Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
Published: 11th, November 2025 GMT
An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.
Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.
Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, bindiga kirar gida guda daya, harsasai 183, motoci uku, babura uku, babur mai kafa uku (Keke-napep) daya, da kuma dabbobi sama da 200 da aka sace.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda 29 a Borno
Rundunar sojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sake samun nasara bayan ta ceto mutane 86 da kuma kama wasu mutum 29 da ake zargi da samar wa ’yan ta’adda kayayyaki a Jihar Borno.
A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar a ranar Litinin, an gudanar da wannan samame ne a ranar 9 ga Nuwamba, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da cewa ’yan ta’adda suna garkuwa da fararen hula a kan hanyar Buratai–Kamuya.
Kotu ta sake dakatar da babban taron PDP John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihiSojojin Bataliyar Musamman ta 135 da ke ƙarƙashin Sashe na 2 na OPHK sun yi artabu da mayakan Boko Haram da ISWAP a Dutsen Kura, inda suka fatattake su bayan fafatawar da ta gudana har zuwa yankin Mangari.
Sanarwar ta bayyana cewa an gano mafakar ’yan ta’adda guda 11, sannan an kubutar da maza, mata da yara 86 da aka garkuwa da su.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai 73, jigidar harsashi 5, motoci 5, babura 5, kekuna 8 da kuma babura masu ƙafa uku guda 2.
A wani samame na daban a Mangada, dakarun sun kama mutum 29 da ake zargi da kai wa ’yan ta’adda kayayyaki, tare da kwace motocin ɗaukar kaya guda 2 da babura masu ƙafa uku cike da man fetur da man injin sama da lita 1,000.
Laftanar Kanar Uba ya ce an gudanar da duka ayyukan ba tare da asarar rai ko rauni a ɓangaren sojoji ba, inda babban kwamandan rundunar ya yabawa jarumtar dakarun tare da buƙatar su ci gaba da hana ’yan ta’adda samun damar shakatawa a duk faɗin yankin Arewa maso Gabas.