Aminiya:
2025-11-03@08:00:48 GMT

Dadiyata: Buhari ya gaza nemo shi, Tinubu yana da lokaci — Amnesty

Published: 3rd, August 2025 GMT

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta ce Gwamnatin Tarayya ta yi sakaci game da ɓacewar ɗan gwagwarmaya Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

A wata sanarwa da ta fitar, Amnesty, ta ce abin takaici ne ganin cewa shekara shida kenan da Dadiyata ya ɓace ba tare da wani sahihin bayani ba.

Mutum ɗaya ya rasu, an jikkata wasu yayin arangama da ’yan sanda a Abuja Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja

Dadiyata ya ɓace ne a ranar 2 ga watan Agustan 2019, bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun shiga gidansa da ke unguwar Barnawa a Jihar Kaduna, suka tafi da shi.

Tun daga wannan lokacin, iyalansa da abokansa ke jiran jin wani abu game da ɓacewarsa, amma har yanzu babu bayani.

Shugaban Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce Dadiyata mutum ne mai kishin ƙasa kuma yana da kishi wajen faɗin gaskiya a kafafen sada zumunta.

Ya ce akwai yiwuwar ɓacewar Dadiyata na da alaƙa da irin sukar da yake yi wa gwamnati da wasu ‘yan siyasa.

Ko da yake gwamnati ta musanta cewa tana da hannu, Amnesty ta ce dole gwamnati ta ɗauki alhakin binciken abin da ya faru da bayyana gaskiya domin rage wa iyalan Dadiyata raɗaɗi.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci hukumomin tsaro su yi bincike mai zurfi, su kuma bayyana sakamakon da suka samu.

Ta ce abin takaici ne a ce shekara shida kenan ba tare da wani bayani dangane da ɓacewarsa ba.

Hakazalika, Amnesty ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ya sa baki cikin lamarin domin a san halin da ake ciki.

Ta ce lokaci na ƙurewa, iyalan Dadiyata suna buƙatar amsa guda ɗaya kan inda ya shiga.

Wanda suka halarci taron manema labaran sun haɗa da matarsa Khadija Lame da ƙaninsa Usman Idris.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buhari Ɓacewa Dadiyata gwagwarmaya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.

“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.

Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.

“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.

Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.

“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya
  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Maganin Nankarwa (3)
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai