Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan
Published: 14th, November 2025 GMT
Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis.
WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin yankin, da safiyar ranar.
Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ce rubuce-rubucen da aka fesa da fenti sun haɗa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan zargin.
Babu rahoton rauni ko mutuwa a lamarin kawo yanzu, amma bidiyon da ke yawo a kafafen yada labaran Falasɗinu da Isra’ila sun nuna lalacewar masallacin.
Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana harin a matsayin “mai matuƙar daure kai.”
Herzog ya ce wannan laifin da “ƙalilan daga cikin masu laifi” suka aikata ya “saba ka’ida,” inda ya ƙara da cewa “dukkan hukumomin gwamnati dole su ɗauki mataki mai ƙarfi don kawar da wannan dabi’a.”
Babban hafsan sojin Isra’ila, Laftanar Janar Eyal Zamir, ya goyi bayan suka da Herzog ya yi, yana mai cewa rundunar soji “ba za ta lamunci ayyukan wasu ’yan ƙalilan masu laifi da ke bata sunan jama’ar da ke bin doka ba.”
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya (UN), Antonio Guterres, a ranar Alhamis, ya la’anci harin da Yahudawan masu haramtattun gidajen suka kai kan masallaci a yankin wanda Isra’ila ta mamaye.
Tashin hankali daga Yahudawa masu ra’ayin rikau kan Falasɗinawa a yankin ya ƙaru tun bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktoban 2023, wanda aka fara bayan hare-haren da Hamas ta jagoranta kan Isra’ila.
Tun daga lokacin, an samu ƙaruwar hare-haren da ke haddasa mutuwa tsakanin Falasɗinawa da sojojin Isra’ila a yankin na Yammacin Kogin na Jodan.
Rundunar sojin Isra’ila na yawan fuskantar zargi kan gazawarta wajen ɗaukar mataki mai ƙarfi kan tashin hankalin da Yahudawa ke haddasawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gabar Yammacin Kogin Jordan Isra ila Yahudawa
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: Matsalar Yammacin duniya ita ce ci gaban kimiyyar Iran ba makaman nukiliya ba
Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban.
Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban na rayuwar mutane, ciki har da maguguna, fannin kiwon lafiya, muhalli, noma, da masana’antu a cibiyoyin Makamashin Nukiliya ta Iran.
A lokacin ziyarar da ya kai wa Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Araghchi ya jaddada cewa fasahar nukiliya tana nan a dukkan fannoni tana ba da gudummawa ga ci gaban fannoni daban-daban. Ya kara da cewa wannan ilimi da fasaha suna hanzarta ci gaban kimiyya a Iran kuma suna ba da tallafi mai mahimmanci ga masana’antu da fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar kasar.
Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce matsayar kasashen Yammacin duniya game da shirin nukiliya na Iran: “Matsalarsu ba wai ta makaman nukiliya ba ce, matsalarsu ita ce ci gaban wannan kimiyya a Iran. Kasar, tare da masana kimiyya da kwararru, ta yi nasara a wani fanni na kimiyya mai sarkakiya wanda ke da fannoni daban-daban musamman a fannin lafiya.
saboda haka suna fakewa da batun makaman nukiliya a matsayin hujja ta kawo cikas ga wannan shiri, inji shi.
Araghchi ya jaddada cewa babban burinsu shine hana Iran cimma waɗannan manufofi da kuma kiyaye komai a ƙarƙashin ‘yanci da cin gashin kai na Iran. Ya lura cewa wannan fasaha tana da ci gaba sosai kuma tana wakiltar babban ci gaban kimiyya ga masana na kasa. Babu wanda zai iya yin watsi da waɗannan nasarori.
Ya ƙara da cewa, a ganinsa, ƙasashen Yamma ba za su sami wani zaɓi ba illa su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyya a fannin masana’antar nukiliya mai zaman lafiya.
Mohammad Eslami, shugaban Ƙungiyar Makamashin Nukiliya ta Iran, ya kuma jaddada cewa Amurkawa, ta hanyar cin zarafinsu, suna da nufin hana ci gaban Iran. Ya bayyana cewa, saboda haka, suna shirin magance wannan batu ta hanyar haɗin gwiwa da Ma’aikatar Harkokin Waje da kuma kawar da wannan barazanar daga Iran. Ya ƙara da cewa ba za su bari cikas a kan hanyar Iran ba ko kuma su bar wani ya haifar da cikas ga ƙasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sheikh Qassem: Kawar Da Hizbullah Ne Babban Burin Isra’ila A Lebanon November 12, 2025 Masar Da Sudan Sun Jaddada Wajabcin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yankin November 12, 2025 Venezuela: Maduro Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tsaron Kasa Mai Cikakkiyar Kariya November 12, 2025 UNICEF: Isra’ila ta hana allurar rigakafin yara masu mahimmanci shiga Gaza November 12, 2025 Ministocin harkokin wajen kasashen yamma sun yi Allah wadai da ta’asar RSF a El Fasher Darfur November 11, 2025 Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya November 11, 2025 Larijani : ‘babu wani sabon sako’ da muka aika wa Amurka November 11, 2025 Gaza : Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau 282 tun bayan aiwatar da ita November 11, 2025 Iraki : Ana zaben ‘yan majalisa don tsara makomar siyasar kasar November 11, 2025 Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar November 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci