Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar UNICEF da gwamnatin Jihar Gombe, sun shirya taron wayar da kai da ’yan jarida domin yaƙi da cututtukan da ba a cika kula da su ba.

Ofishin UNICEF na Bauchi ya haɗa kai da ’yan jarida da JPHCDA da wakiliyar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Hauwa Abubakar, domin tattaunawa kan yadda za a rage yaɗuwar cututtukan a jihar.

Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji

A taron, ’yan jarida sun samu damar jin bayanai daga masana da kuma yadda aikace-aikacen yaƙi da cututtukan ke tasiri a cikin al’umma.

Gwamnatin Jihar Gombe tana ware Naira miliyan 25 duk shekara domin yaƙi da NTDs, amma har yanzu akwai wuraren da ake buƙatar ƙarin tallafi.

Ƙungiyar Amen Health Care and Empowerment Foundation, ta ce tun 2015 ake samun ci gaba wajen yaƙi da cututtuka kamar onchocerciasis, lymphatic filariasis, da schistosomiasis.

Ƙungiyar ta kuma ce an yi wa waɗanda ke fama cututtukan tiyata kyauta.

Wakilin UNICEF, Hillary Adie, ya ce matsanancin talauci da rashin tsafta na taimaka wa yaɗuwar cututtukan.

Ya jaddada muhimmancin tsaftar muhallin zama.

Hauwa Abubakar, ta yi kira da a ƙara haɗa kai tsakanin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Ita kuwa Shugabar UNICEF ta Bauchi, Dokta Nuzhat Rafique, ta yaba wa Gombe kan ci gaban da ta samu, tare da roƙon ’yan jarida su ci gaba da wayar da kan jama’a game da cututtukan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Jarida Gwamnatin tarayya

এছাড়াও পড়ুন:

Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya musanta zargin cewa yana da wani saɓani da rundunar sojin Najeriya, yana mai cewa batun rikicin fili ne ya haɗa jami’ansa da wasu sojoji sa-in-sa da a yanzu ake faman cece-kuce a kai.

Wike ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, inda ya nanata cikakkiyar girmamawar da ya ce yana yi wa sojoji, kuma babu wata gaba a tsakaninsu.

Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe ya rasu Nijeriya ta doke Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya

Ya ce abin da ya faru dai rikici ne da ya shafi wani mutum ɗaya mai fili da ake rigima a kai saboda mallakarsa ba bisa ka’ida ba, saboda ba rikici ba ne tsakaninsa da rundunar sojin gaba ɗaya ba.

Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa wai yana amfani da batun filin ne don yaƙi da rundunar soji, yana mai cewa: “Ina girmama sojoji, kuma ba ni da wata matsala da su. Duk wanda yake ƙoƙarin kawo rikici tsakanina da su, kawai yana neman a rikita jama’a ne.”

A hirarsa da manema labaran, Ministan ya kuma koka kan yadda ake cin zarafin ma’aikata idan an tura su duba irin waɗannan filayen da ake zargin an mallaka ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na karya ƙa’idojin amfani da filaye ko kuma hana jami’an gwamnati gudanar da ayyukansu da ke kan ka’ida ba.

A cewar sa, babu yadda za a yi ya zauna ya yi shiru a matsayinsa na Minista alhali ana kai wa ma’aikatan gwamnati hari, “Ana dukan manyan jami’an gwamnati da suka kai matsayin darakta, ta ya za a yi su yi aikinsu bayan sun san ni ina can zaune a ofis ba zan iya kare su ba,” in ji shi.

Wike ya kuma bayar da misalin yadda wasu manyan sojoji da suka yi ritaya kamar tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo, suka samu matsalar fili, kuma su ka kira shi ya warware musu matsalar ba tare da sun tura sojoji su yi barazana ba.

Sai dai ya ce bai kamata wani ɗan ƙasa, da ya san ya yi ba daidai ba, saboda ya na da alaka da sojoji, ya hana gwamnati yin aikinta.

Rahoton ya zo ne a lokacin da ake ta tofa albarkacin baki kan takaddamar da ta barke tsakaninsa da wani matashin soja, lokacin da Wike ya je duba filin da ake zargin an mallake shi ba bisa ƙa’ida ba, inda sojan ya hana shi shiga wajen.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU
  • Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026
  • BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani
  • Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki
  • Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike
  • NIQS Ta Buƙaci Gwamnati Ta Tsawatar Kan Tsadar Gidajen Haya A Manyan Birane
  • An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe
  • Gwamna Nasarawa Ya Ce Za Su Samar da Masana’antu Don Ayyukan Yi
  • UNICEF da Abokan Hulɗa Sun Kaddamar da Shirin Wayar da Kai Kan Rijistar Haihuwa a Yankin Gwarzo