2025-11-02@23:33:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 249
«kujerar gwamna»:
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari. Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.” A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa. ...
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da kasashen duniya ke ba ta musamman kan batun hakkin dan’adam da hakkin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a kasar ba haka ba ne. Duk yan Najeriya suna da yancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.” Inji sanarwar. Shi dai shugaban Amurka Donald Trump Ya ce kiristanci na fuskantar...
3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
A cewar Salahudeen, Ranar Yaƙi da Cutar Polio ta Duniya muhimmiyar dama ce ta faɗakar da jama’a kan barazanar da cutar shan-inna ke haifarwa ga rayuwar al’umma da tattalin arziki, tare da sake duba nasarori da kalubalen da ake fuskanta. Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin bunkasa lafiya — musamman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) — ya taimaka matuƙa wajen cimma wannan gagarumar nasara. “Gwamna Dauda Lawal ya ayyana dokar ta-baci a bangaren lafiya, kuma hakan ya zame ginshiqin da ya taimaka wajen samun tallafi, goyon baya da isassun ma’aikata don tabbatar da an kai rigakafi ko’ina,” inji shi. Dekta Salahudeen ya kara da cewa WHO, UNICEF, Chigari, Sultan Foundation da Salina Foundation sun...
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da taron sauraron ra’ayoyi jama’a kan shirye-shiryen tsara kasafin kuɗin shekarar 2026 a wani yunƙuri na jaddada ƙudirinta na gudanar da mulki cikin gaskiya da haɗin kai. Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna jajircewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya wajen tabbatar da cewa ra’ayoyin jama’a na taka muhimmiyar rawa a tsara kasafin kuɗi da aiwatar da shi. Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ya ce tattaunawar ta bai wa gwamnati damar haɗa kai da sarakunan gargajiya, mata, matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayar da...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta ƙirƙiri ƙarin ƙananan hukumomi 29 a jihar. Wata takarda da Aminiya ta samu ta nuna cewa Mukaddashin Mataimakin Magatakarda na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Musa Yerima, ya tura wannan ƙuduri zuwa Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, yana neman amincewar Majalisar Tarayya domin tabbatar da dokar a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ake yi. Tinubu ya ƙirƙiri sabon harajin da zai iya ƙara N100 a kan kowacce litar man fetur Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati A halin yanzu, Jihar Bauchi na da ƙananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya amince da su. Da...
Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, ya amince da buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi guda shida. Wannan mataki na cikin abin da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu. Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum A cewar kwamitin, an tattauna kan buƙatu 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278. Daga cikin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi...
Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf. Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki October 22, 2025...
Kasar Iran Ta Kai Hare-Hare A Wuraren Da Kawayen Isra’ila Ba Su San Da Su ba A Lokacin Yakin Kwanaki 12
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wuraren da hatta kawayen haramtacciyar kasar Isra’ila ba su sani ba Tauraron dan Adam na Noor 3 ana daukarsa a matsayin dabara, soja, tauraron dan adam da Iran ta kera wanda ya samu gagarumin ci gaba na bayanai da leken asiri ga sojojin Iran. Masanin tsaro da dabarun yaki Laftanar Janar Abdul Karim Khalaf ya tabbatar da cewa: Tauraron dan adam Noor 3 na Iran yana wakiltar ingantaccen na’ura akan tauraron dan adam na Noor 2, wanda aka kara masa kilo 7 na karin kayan aiki. Tauraron dan Adam na Noor 2 yana da nauyin kilogiram 25, yayin da tauraron Noor 3 ke daukar nauyin kilogiram 32. Abin lura shi...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025. Hukumar wacce ta ce kudin kama kujerar kar su gaza Naira Miliyan Biyu, ta ce Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, na kokarin sama wa Maniyyata rangwame bisa kudin kujera da ta sanar a baya. Ta kara da cewa duk wanda bai biya ba kafin karshen wa’adin da ta bayar, ba zai sami kujerar Aikin Hajjin Bana ba. Har ila yau Hukumar ta ce Maniyyata za su...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da yin Allah wadai da ci gaba da rufe mashigar Rafah a matsayin wani mataki na karan tsaye ga sulhun. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi Allah wadai da matakin da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na jinkirta bude mashigar Rafah tare da bayyana hakan a matsayin karya sharuddan tsagaita bude wuta da kuma kaucewa alkawurran da aka dauka ga masu shiga tsakani da masu bada garantin. Kungiyar ta yi gargadin cewa rufewar yana kuma kawo cikas ga zuwan tawagogi na musamman domin zakulo gawarwakin da ke karkashin baraguzan gine gine da kuma gano wadanda suka mutu,...
Hukumar samar da abinci ta MDD ta bukaci a bude duk wasu hanyoyi domin shigar da abinci a Zirin Gaza, saboda yadda magance matsalar yunwa a Zirin zai dauki lokaci. Kakakin WFP Abeer Etefa ta shaidawa manema labarai a Geneva cewa, za a dauki lokaci kafin a rage yunwa. “Yanayi a Gaza yana da matukar wahala kuma har yanzu muna da nisa daga cimma wannan burin,” in ji ta. A cewar WFP, bukatar gaggawa ta ta’allaka ne ga “bude mashigar kan iyaka guda biyar” zuwa cikin yankin “domin a wadata Gaza da abinci da kuma samar da wuraren rarrabawa cikin gaggawa,”. Shirin WFP, “shi ne kara yawan taimakon da za a kai ga mutane miliyan 1.6 a cikin Gaza cikin...
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi watsi da daukaka karar da Isra’ila ta shigar kan sammacin da ta fitar a baya na kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant. . A watan Nuwamba ne, kotun ta fitar da sammacin bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza. Sammacin ya fusata Isra’ila da Amurka, wadanda tun daga lokacin suka kakabawa manyan jami’an ICC din takunkumi. Benjamin Netanyahu ya kira matakin a matsayin “mai nuna kyama ga Yahudawa.”.” A cikin watan Mayu, Isra’ila ta bukaci kotun ta ICC da ta yi watsi da sammacin. Kotun dai ta yi watsi da bukatar ne a ranar 16 ga watan Yuli. Mako guda bayan...
159-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a mu a cikin shirimmu na yau. ////…Madalla. Masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun kawo maku wasikar da Imam Al-Hassan(a) ya rubutawa Mu’awiya dan Abu Sufyan wanda...
158-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a mu a cikin shirimmu na yau. ////…Madalla. Masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun yi bayanin yadda Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan(a) wasika inda a ciki...
157-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a mu a cikin shirimmu na yau. ////…Madalla. Masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun yi bayanin yadda Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan(a) wasika inda a ciki...
156-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa...
155-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa...
154-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar Khudubar Imam Hassan Al-mujtaba (a) ya gabatar da khudubarsa ta farko bayan shahadar...
153-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, addinin musulunci ya himmatu da shugabanci, saboda haka ne ya ciki addini...
152-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, aka kawo likitoci don jinyar Amirulmuminina(a). Inda shugaban likitocin Atthi dan Amru...
151-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda Imam Ali (a) ya daga murya yana cewa {Na rantse da Ubangijin...
150-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda Abdurrahman dan Muljamul Muradi la’anenne ya sare Amirul muminina (a) a kansa...
An gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta wasan kwallon kafa na Asiya da Futsal na shekarar 2025 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. A bangaren mata kuwa, Marzieh Jafari, shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran, ita ce babbar mai horar da mata, yayin da Salar Aghapour ta lashe kyautar ‘yar wasa mafi nuna kwazo a wasan Futsal a wannan shekara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau...
Kwamandan Dakarun Sa Kai Na Iran Ya Bayyana Cewa: Iran A Yayin Yaki Da Isra’ila Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza a yunkurin da suka yi. Ya jaddada cewa: Iran ta lalata muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya da makamanta masu linzami a yakin karshe. Birgediya Janar Gholamreza Soleimani ya bayyana a wurin taron tunawa da shahidai a Isfahan cewa: Makiya sun yi tunanin cewa za su iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran nan da kwanaki 10, kuma sun yi niyyar haifar da hargitsi da...
Hukumar Kula Da GIdajen Gyaran Hali A Zamfara Ta Neman Shigarda Fursunoni Tsarin Inshorar Lafiya Na NHIS
Kwanturola na hukumar gyaran Hali a Najeriya reshen jihar Zamfara, Murtala Muhammad Haruna, ya yi kira da a shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIS) domin tabbatar da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya. Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga kwamishiniyar lafiya ta jihar Zamfara, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, a ofishinta da ke Gusau. Haruna ya ce shirin ya yi dai-dai da hangen nesan babban kwamandan hukumar gyaran hali ta Najeriya da nufin inganta jin dadin fursunonin da ke gidajen yari. Kwantirolan ya kuma jaddada bukatar inganta asibitin hukumar da ke cibiyar tsaro ta matsakaita, Gusau, da samar da isassun kayan aikin likita da magunguna masu mahimmanci...
Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane. Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu ya mayar da hankali ne kan inganta harkar sharar gida, da inganta tsarin tattara shara, da kuma kawata wuraren jama’a a fadin birnin na Kwankwasiyya. A cewarsa, aikin na da nufin tabbatar da tsaftar tituna, wuraren shakatawa, da wuraren jama’a tare da inganta alkinta muhalli. Engr. Kwa ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin karfafawa mazauna garuruwan Kwankwasiyya da Bandirawo da...
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka. Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama. “Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani. “Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba waɗanda ke kashe mutane ba gaira ba dalili. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a yau a wajen bikin yaye sabbin jami’an tsaron cikin gida (Community Watch Corps – CWC) guda 100, a karo na uku da aka gudanar a Katsina. Gwamna Buni ya ware N5.8bn don biyan haƙƙin tsoffin ma’aikata a Yobe Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan Radda, ya karyata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yada cewa gwamnatinsa tana tattaunawa da ’yan bindigar da ke ɓoye a dazuka. A cewarsa: “Babu wata tattaunawa ko sasanci da gwamnati ke yi da ’yan ta’adda....
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki. Majalisa ta gayyaci CBN da bankunan kasuwanci kan yawan cire wa kwastomomi kuɗaɗe DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique October 14, 2025
Majalisar Wakilai ta gayyaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da bankunan kasuwanci domin amsa tambayoyi kan yadda suke cirar cajin kudade barkatai daga asusun masu ajiya. Majalisar ta gayyace su ne bayan kudurin da Honorabul Tolani Shagaya ya gabatar kan abin da ta kira ‘cirar cajin kudade barkatai babu bayani ba,’ da bankuna suke yi daga asusun masu ajiya, sabanin dokokin CBN. Honorabul Shagaya ya ce kodayake bankuna da gudanar da hidima ne da ake biya, amma yawancin ’yan Najeriya suna kuka kan yadda suke yawan ciyar kudade — kamar na tura sakon tses, kula da katin ajiya, kula da asusun ajiya, tura kudi, hrajin kan sarki da wasu da ba su san da ake fiye da sau daya. Ya ce...
An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya. Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse. Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben. Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka...
Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa. Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama. A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin. Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi. Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin...
Wadanda suka amfana da horon, an ba su horon ne a fannoni daban-daban da suka hada da yin noma da takin gargajiya da kuma yin noman kayan lambu da sauransu. Kajin gidan gona da tare da kuma tallafa masu da kayan aikin noma. Bisa tsarin wannan haron, kowace mace daya da ta amfana da horon, an ba su tallafin Naira Naira 50,000. Kazalika, Adeleke ya danganta wannan tallafin kudin a matsayin mayar da hankalin gwamnatinsa na taimaka wa matan jihar. Gwamnan ya kuma jaddada muhimmcin tallafa wa mata, wanda ya sanar da cewa; hakan na da muhimanci domin inganta gobensu. Shi kuma shugaban gidauniyar, Dakta Deji Adeleke a nasa jawabin ya bayyana cewa, shirin wanda...
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
A cewarsa, gyaran yana taimakawa wajen samun bayanai daidai domin tsara ci gaba da kuma rarraba albarkatun ƙasa bisa adalci daga gwamnatin tarayya.“Wannan tsarin yana daidai da yadda ake yi a wasu jihohi, inda ake amfani da bayanan masarautu, yankuna da ƙauyuka wajen tsara ci gaba da rarraba kuɗaɗe,” in ji shi.Gwamnan ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɗa kan jama’a da tallafa wa ayyukan ci gaba, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sabon tsarin cikin gaskiya.Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu da yadda suka gudanar da aikin cikin gaskiya da tsari.Tun da farko, shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya bayyana cewa sun karɓi buƙatu 196, wanda 17 don kafa sabbin masarautu, 166 don sabbin yankuna, da...
A wani bangare na kudirinta na bunkasa tattalin arzikin mata, gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na shirya tarurrukan horaswa kan kula da tsaftar madara, da shirya kayayyaki, da dabarun kiyayewa ga mata masu sayar da madara ko nono a fadin jihar. Kwamishiniyar harkokin mata da yara da masu bukatu ta musamman Ambasada Amina Abdullahi Sani ta bayyana hakan a wata ziyarar aiki da ta kai kasuwar masu sayar da madarar mata (Nono Sellers) dake kan titin Zaria a Kano. A cewar kwamishinan, ziyarar na da nufin tantance yanayin da kasuwar ke ciki da kuma lalubo hanyoyin da za a bi don inganta yanayin aiki da kuma sa’o’in na mata masu sana’ar sayar da kayayyaki a can. ...
Kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin nazarin buƙatun ƙirƙirar sababbin masarautu da yankunan hakimai da dagattai, ya ba da shawarar ƙirƙirar masarautu 13, da hakimai 2 da dagattai 113 a fadin jihar. Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton da shugaban kwamitin, Hamza Koshe Akuyam, ya miƙa wa Gwamna Bala Mohammed a ofishinsa da ke Bauchi. Da yake miƙa rahoton, Akuyam ya bayyana cewa masarautu 13 da yankunan hakimai biyu da aka bayar da shawarar kafa su su ne suka cancanta daga cikin sama da buƙatu 100 da aka karɓa daga sassan jihar daban-daban. Kwamitin, an kaddamar da shi ne a ranar 4 ga Yuli 2025, da umarnin ya duba buƙatun al’ummomi, ya tantance dalilan tarihi, al’ada da...
Sojojin HKI sun bada sanarwan cewa zasu fara shirin aiwatar da shirin shugaban Trump na tsagaita buduewa juna wuta a Gaza. Da kuma batun musayar fursinoni gaba daya da kungiyar Hamas. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudia ya bayyana cewa a jiya da yamma ne kungiyar Hamas ta bayyana cewa ta amince da tsagaita wuta tsakaninta da HKI wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar. Kungiyar ta bayyana cewa ta amince da wasu sassa na yarjeniyar amma sai an tattauna kan wasu. Wata majiyar sojojin yahudawan ta bayyana cewa shuwagabannin kasar sun basu umrnin dakatar da kai hare- hare kan falasdinawa a Gaza. Wannan sanarwan ta zo sa’o’ii kadan bayan da shugaban Amurka ya umurci...
Burgediya JanarEsma’il Qa’ani babban kwamnadan dakarun “Qudus'” IRGC a nan Iran ya bayyana cewa kungiyar Hamas ta boye ranar fara yakin tufanul Aksa har shugaban kungiyar Shahid Isma’il Haniyya da shahida Nasarallah duk basu san da lokaci fara yakin ba, sai suka ji an fara. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Qa’ani yana fadar haka, a jiya jumm’a a hirar da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida a nan Iran. Ya kumakara da cewa a lokacinda aka fara yakin shugaban kungiyar ta Hamas yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Iraki, yana dawowa ne ya ji labarin fara shi. Janar Qa’ani ya kara da cewa, amma duk da haka, shahida Nasarallah ya zauna...
Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi. Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko na cibiyar cilla taurarin yan’adam na Chabahar kuma hukumar ta fara shirin amfani da sandarerren makamashi don cillan taurarin yan’adam da suke gabanta, wadanda a shirye suke a cillasu. Salarieh y ace a halin yanzu akwai tauraron dan Adam mai suna Pars-2 da ke jiran cillawa, sannan hukumar zata ci gaba da aiki a bangare na 2 na cibiyar don kammala aikin cibiyar cilla tararin...
Shugaban cibiyar fasaha da kere-kere ta Pardis a nan Tehran ya bada sanarwan cewa, wakilai daga kasashe 65 ne suka bayyana anniyarsu ta halattan gasar fasahar kere-kere ta shekara ta 2025 a cibiyarsa. Kamfanin dilancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Mehdi Saffaari –Nio yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa gasar ta dai-dai kun mutane, wadanda zasu gwada korewarsu da kuma fasahar da suke da ita a gasar wacce za’a gudanar daga ranar 27-30 ga watan Octoba damukeciki a nan Tehran. A taron yan jaridun da ya kira don bada wannan sanarwan Mehdi Safaari-nio ya ce mafi yawan mahallata gasar matasa ne musamman daliban makarantu wadanda suke son gwada korewarsu da kumailminsu. Kuma a...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda ya ke kawo maku kissoshin da suka zo cikin Alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan, wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahida muttahari, kuma kuma cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirarar ImamAl-Hassan Al-Mujtaba (a) jikan manzon All..(s) kuma dan Fatimah (a) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun yimaganar yakin Nahrawan, inda Imam Amirulmumina(a) ya yaki khawarijawa, wadanda su...
144-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko , mon tsaya inda muka bayyana yadda Talha da Zubair suka bukaci Amirulmuminina (a) ya yi masu izini...
143-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Mutahhari ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalalluddin Rumi ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. /////… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Alhassan Almujtaba dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku. A cikin shirimmu da ya gabata mun yi Magana dangane da yadda aka gudanar da hukunci tsakanin Abdullahi dan...
142-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Shahid Aya. Muttahari, ko kuma littafin Mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. /////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata , a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) jikan manzon All..(s) kuma dan Fatima (s) da muke kawo maku a cikin shirin da ya gabata, munyi maganar yadda Khawarijiwa suka ki...
141- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Shahid Aya. Muttahari, ko kuma littafin Mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. /////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata , a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) jikan manzon All..(s) kuma dan Fatima (s) da muke kawo maku a cikin shirin da ya gabata, munyi maganar yadda Aka ayyana...
Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sanar da korar daukacin mambobin gwamnatinsa biyo bayan mummunar zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a kasar. A wani jawabi da ya yi na tsawon mintuna 17, ranar Litini, , Andry Rajoelina ya sanar da cewa ya ji kiran matasa tare da korar firaministansa da gwamnatinsa. Ya fara jawabinsane da jajanta wa wadanda suka rasa yan uwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Da yake jawabi ga matasan da suka fusata, ya bayyana cewa: “Na saurari muryoyinku, da bukatunku, Kuma ina ba da hakuri idan akwai mambobin gwamnati da ba su yi aikin da mutane suke tsammani […].” Shugaban ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “A bisa...
149-Assakamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin Al-Kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen romi, ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun ji yadda al-amura suke kara dagulewa a cikin...
148-Assakamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sakesaduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo makukissoshi wadanda suka zo cikin Al-Kur’ani mai girma ko cikin wasu littafanwadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari,ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen romi, ko kuma cikin wasulittafan, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata,a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtaba (a) dan Fatimah (s) diyar manzonAll..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun yadda Mu’awiyadan Abusfyan ya kwace kasashen musulmi karkashin ikon Amirul muminina (a)wadanda suka hada da Madina,...
Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kan Malam Shu’aibu Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph, ga Kwamitin Shura na Jihar don ɗaukar matakin da ya dace. Sakataren Gwamnatin Jihar ne, ya tura ƙorafe-ƙorafen a ranar Juma’a, inda kwamitin ya fara zama domin sauraronsu. ’Yan Najeriya da tauraronsu ya haska a Ballon d’Or Yadda ’yan haya za su samu ragin N500,000 a shekara A cewar kwamitin, za a gayyaci masu ƙorafi da Malam Triump domin su gabatar da hujjoji. Masu ƙorafi za su fayyace abubuwan da suke tuhumar malamin, yayin da shi kuma za a ba shi damar kare kansa. Bayan haka kwamitin zai tattauna bisa ƙa’idojin shari’ar Musulunci. Sakataren kwamitin, Shehu Wada Sagagi, ya shaida...
A ranar Litinin aka gudanar da bikin bayar da kyautar Ballon d’Or a Birnin Paris, inda ake karrama fitattun ’yan ƙwallon duniya. A bana, Ousmane Dembele na Ƙasar Faransa da PSG ne, ya lashe kyautar maza, yayin da Aitana Bonmati ta Spaniya ta lashe ta mata karo na uku a jere. An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Abin farin ciki ga Najeriya shi ne, mai tsaron ragar Super Falcons, Chiamaka Nnadozie, ta zo ta huɗu a jerin mata, wanda shi ne matsayi mafi girma da wata ’yar Najeriya ta taɓa samu. Ga jerin ’yan Najeriya da suka taɓa shiga cikin jerin waɗanda suka fafata neman kyautar Ballon d’Or:...
Magajin garin Landan ya caccaki shugaban Amurka Trump, yana mai cewa shi mai nuna wariyar al’umma ce tare da kyamar musulmi Magajin garin Landan Sadiq Khan ya bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin “mai nuna wariyar al’umma kuma mai kyamar musulmi,” bayan da Trump ya zarge shi da neman aiwatar da shari’ar Musulunci a babban birnin Birtaniya. Khan ya shaida wa tashar Sky News cewa: “Yana ganin Trump a matsayin mai nuna wariyar al’umma, mai dabi’ar bunsuro, mai son zuciya, kuma mai kyamar musulmi.” Ya yi nuni da cewa, Landan ce ta farko a cikin alamomi da dama, kamar zuba hannun jari na kasashen waje, ya kuma jaddada cewa “yana matukar alfahari da cewa Landan ce birni mafi girma...
Ya ce zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai tabbata ne kawai idan aka tabbatar da adalci. Shugaban ya jaddada irin gyare-gyaren tattalin arziƙin Nijeriya, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya dokokin musayar kuɗi. Ya ce matakan suna da tsauri, amma dole ne a ɗauke su domin samar da ci gaba mai ɗorewa. A kan tsaro, Tinubu ya ce yaƙin da ta’addanci ba wai da bindiga kaɗai ake cin nasara ba, sai da ra’ayoyi da ɗabi’u waɗanda ke haɗa al’umma. Ya kuma jaddada aniyar Nijeriya ga zaman lafiya, ci gaba, da kare haƙƙin ɗan Adam, inda ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta yi canje-canjen da za a iya gani, tare da gargaɗin cewa idan...
Za a fara samar da sabon maganin riga-kafin kare mutum daga kamuwa da cutar HIV, a ƙasashe masu ƙaramin karfi, a kan farashi mai rahusa daga shekarar 2027. Maganin allura mai suna lenacapavi wanda a ƙasashen da suka ci gaba ake sayarwa da dubban daloli a duk shekara, zai koma dala 40 kacal a kowace shekara. Wannan sabuwar hanyar riga-kafin za ta bai wa miliyoyin mutane damar ci gaba da rayuwa da kuma kauce wa haɗarin kamuwa da cutar HIV. Za a riƙa samar da maganin mai rahusa a Indiya, sannan kuma za a watsa shi a duniya ta hannun gamayyar wasu ƙungiyoyin kiwon lafiya a ƙasashe guda 120.
A ƙarshe, Shugaban ya ce matakan da gwamnati ta ɗauka kamar cire tallafin mai da sauya tsarin kuɗi, duk duk sanya shan wahala amma wajibi ne domin tabbatar da cigaba. Ya jaddada cewa Nijeriya za ta ci gaba da kare haƙƙin ɗan Adam, da haɗin kai da zaman lafiya, inda ya gargaɗi duniya da cewa babu wanda zai tsira sai idan duk mun tsira tare. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Akalla yara miliyan 4.8 ne ake shirin yi wa allurar rigakafin cutar kyanda da cutar shan inna a jihar Katsina a wani bangare na shirin allurar riga-kafi da aka shirya yi a wata mai zuwa. Shugabar ofishin kula da kananan yara ta UNICEF, Rahama Farah, ce ta sanar da hakan a wani taron tattaunawa da wayar da kan masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Katsina a wani bangare na shirye-shiryen rigakafin da ke tafe. Ya bayyana cewa za a yi allurar rigakafin cutar kyanda ga yara ‘yan tsakanin watanni 9 zuwa 14 yayin da za a yi allurar rigakafin cutar shan inna ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Mista Farah...
A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin. Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba. An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala. NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala. A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa. Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Hatsarin ya rutsa da mota ƙirar Toyota Hiace wadda ke ɗauke da fasinjoji daga Jakusko zuwa kasuwar Jajimaji da kuma mota ƙirar Volvo daga garin Azare. Rahoto ya nuna cewa mota ƙirar bas ce ta ƙwace ta buga wani Keke Napep...
Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda. Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya...
Ƙasar Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a dakatar da yaki a Gaza nan take kuma ba tare da sharaɗi ba. Daftarin kudurin na majalisar ya kuma buƙaci Isra’ila ta cire duk wani takunkumi kan kai agaji ga yankin na Falasɗinawa. Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Kudurin, wanda ƙasashe 10 da aka zaɓa daga cikin mambobi 15 na majalisar suka tsara, ya kuma buƙaci a saki dukkan fursunonin aka yi garkuwa da su daga hannun Hamas da sauran kungiyoyi ba tare da sharadi ba, cikin mutunci da girmamawa. Kudurin dai ya samu goyon bayan ƙasashe 14, sai dai...
Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo. Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Idan za a iya tunawa, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa, ba ta fitar da wata ƙwaƙwarar sanarwa, kan maƙasudin soke takardar ɗaukar aikin da aka yiwa Umunubo ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya, tare da rufe tashar rediyo ta kashin kai a Jihar Neja, kafin ya ƙaru zuwa ga kai hare-haren da aka ɗauki nauyi kan taronmu na Kaduna, sannan kuma da hare-hare a kan ayarin motocin shugabannin ADC a Kebbi. “Haka kuma an kai hari a wurin taron ADC a Alimosho a Jihar Lagos, wannan yana nuna cewa APC ta ji kunya kuma ba ta girma ko...
Dakarun runduna ta 3 da rundunar haɗin gwiwa – Operation Enduring Peace (JTF OPEP) masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun kama wasu da ake zargin ɓarayin shanu ne a ƙauyen Kogul da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. A cewar rundunar, kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan ƙoƙarin da sojojin suka yi ne don daƙile barazanar satar shanu, “wanda ke haifar da rikici a yankin da Rundunar haɗin gwiwa ta ke.” 2027: Malamai sun gudanar da addu’o’in nasarar Tinubu-Barau a Kano An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus Da yake yi a wa manema labarai bayan ikan nasarar da rundunar ta samu a Jos, a ranar Alhamis, kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya ce a...
An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa
Rahotanni daga ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin, na cewa an kara wasu wurare hudu dake kasar Sin, cikin jerin muhimman wuraren ban ruwa na kasa da kasa ko WHIS. Wuraren sun hada da yankin ban ruwa na tafkin Chishan, da gonaki kan tuddai na kabilar Hani na Yuanyang, da madatsar ruwa ta Jianjiangyan, da tsohon mashigin ruwa na Mentougou dake kan kogin Yongding. An ce, za a shigar da wuraren cikin sabon jerin ne a hukumance yayin taro na 76, na kwamitin zartarwar hukumar kasa da kasa mai lura da wuraren ban ruwa da magudanansu ko ICID, taron dake gudana a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Da wannan kari, adadin wuraren dake kasar Sin da aka...
A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa. Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka. Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.” Ya yi gargadin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin wadannan maganganu...
Kamfanin Aero Engine Corporation na kasar Sin, ya fitar da sabon injin aiki a manyan na’urori mai aiki da iskar gas mai karfin gaske, wanda ke iya samar da karfin megawatt 110. Kamfanin ya fayyace sashen kirar injin mai suna Taihang 110, a yankin kira na kamfanin a Litinin din nan, kuma ana fatan fara shigar da injin kasuwa. Fitar da injin zuwa kasuwanni na nufin kasar Sin ta cimma nasarar gabatar da inji kirar gida mai matukar karfi, wanda manyan na’urori za su rika amfani da shi ta hanyar sarrafa iskar gas. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan da ya yi murabus, inda tsohon Ministan Harkokin Waje ya bayyana takarar neman kujerar mai tasiri a kasar wadda take sahun gaba na kasashe masu arziki a duniya. Tsohon Ministan Harkokin Wajen kasar Japan, Toshimitsu Motegi ya zama mutum na farko da ya nemi ’yan majalisar dokoki na jam’iyya mai mulki ta Liberal Democratic Party (LDP) su ba shi damar zama sabon Firaminista, domin ya maye gurbi Firamnista Shigeru Ishiba mai barin gado wanda ya bayyana yin murabus daga kan mukamin. Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda da yaransa 5 a Kogi Yiwuwar yajin aikin direbobin tankar mai kan rikicin Matatar Dangote Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Lahadi ce Firaministan Japan,...
Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar. Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a — MURIC Oginni ya yi Allah wadai da korar ɗan majalisar, yana mai cewa babu wata hujja kuma ba su ba da izini ko wani iko na ɗaukar wannan hukunci ba. Sunday ya ce tuni an sallami shugaban jam’iyyar na Kano, Hashim Dungurawa tare da rukunin tsagin Kwankwasiyya daga jam’iyyarsu ta NNPP. A bayan nan ne...
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar wa auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
136- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin Siffin yakin da ya sauya tarihin musulunci, yakin...
Sin Ta Sanar Da Rukuni Na Hudu Na Abubuwa Da Wuraren Tunawa Da Yakin Kin Jinin Mamayar Dakarun Japan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa: Ina kiran mutanen Jamus kan cewa ku ne kuka samar da ikidar Nazi, a yayinda mu a kasar Italia da Spaine muka samar da akidar Fasim a nahiyar turai a baya, wana ya kai kasashen turai ga lalacewa.. Jami’ar ta bayyana haka ne bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro na Jamus suka yi kan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa wadanda kuma suke bukatar HKI ta...
Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni. A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi. Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa. Ta sha alwashin cewa...
Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.” Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan. Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya yi hastari a hanyar Kaduna-Abuja Ya ce an haramta gudanar da al’adun gargajiya irin su Shadi, Sharo, Garaya da kuma shagulgulan wannan zamani kamar Kauyawa Day, Gala, DJ, Aloba da sauransu a bukukuwan aure. Isah ya ce an ɗauki waɗannan matakan ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan yadda abubuwa na rashin tarbiyya da tayar da...
A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya. An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta. An ɓullo da ranar ce domin haɗa kan masu magana da harshen Hausa a faɗin duniya da nufin magance matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Da farko dai, an fara bikin wannan rana ce kamar wasa a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta amfani da kalmar #RanarHausa. Zuwa shekara ta 2018 kuma aka fara yin bikin a zahiri tare da gudanar da tarurruka...
Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
“Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun. “Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da...
Ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga kasa da kasa su ci gaba da tallafa wa ayyukan UNRWA, yana mai cewa a shirye Sin take ta yi abun da zai kawo karshen rikicin da samar da mafita mai adalci da dorewa bisa manufar kafa kasashe biyu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna cewa, kaso 92 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na bayyana matukar damuwa game da tsaron rayukan al’ummun Amurka, yayin da kaso 81.7 bisa dari suka ce muggan laifuka, da karuwar masu kwana a kan tituna sun zamewa manyan biranen Amurka alakakai, lamarin da ya zamo cutar Amurka mai matukar wahalar magani. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar da hankulan Larabawa kuma suka yi watsi da shi. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce “tana tabbatar da aniyarta ta abbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tare da yin Allah wadai da abin da wasu kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito dangane da abin da ake kira Isra’ila Babba. Ya yi bayanin cewa, “ya bukaci a yi karin haske kan hakan, bisa...
Ministan harkokin wajen Yemen Jamal Amer a ranar Laraba ya karbi wata wasika daga Dr. Khalil al-Hayya shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda wakilin kungiyar a Sanaa, Moaz Abu Shamala ya mika. A cikin wasiƙar nasa, al-Hayya ya bayyana matuƙar godiyar Hamas ga sadaukarwa da tsayin dakan al’ummar Yemen, yana mai bayyana su a matsayin “‘yan’uwa na gaskiya, Ansar Allah,” a tinkarar mamayar Isra’ila da kawayenta duk da gagarumar sadaukarwa, barazana, da hare-hare. Ya tabbatar da cewa nisan da kasar Yamen ke da shi da Falasdinu ya kara dankon kusancinta da al’ummar Palastinu ne kawai da kuma kudurinta na ci gaba da ba da taimako da taimako da kuma kare Gaza da Palastinu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe...
Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa sabon Sarkin Alkaleri a Bauchi Wannan mataki, a cewar Ministan Ilimi Dakta Olatunji Alausa, an ɗauke shi ne domin rage yawan makarantun da ba a amfani da su yadda ya kamata, lamarin da zai ba da damar mayar da hankali wajen gyara da inganta waɗanda ake da su yanzu. Da yake zantawa da manema labarai bayan taron na FEC a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba,...
130-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafai wadanda suka hada da littafin Dastane Rastantan na Aya. Shaheed Murtadan Muttahary ko kuma cikin littafin mathnawi na Maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro za su kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmun da ya gabata mun bayyana yadda Amirulmuminina Aliyu...
129-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafai wadanda suka hada sa littafin Dastane Rastantan ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun bayyana yadda Imam Ali (a) ya kammala hujja a kan mutanen...
128-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafai wadanda suka hada sa littafin Dastane Rastantan ko kuma cikin littafin mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun bayyana yadda Imam Ali (a) ya kammala hujja a kan mutanen...
126-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko da muke kawo maku, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda....
125-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur;abi mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada muttahari ko littafin Mathnawa na maulana Jalaluddin rumi ko kuma cikin wasu littafai. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah masu sauraro, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabaya, a kuma cikin sirar Imam Hassan Akmujtaba (a) dan Fatima (s) diyar manzon All…(s). da muke kawo maku. A shirimmu na karshe mun kawo maku yadda amirulmuminina (A) ya yi zango a wani wuri da...
124-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko da muke kawo maku, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda....
Gwamnatin jihar Kano ta gana da shugabannin ‘yan bangar siyasa da suka tuba a jihar tare da yi musu alkawarin tallafa musu ta hanyar sauya tunaninsu da horar da su sana’o’i da kuma kayan aikin fara sana’ar. Taron wanda ya gudana a ranar Talata a Kano ya samu halartar tubabbun ‘yan barandan siyasa da masu satar waya kusan 718. Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Naira Biliyan 40.8 Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ya yi kira ga mahalarta taron da su rungumi tuba da gaskiya tare da bayar da hadin kai ga shirin gwamnati na...