laifukan yakin da ya aikata.  Kasashen Turkiya, Norway, Italiya, Canada, Slovenia da Lithuania, sun bayyana cewa a shriye suke su kama fira ministan na haramtacciyar Kasar Isra’ila. A kasar Turkiya mai shiga da kara na birnin Istanbul ya fitar da sammacin kamo mutane 37 masu hannu a kisan kiyashin Gaza daga cikinsu da akwai Netanyahu, ministansa na yaki, Kats, da babban hafsan hafsoshin sojan ‘yan sahayoniya Iyal Zamir. A ranar 21 ga watan Nuwamba 2024 ne kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta fitar da sammacin kamo Fira minista Netanyahu da tsohon ministansa na yaki Yoav Gallant saboda amfani da yunwa...
    Shirin Majalisar Dinkin Duniya Na Samar Da Abinci ( WFP) ya fitar da gargadi akan cewa, yankin gabashin DRC yana fama da matsananciyar yunwa.  Daraktar cibiyar ta WFP a kasar ta DRC Cynthia Jones ce ta yi wannan gargadin yana mai kara da cewa; Da akwai iyalan da suke tsallaken cin abinci, bayan da su ka sayar da kayan gidansu da kuma dabbobin da su ka mallaka.” Hukumar da yake kula da wadatar abinci ( IPC) ta ce da akwai mutanen da adadinsu ya kai miliyan 25 da suke cikin matakin karshe na yunwa, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3 da suke cikin hatsari. Hukumar ta MDD ta kuma ce, a halin yanzu mutane suna ta mutuwa saboda babu...
    Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi. Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo. ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyu Sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar. Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya...
    Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka.   Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9, 2025 Labarai Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza November 8, 2025
    Charles Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA, ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba. Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi. Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445. George Moghalu na jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401. Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban...
    Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kansila mai suna Nze Ala Kuru Orji yayin da ya fita jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe da ke ƙauyen Orumba, a yankin ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu, lokacin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewa, lamarin ya faru ne da ranar Asabar, a akwatin zaɓe na mazabar Ezukaka 1, da misalin ƙarfe ɗaya na rana. Ban taɓa zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Yaran Bello Turji sun kashe mutum 5, sun sace 9 a Sakkwato Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ana tsaka da jefa ƙuri’a sai wasu matasa da ke sanye da abun rufe fuska suka bayyana, suka harbe mutumin...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce faɗaɗa cinikayyar kan iyaka da hadin gwiwar tattalin arziki Tsakanin Iran da Pakistan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kuma habaka ci gaban kasashen biyu, yayin da ake kokarin samar da sabbin damammaki don ci moriyar juna a tsakaninsu. Da yake magana bayan dawowarsa daga ziyarar kwanaki uku da ya kai Pakistan ranar Juma’a, ya ce, “Idan aka habaka kasuwannin kan iyaka kuma ciniki da Pakistan ya ci gaba da bunkasa, to za a magance yawancin matsalolin rashin tsaro da kalubalen kan iyaka tsakanin kasashen biyu, domin mayar da yankunan kan iyaka zuwa cibiyoyin manyan ayyukan tattalin arziki zai rage fasa-kwauri da rashin tsaro, haka nan kuma  zai share fagen...
    ‘Yan sandan Tanzania sun kama Amani Gologowa, mataimakin sakatare janar na jam’iyyar adawa ta Chadema a ranar jiya Asabar, bayan zanga-zangar da ta barke bayan zaben makon da ya gabata. Hukumomi sun sanar da sunayen wasu mutane 9 da ake nema ruwa a jallo dangane da abubuwan da suka faru. Jam’iyyar Chadema da wasu mambobi na kungiyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam da dama sun yi ikirarin cewa, jami’an tsaro sun kashe mutane sama da 1,000 yayin da suke tarwatsa zanga-zangar, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su a matsayin marasa tushe, amma kuma gwamnatin ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu a hukumance ba. ‘Yan sanda sun sanya Gologowa da wasu mutane tara a cikin jerin...
    Tsohon Shugaban Amurka Biden ya yi dirar mikiya kan shugaba Trump cewa; Ba wai kawai yana lalata Fadar White House ba ne  har ma da dukkan al’ummar kasar Tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yi dirar mikiya kan magajinsa Donald Trump, yana mai cewa: Shugaban na yanzu ba wai kawai ya kawo wani abin kunya ga Fadar White House ba ce, har ma ga dimokuradiyyar Amurka. CNN ta ambato Biden yana cewa: A lokacin wani taron Jam’iyyar Democrat a Nebraska a yammacin Juma’a a Omaha: “Biden na cewa, ya san Trump zai kawo wani abin kunya a kasar, amma bai sani ba shin dole ne ya amince cewa akwai wani abin kunya da ya riga ya faru.” Biden yana magana...
    Daga cikin ƙorafe-ƙorafen da masu ƙara suka zayyana sun haɗa cewa, ya danganta halittar Annabi SAW da ƙasƙantun halittu (‘Ya’yan Tumkiya, da Karya, da Ƙwarƙwata), sannan kuma ya taɓa alfarmar iyayen Annabi SAW wanda a cewarsu, hakan bai dace ba a alfarmarsa fiyayyen halitta.   Gwamnatin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba tare da ɓata lokaci ba, ta miƙa koken ga Majalisar Shura ta jihar domin fayyace gaskiyar lamari.   Majalisar Shura, ta bakin Sakatarenta, Shehu Wada Sagagi, a wani taron manema labarai da ta gudanar, ta tabbatar da cewa, za ta gudanar da cikakken bincike akan zargin da aka yi wa Malamin (Abubakar Triumph). Sannan kuma, za ta gayyaci masu ƙorafe-ƙorafe da kuma Malamin domin sauraron bayanansu....
    Ministan Kasa a Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Bello Muhammad Goronyo, ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna har zuwa Kano, da kuma wasu manyan tituna a Arewacin ƙasar nan. Ministan, Barrister Bello Goronyo (ESQ), ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara don duba yadda aikin ke gudana, domin tabbatar da cewa ana sa idanu sosai, kuma ‘yan kwangila suna gudanar da aikin cikin inganci da nagarta. Ministan ya fara duba aikin tun daga Tungan Maje, Madalla, Zuma Resort, Sabon Wuse, Jere, Abuja Junction, Gwanin Gora, sannan ya ci gaba zuwa Zaria har zuwa Kano, inda aikin ke ci gaba yadda ya dace. Haka kuma,...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun  tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar a ranar Asabar, Abdelatty ya yi nazari kan ci gaba da kokarin da Masar ke yi na karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa. Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya zuwa mataki na biyu na shirin tsagaita wuta, wanda zai  magance matsalolin siyasa da ayyukan  jin kai domin samun...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi November 8, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025
      Kazalika, duk dai a jiya Jumma’ar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da taron, Chen Binhua, mai magana da yawun Ofishin Harkokin Taiwan na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ya ce taron wanda ya gudana shekaru goma da suka gabata ya karfafa muhimmiyar rawar da Yarjejeniyar 1992 ta taka a matsayin ginshikin siyasa ta bunkasa zaman lumana a dangantakar bangarori biyu na mashigin tekun, kana matukar an ci gaba da amincewa da Yarjejeniyar 1992 kuma aka nuna adawa da batun “‘yancin kai na Taiwan”, to dangantakar bangarorin biyu za ta iya bunkasa cikin lumana kuma za a iya kara inganta muradun ‘yan kasa da ke bangarorin biyu na mashigin tekun. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga...
    Wasu ’yan bindiga da Bello Turji ke jagoranta sun kai hari ƙauyen Bargaja da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato da safiyar ranar Asabar. Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe mutum biyar, tare da jikkata wani ɗan sa-kai, sannan suka sace wasu mutum tara waɗanda mafi yawansu mata ne. Ban ɓata zargin Shettima da ƙirƙiro Boko Haram ba — Sheriff Uwargidan Gwamnan Gombe ta nemi a tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata Kafin faruwar harin, wani mai ɗan gwagwarmaya a yankin mai suna Basharu Altine Guyawa, ya wallafa a kafafen sada zumunta inda ya yi gargaɗin cewa Bello Turji da tawagarsa suna shawagi a yankin Fadanar Tursa da Dorawar Madugu zuwa Dan Huntuwa ta gadar...
    BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”.   Somalia (1992–1994) Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s. A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya. Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida. Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen...
    Rahotanni sun nuna cewa dan wasan Taekwando na kasar Iran mai suna Abulfazl zandi ya zamo shi ne na daya a duniya a bangaren maza a ma’aunin kilograme 58, bayan yayi nasarar samun lambar yabo ta zinariya a gasar taekwando ta duniya a kasar China, Hukumar kula da wasan taekwando ta duniya ta fitar da sunayen wadanda suka yi fice a duniya a watan nuwamba, inda ta sanya gasar teakwando ta duniya da aka yi a kasar china , yan wasan kasar Iran da dama maza da mata sun samu gagarumin ci gaba a jerin fannonii daban daban na wasanni. Zandi  ya zo na daya a duniya  da maki 170.80  kuma yana mataki na 4  a bangaren Olympic, A gefe...
    Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa. Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025 Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025
    A bana ne ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, gami da kawo karshen mulkin mallakar kasar Japan a yankin Taiwan da dawo da shi kasar Sin. Kwanan nan ne CMG wato babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin ya wallafa jerin wasu rahotannin talabijin guda biyar dangane da batun dawowar Taiwan kasar Sin. ’Yan jarida ma’aikatan CMG ne suka dauki rahotanni da bidiyo a yankin Taiwan, inda suka yi amfani da kwararan shaidun tarihi, don mayar da martani ga wasu kalaman karya da ke cewa wai “matsayin Taiwan ba shi da tabbas”, tare kuma da bankado markarkashiyar mahukuntan jam’iyyar DPP...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida. Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri. Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu. Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025 November 7, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku  November 7, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka November 7, 2025
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci. Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame...
    Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano: Haduwa da kawayen banza da kuma kuntatawa da wasu malaman suke nuna musu, saboda kin amincewa da su na bukatun da suke nema a wajensu. Da yawa iyayen ba sa tsayawa su saurari matsalolin ‘ya’yansu kan abin da ke damunsu a makaranta, da kuma rashin bibiyar karatunsu da abokansu. Iyaye su tabbatar da suna bawa yara kudi da kayan abincin da zai ishesu idan a makarantun kwana suke, sannan su tabbatar da tarbiyyar malaman da za su kai yaran nasu. Sunana Aisha Isah Gama (Mai Waka), Jihar Kano: A gaskiya abin da ke janyo wa baya wuce gurba tattun abokai, har da lefin malamai saboda malami ne za ka ga ya kulla...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
    Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi.   Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.”   Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
    Kotun koli ta tarayyar Najeriya ta tsayar da ranar 20 ga watan nan na Nuwamba domin zama shari’ar shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara Nnamdi Kanu. Zaman shari’ar da za a yi zai mayar da hankali akan tuhumar ayyukan ta’addanci da ake zargin shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafara din da aikatawa. An bai wa Kanu kwanaki shida a jere domin ya kare kansa akan zargin ta’addancin, sai dai bai iya yin hakan ba. A jiya Juma’a Kanu ya gabatar da nashi bayanin akan cewa; Ai daina daukar ta’addanci a matsayin laifi a Najeriya, domin an yi wata sabuwar dokar da ta maye gurbin tsohuwar da ake da ita akan hakan. Har ila yau Kanu ya ce babu wata madogara ta doka...
    Yanda ake amfani da shi: A dan dumama man zaitun a wuta, kar ya yi zafi da yawa yanda zai kona fata. Sai a shafa a gurin da nankarwar ta ke. A yi hakan da safe da yamma a kullum. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ado Da Kwalliya Yadda Za A Magance Amosanin Baki October 4, 2025 Ado Da Kwalliya Hadin Tsumin Baure September 27, 2025 Ado Da Kwalliya Gyaran Fuska Da Laushin Fata August 30, 2025
    Bisa ga imanin da yake da shi ya bayyana cewa “Ba za ka iya samar da zaman lafiya da bama-bamai ba; sai dai ka gina shi da amana,” ya kaddamar da abin da yanzu ake kira ‘Samfurin Zaman Lafiya na Kaduna’.   Tsarin Hadin Gwiwa:r Gwamnatin Kaduna Da ofishin ONSA A tsakiyar wannan sauyi akwai hadin gwiwa mai karfi a tsakanin Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) da Gwamnatin Jihar Kaduna. Tare suka kafa kwamitin fasaha na hadin gwiwa wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki, masana halayyar dan’Adam, da shugabannin kananan hukumomi, wannan tawaga ba ta zo da tankoki ko jiragen yaki ba, ta zo da tausayawa, tattaunawa da bayanai. A babban aikinsu na farko, ’yan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.” Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka...
    A cewar ‘yansanda, “A ranar 10/10/25, an gayyato wani Mista Oke Emmanuel, dan NYSC kuma abokin dakin wanda ya bace, domin yi masa tambayoyi. Ya tabbatar cewa wanda ake nema ya kasance tare da iyalan George har zuwa 06/10/25. “An samu karin bayani daga George cewa dan NYSC din ya koka da rashin lafiya, aka kai su Asibitin Kaiama Referral Hospital a ranar 04/10/25, kuma aka sallame shi ranar 05/10/25. Sai dai a ranar 06/10/25, dan NYSC din ya bace zuwa wani wurin da ba a sani ba.” ‘Yansanda kuma suna binciken zargin karbar kudin rashawa na Naira 100,000 daga iyayen wanda ya bace, da wasu fursunoni biyu da ke gidan gyaran hali na Igbara, Abeokuta, Jihar Ogun, wadanda suka...
    Sanarwar ta ce, “A ranar 2 ga Oktoba, 2025, misalin karfe 08:25 na safe, wani mutumin kirki ya kai rahoton kisan gilla a ofishin D Dibisional Police Headkuarters. “Rahoton ya bayyana cewa wasu mutane biyu sun je gidan wani Ahmad Lawan, namiji, mai shekaru 29, wanda ake kira Soje, mazaunin Sabon Kasuwa, wanda ake zarginsa a matsayin shahararren dan sara-suka.” “Suka kwankwasa kofar gidansa, bayan da ya bude, sai suka soka masa wuka a kirji sannan suka tsere zuwa wani wuri da ba a sani ba.” Wakili ya bayyana cewa jami’an da ke karkashin D’ Dibision, karkashin jagorancin DPO CSP Mubarak Sani Baba, “sun hanzarta zuwa wurin da abin ya faru, suka dauki wanda abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa...
    Tun da farko, Daraktan DSS na Jihar Kaduna, Mr. Hakeem Abiola, an shirya taron ne domin nazarin ƙalubalen aiki da kuma karfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa hukumar DSS a ƙarƙashin jagorancin Mr. Oluwatosin Adeola Ajayi tana amfani da dabaru biyu – na ƙarfi da na sulhu – domin tabbatar da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai da na al’umma kamar JNI da CAN ya taimaka wajen shawo kan rikice-rikice kafin su zama tashin hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa. Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse. Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana. Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a...
    Ya ci gaba da cewa, rungumar wannan tsari; zai kuma taimaka wajen yakar yunwa a kasar nan, inda ya yi nuni da cewa; ana aiwatar da wannan dabarar yakar sauyin yanayi ne ta hanyar yin amfani da dabarun noman gargajiya, wato yin amfani da takin gargajiya da sauyawa daga gonar da aka yi noma zuwa wata gonar daban. Sauran dabarun ya bayyana cewa, sun hada da yin shuka da ingantaccen Irin noma da kuma yin noman rani. Kazalika, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya wannan tsari ya zama na kasa baki-daya da za a rika yin amfani da shi. Shi ma a nasa jawabin a wajen taron, Shugaban Jami’ar Farfesa Suleiman Bala-Mohammed ya ce; kasidar da aka...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a. Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya gana da Shugaban Ƙasa ba tare da ’yan jarida ba. Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Ganawar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya gana da Archbishop Ignatius Kaigama na Katolikan Abuja, a wani yunƙuri na inganta dangantakar addinai da zaman lafiya a Najeriya. Ko da yake ba a bayyana abin da suka tattauna ba, amma ganawar ba za ta rasa nasaba da ƙarfafa...
      A nata tsokacin kuwa, kwamishiniya mai lura da ababen more rayuwa da makamashi a hukumar zartarwar kungiyar AU Lerato Dorothy Mataboge, kara tabbatar da alaka ta yi tsakanin hadin gwiwar Sin da Afirka, da burin da ake da shi na bunkasa masana’antu a sassan nahiyar.   Mataboge ta kara da cewa, yunkurin bunkasa samar da masana’antu a Afirka na bukatar karfafawa ta hanyar gina kwarewa, da horar da sana’o’i, da samar da cibiyoyi da albarkatun al’umma, don haka ta yi kira da a hada karfi-da-karfe wajen tsara shirye-shiryen bunkasa sanin makamar aiki a cikin gida, da samar da cibiyoyin horo masu nagarta, don horar da jama’a fasahohin amfani da makamashi marar gurbata yanayi. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
    “Mutanen duk sun manta da ‘yan garancin da suka yi gaba dayansu suka shiga wani sabon babi. Babban bango da ake ingina da shi ya fadi. Yanzu Kudancin Kaduna na jam’iyyar APC ne.” Ya yi bayanin komawar manyan mutanen biyu zuwa APC wani kokarin ci gaba ne na shi Kakakin majalisar, ya ce SHugaban majalisar ya kara jadddad Sanata Katung da Honorabul. Amos “sun zabi lamarin kawo ci gaba ne. Sun zabi su ci gaba da kasancewa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne da kuma APC. Wannan ba karamin sauya jam’iyya bane. Jirgizar kasa ce ta siyasa. Wani sabon babi ne ga siyasar Kudancin Kaduna, da kuma gaba dayan Nijeriya.” “’Yan ‘uwana maza da mata wannan sauay shekar wani...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birni Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassa Abu Turabi Fard, ya bayyana cewa; Tsayin dakar da kungiyar Hizbullah ta Lebabon da Ansurllah na kasar Yemn da kuma al’ummar Iran su ka yi wajen fada da masu girman kai na duniya, sakamako ne na koyarwar alkur’ani maigirma, Ahlul Bayt ( a.s) da kuma Ashura da jagorar matan duniya Fatima az-Zahra ( a.s). Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya ambato limamin na birnin Tehran yana kuma cewa; Makarantar gwgawarmaya tana yi wa zuriya bayan zuriya tarbiyya akan riko da gaskiya da kuma kalubalantar masu danniya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
    Tarayyar turai ta bayyana cewa ma’aikatan Agaji ba za su iya isha cikin garin Al-fahar ba,kuma birnin ya zama tamkar makabarta. Tarayyar turai din ta  bakin mai Magana da yawunta Eva Herneserova ta kuma ce; Sudan ta zama daya daga cikin kasashen da gudanar da ayyukan agaji ya tsananta a duniya,kuma har yanzu da akwai fararen hula da aka killace su adaidai lokacin da ake ci gaba da kai wa asibitoci hare-hare. Eva Herneserova ta kuma ce; Babu sauki ko kadan a kokarin shiga cikin birnin domin isar da kayan agaji. Ma Magana da yawun kungiyar tarayyar turai din ta kuma yi gagradi akan cewa bai kamata a rika amfani da yunwa da kuma kisan kiyashi a matsayin makamin yaki...
    Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
    Kwamandan Ƙungiyar sa kai ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) reshen Jihar Kaduna, Abdulwahab Muhammed ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta amince da Ƙungiyar a matakin ƙasa ta hanyar sanya hannu a kan ƙudurin da aka gabatar. A cewar ƙungiyar bisa la’akari da irin rawar da take takawa wajen daƙile ayyukan miyagu da samar da tsaro a sassan ƙasar nan. An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta sa hannu kan kudurin amincewa da kungiyar domin kasancewa cikin jerin hukumomin tsaro na kasa, la’akari da irin jajircewar da suke nunawa musamman a Jihar Kaduna. Abdulwahab...
    3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
    Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 ​​a cikin  masai. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a. Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai. “Hukumar kashe gobara ta...
    Wata kotu a Ƙasar Jamus ta yanke wa wani ma’aikacin jinya hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin kashe marasa lafiya 10 da kuma yunƙurin kashe ƙarin wasu 27 ta hanyar yi musu allurar guba. Kotun da ke birnin Aachen a yammacin Jamus, ta tabbatar da cewa mutumin mai shekaru 44 ya aikata laifukan ne tsakanin watan Disamban 2023 zuwa Mayun 2024 a asibitin Wuerselen. Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kotun ta bayyana cewa laifin da ya aikata babban laifi ne, wanda zai hana shi samun ’yanci bayan shekaru 15 kamar yadda ake yadda...
    “A yayin da ake tarwatsa masu kai harin, DPO na Sassan A da B sun tura ma’aikatansu suka harba hayaki mai sa hawaye, amma wasu motoci cikin motar gwamnan sun lalace,” in ji Abiodun. Ya bayyana cewa mutane uku na farko da ake zargi sune Ali Mohammed da Adamu Hussain, dukkansu daga yankin Nasarafu, Bida, da Isah Umaru na yankin Darachita, Bida. Ya kara da cewa an kama Nagenu, mai shekaru 39, daga yankin Bello Masaba, daga baya dangane da wannan lamari, sannan ya ambaci wasu biyu, Salihu Mohammed da Abdulrahman Baba, yayin tambayoyi. “Dukkan wadanda ake zargi suna karkashin bincike kuma suna taimaka wa ‘yansanda wajen gano wasu. Ana ci gaba da kokarin kama karin mutane da ake zargi,”...
    Ina gaishe da Mamana da Babana, sai kannena Labiba, Nasira, Fati, Maimuna, Khairat, da yayyene Yaya Muhammad, Yaya Ibrahim, Yaya Maryam, Yaya Abu, Yaya Larai. Sannan malaman makarantarmu na boko da islamiyya, Malama Aisha, Malama Kubra, Malam Isah, Malam Nuhu, Malam Yahyah, Malama Batulu, ai kawayena na boko da na islamiyya kamar su Wasila Sabo, Fatima Muhammad, Hauwa Yunus, Walida Tahir, da dai sauransu. Da fatan sunyi Juma’a lafiya. Sako daga Ummu’aimana daga jihar Gombe: Ina gaishe da Mahifana, da fatan Allah ya kara masu lafiya da nisan kwana, sai y’an’uwa, makoftana, dama kawayena irinsu Zahra’u(maman daddy), Bara’atu Saleh, Shafa Liman mai turare, Asiya Muhammad Tayo (maman Shahid), sai Binta Usman,p Jummai, Yahanasu Jabir, Fatima Jafar, Alhaji Abdulkadir Abdullahi, Zakiyya,...
    “Wannan mummunan hari ya yi sanadiyyar mutuwar jaruman jami’an tsaro da suka sadaukar da rayukansu wajen kare shi,” in ji sanarwar. Majalisar ta yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu, da hukumomin tsaro, da al’ummar jihar Neja, tare da yi wa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙin cikin gaggawa. A ƙarshe, Majalisar Wakilai ta sake tabbatar da jajircewarta wajen ganin an tabbatar da tsaron jama’a da jami’an gwamnati. Ta yi alƙawarin ci gaba da bai wa ɓangaren zartarwa da hukumomin tsaro goyon bayan doka wajen yaƙi da ta’addanci, da fashi da makami, da sauran nau’o’in laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa...
    Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna...
    Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawat 1 a garin Talasse, karamar hukumar Balanga. Aikin, wanda aka kulla ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Bankin Duniya, da kamfanin MIDS Dynamics, na da aniyar samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba ga sama da gidaje 8,000 a Talasse da kauyuka makwabta, idan aka kammala shi cikin watanni huɗu. Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 A wajen bikin kaddamar da aikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana shi a matsayin muhimmin ci gaba a...
    ’Yan sanda a kasar Indonesia sun ce an garzaya da daruruwan mutane zuwa asibiti bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a wani masallacin Juma’a da ke Jakarta babban birnin kasar. Lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma’a a cikin wani ginin makaranta da ke Kelapa Gading, a arewaci Jakarta. Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Kwamishinan ’yan sandan birnin, Asep Edi Suheri, ya ce har yanzu ana bincike don gano musabbabin fashewar. Shaidun gani da ido sun ce sun ji fashewa biyu masu ƙarfi da misalin ƙarfe 12 na rana a agogon kasar, daidai lokacin da aka fara hudubar sallar Juma’a...
    Dangane da fargaba game da karancin abinci na amfanin gona da aka canza jinsinsu (GMOs), farfesan ya ce domin tabbatar da lafiyar abinci da kare lafiyar jama’a, dole ne kowace iri da za ta shigo kasar ta bi matakan doka da ka’idoji da ke tabbatar da cewa tana da aminci. Ya ce, dokokin da ake amfani da su wajen kula da GMOs ma sun fi tsauri fiye da na amfanin gona na gargajiya saboda an kara musu sinadaran halittu (genetic materials). “Kafin a saki kowane irin amfanin gona domin a fara amfani da shi a kasuwanci, dole ne ta bi diddigin binciken halittu da sinadaran gina jiki sosai. Bayanai da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa amfanin...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza. Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin...
    Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da dage takunkumin da ya sanya wa al-Julani Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a ranar Alhamis domin amincewa da daftarin kudirin da zai cire takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Shugaban rikon kwaryar kasar Siriya Abu Muhammad al-Julani da Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Anas Khattab, inda kasashe 14 suka kaɗa ƙuri’a kan amincewar, yayin da kasar China ta kauracewa kada kuri’a. Daftarin kudurin, wanda Amurka ta rubuta kuma ta gabatar, ya yi kira da a dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa al-Julani da Khattab. A cewar jami’an diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya, ofishin jakadancin Amurka ya rarraba daftarin kudurin ga mambobi, kuma an...
    Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya a daidai lokacin da ake kara samun karuwar fada a Darfur da El Fasher Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa: Matsalar karancin abinci mai gina jiki ta kara ta’azzara a Sudan, yana mai tabbatar da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan. A halin yanzu, shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar na tabbatar da tsaron dukkan iyakokin Sudan da kuma murkushe ‘yan tawayen. Wani sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Sudan a kan gaba wajen fuskantar bala’in...
      ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an November 6, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025 Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025
    Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru. Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci. A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho November 7, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria October 25, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life October 25, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025 Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  November 7, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT November 6, 2025
    Shugaban ya kuma yaba bisa gudunmawar da kwararrun matasa ke samar wa, musamman masu yiwa kasa hidima da ke yin aikin yiwa kasa hidama, a Hukumar ta NPA. Ya danganta su a matsayin matasan gobe da za su samar da sauyi wajen ci gaba da bunkasa fannin tattalin azrki na Teku da kuma ga daukacin tattalin arzikin kasar nan. An kirkiro da wannan ranar ta NMD ce, a shekarar 2014 wadda kuma aka kaddamar da ita a kasar Ingila a shekarar 2016, wadda kuma ake gudnar da bikin zagoywar ranar, a duk ranar 27 na watan Okutobar kowacce shekara. Kazalika, gudanar da bkin wannan ranar, ta yi daidai da cimma muradun karni, na Majalisar Dinkin Duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
    A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Trump ya sake mayar da Nijeriya matsayin kasa mai matukar damuwa, sannan ya yi gargadin cewa; “idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bayar da izinin kashe kiristoci, nan take Amurka za ta dakatar da duk wani taimako da take bai wa Nijeriya, sannan kuma mai yiwuwa ta shiga kasar, domin kakkabe ‘yan ta’addan Islama da ke aikata wadannan munanan ayyuka na ta’addanci.” Kazalika, ya kuma umarci Ma’aikatar Yakin Amurka, da ta shirya domin daukar mataki. Pete Hegseth, Sakataren Yakin Amurka, a ranar Asabar ya ce; Ma’aikatar Yaki na shirin daukar mataki. Barazanar Trump dai, ta biyo bayan zargin da wani dan majalisar dokokin Amurka, Ted Cruz, ya yi a shafinsa na D,...
    Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na shiyyar Abuja (AEDC) ya fara aikin rage ma’aikata kusan 800, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da fama da hauhawar farashi, tsadar rayuwa, da rashin tabbas wajen samun wutar lantarki. Matakin korar wanda ta fara a ranar Laraba, ya biyo bayan watanni na sake fasalin cikin gida a kamfanin da ke ba da wutar lantarki ga Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Kogi, Neja da Nasarawa. Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa shugabannin kamfanin sun fara ne da shirin korar ma’aikata 1,800, kafin su rage...
    Sai dai, bisa batun gasakiya, karya ce tsagwaronta kan batun kisan kiyashin da ake yamadidin cewa, ana yiwa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya. Bugu da kari, wannan batun ana wani yunkuri ne na son kawo rudadi a kasar nna, musamman duba da cewa, masu son kawo rudadin, a zahiri, sun jahilci irin yanayin sarkakiyar lamarin tsaro na kasar nan. Wannan Jaridar, ta sha yin tsokaci, kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar nan, tare da kuma yawan gabatar da kira ga Gwamnatin kasar da ta tashi tsaye, domin daukar matakan da suka dace, na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya. Batun aikata ta’addanci, yin garkuwa da mutane da kuma aukuwar rikici a tsakanin manoma da makiyaya, matsaloli ne, da...
    An rantsar da Paul Biya mai shekaru 93 a matsayin shugaban kasar Kamaru karo na takwas a majalisar dokokin kasar da ke Yaoundé. Ya shafe shekaru 43 yana mulki, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai. Biya wanda shine shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na kuri’un zabe, yayin da abokin hammayarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar kasa. Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaben, yana zargin cewa an yi maguɗi,wanda hukumomi suka musanta. Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi. Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alkawarin dawo da doka a kasar...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan yace rarrabuwa da sabanin tsakanin musulmi shi ne babban abin da makiya musulunci suke so, kuma yayi gargadin cewa rabe-rabe na cikin gida yana kare manufofin makiya ne da kasashe ma’abota girman kai na duniya. shugaban ya fadawa manya- manyan malaman Ahalus sunna da sauran malaman addini dake Sanandaj a yammacin lardin Kurdistan cewa ta hanyar hadin kai da rikon amana da kuma riko da yan uwantaka na musulunci ne kawai  musulmin duniya za su iya tunkarar makircin Amurka da Israila da ma sauran yan sahayuniya. Har ila yau ya kara da cewa wannan rarrabar ce isra’ila da Amurka da sauran yan sahyuniya na duniya suke so, domin su shagaltar da kasashen musulmi su yi...