Babu wani gwamna da zai yi ƙorafin ƙarancin kuɗi a mulkin Tinubu — Sanwo Olu
Published: 12th, November 2025 GMT
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi.
Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna.
Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa shugabanni, masana, matasa, da ’yan kasuwa domin nazarin cigaban ƙasar tun bayan zuwan sabuwar gwamnati.
Sanwo-Olu ya yaba da jajircewar ’yan Najeriya tun bayan samun ’yancin kai, yana mai cewa ƙasar ta fuskanci ƙalubale da dama amma tana ƙara ci gaba ta hanyar ƙarfin haɗin kai.
“Yanzu labari ya sauya. Ka tambayi kowanne gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma, zai gaya maka yadda kuɗaɗen shiga suka ƙaru a zamanin Shugaba Tinubu. Yanzu akwai isasshen kuɗi domin aiwatar da muhimman ayyuka da jama’a za su amfana,” in ji shi.
A cewarsa, tsakanin shekarar 2023 da 2024, an samu ƙarin kaso 62% a rabon kuɗaɗen tarayya ga jihohi, yayin da ƙananan hukumomi suka samu ƙarin kaso 47%.
Ya ƙara da cewa, sabbin dokokin haraji da suka rage kasafin Gwamnatin Tarayya daga kashi 15% zuwa 10% na harajin kayayyaki (VAT) sun nuna yadda Shugaba Tinubu ke son ƙarfafa ikon jihohi.
“A tsarin haraji na yanzu, jihohi ke karɓar kashi 55% na VAT, yayin da ƙananan hukumomi ke samun kashi 35%. Wannan wata babbar nasara ce don tabbatar da cewa jama’a sun ɗanɗani tasirin mulki,” in ji shi.
Sanwo-Olu ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa tabbatar da bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kai, yana mai cewa hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da hakan wani muhimmin tarihi ne a tafiyar dimokuradiyyar Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa babban sauyin da Shugaba Tinubu ke shirin kawowa nan gaba shi ne na ƙirƙirar rundunar ’yan sanda ta jihohi, wanda ya ce “an daɗe ana buƙatar hakan kuma ya zama wajibi.”
Sanwo-Olu ya bayyana Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) a matsayin tsarin haɗin kai wanda ke ƙoƙarin gina ƙasa ɗaya mai ɗorewa ta hanyar tabbatar da adalci a tsakanin yankuna da kawo ci gaba.
Ya kuma yi kira ga shugabanni da su yi hobbasa kan tubalin da wadanda suka kafa ƙasar suka bari, musamman irin su marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato da ya ce “nauyinmu ne gina Najeriya mai ƙarfi don al’umma masu zuwa.
“Za mu ci gaba da tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce mai ƙabilu, addinai, da al’adu mabambanta amma al’ummarta sun haɗu a ƙaunar ƙasa. Abin da ke haɗa mu ya fi abin da ke raba mu,” in ji shi.
A nasa jawabin, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Pius Anyim Pius, wanda shi ne shugaban taron, ya ce tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki muhimmin ginshiƙi ne ga nasarar kowace gwamnati.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamna Jihar Legas Sanwo Olu ya tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC
Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027.
“A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA