Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump bisa zargin kisan Kiristoci
Published: 9th, November 2025 GMT
A Najeriya an yi zanga zangar yin Allah wadai da barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji kan kasar bisa zargin gwamnatin kasar da kauda kai kan kisan da ake wa kiristoci a kasar.
Masu zanga-zanga a Kano, dake arewacin Najeriya, sun yi Allah wadai da barazanar da kuma yin watsi da ikirarin na Trump na “kisan kiyashin Kiristoci.
Masu zanga-zangar sun zargi Washington da amfani da addini domin tsoma baki da a cikin harkokin cikin gidan Najeriya, suna gargadin cewa duk wani matakin soja na Amurka zai keta hurumin Najeriya.
A ranar 1 ga Nuwamba, ne Trump ya ce ya umarci Pentagon da ta shirya daukar matakin soji a Najeriya, yana mai ikirarin cewa wannan shiri an yi shi ne don kare Kiristoci.
Sannan ya yi barazanar dakatar da duk wani tallafi ga kasar” idan gwamnatin Najeriya “ta ci gaba da yin biris ga kisan Kiristoci, Kalaman da suka haifar da fushi a fadin Najeriya.
Kungiyoyin fararen hula da masu sharhi kan siyasa sun zargi Trump da yada labaran karya da kuma haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma.
Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wadannan zarge-zargen da kakkausar murya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin da aka aikata a El-Fasher November 9, 2025 Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila November 9, 2025 An Kafa Mutum-mutumin Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran November 9, 2025 Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati November 9, 2025 Wasu Kasashe Takwas Sun Bukaci Ganin An kama Benjamine Netanyahu November 9, 2025 WFP: Ana Fama Da Matsananciyar Yunwa A Gabashin DRC November 9, 2025 Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro November 9, 2025 Tanzania: ‘Yan sanda sun kama wani babban jigon adawar siyasa November 9, 2025 Martanin Iran ya haddasa wa Isra’ila hasarar fiye da Dala Miliyan 200 November 9, 2025 Biden Ya Caccaki Trump Bisa Tuhumarsa Da Kawo Barna November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta buɗe kofofin tattaunawa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, dangane da barazanar kasar ta kaddamar da yaki a Najeriya.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce gwamnatinsu ba ta son ƙara yin yamadidi da maganar.
An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa“Babban nauyin da ke kanmu a matsayin gwamnati shi ne tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar mataki a kan duk wata damuwa ta gaskiya da ke da alaƙa da tsaron ’yan ƙasa.
“Amma ba ma cikin yanayin firgici. Muna mayar da martani cikin natsuwa, hankali, da kuma la’akari da muradun ƙasarmu, tare da duba damuwar da ke cikin gida da waje dangane da halin da ake ciki. Amma zan sake jaddadawa, Najeriya ƙasa ce mai ba da ’yancin yin addinai,” in ji ministan.
Ya kuma ce gwamnati na mayar da martani kan waɗannan batutuwa ta hanyar kiyaye mutunci da darajar ƙasar, da kuma haɗin gwiwa da kowa, ciki har da ƙasashen duniya, don magance wannan matsala.
“Muna da iyakoki masu sauƙin shigowa, shi ya sa muke da fahimtar juna da makotanmu. Haka kuma muna da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kuma Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa. Mun fara magana da gwamnatin Amurka. Hanyoyin sadarwar mu a bude suke. Muna so a warware wannan matsala ta hanyar diflomasiyya.
“Baya ga siyasar lamarin, muna ɗaukar batun da muhimmanci. Amma ina so in ƙara jaddada cewa gwamnati, tun kafin abubuwan da suka faru a kwanakin baya, ta jajirce matuƙa wajen tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce amintacciya ga kowa.
“Shin akwai matsalolin tsaro a ƙasa? Eh, akwai. Shin ana kashe mutane a wasu sassan ƙasa? Eh. Amma shin gwamnati na yin wani abu don dakile hakan? Eh, tabbas akwai. Shin gwamnati na mayar da martani? Eh, tana yi. Amma ana yin hakan cikin cikakken hanyoyin da suka dace, tare da kiyaye daidaito da ake buƙata don fuskantar waɗannan matsaloli kai tsaye,” in ji shi.