HausaTv:
2025-11-10@06:57:19 GMT

Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla

Published: 10th, November 2025 GMT

Gwamnan yankin Darfur na Sudan, Bahreldin Adam Karamah, ya bayyana cewa shugabannin mayakan RSF sun aikata laifuka a El Fasher, yana mai jaddada cewa “ba za su iya ɓoye su ba.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga Kamfanin Dillancin Labarai na Sudan (SUNA), Karamah ya fayyace cewa shawarar da Majalisar Tsaro ta Sudan ta yanke, wacce shugabanninta suka goyi bayanta baki daya, ta tabbatar da cewa “babu wani sulhu da masu kisan gillar al’ummar Sudan.

” Ya kara da cewa, “Ba za mu yi sulhu a kan wannan kasa ba, kuma ba za mu bari a sauke tutarta ko a lullube ta a cikin laka tare da ta wulakanta ta ba.”

Gwamnan Darfur ya nuna cewa rikicin da ake yi a yanzu “yakin son rai ne da gwagwarmayar domin fayyace makoma” da mutanen da “suka rubuta alkawari na girmamawa da biyayya ga kasa da jininsu.” Ya tabbatar da cewa Sudan “ba za ta ci amanar shahidanta ba kuma za ta mika tutar kasar ga al’ummomi masu zuwa a cikin nasara.”

A wani yanayi makamancin haka, Shugaban Majalisar Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ziyarci matsugunan mutanen da suka rasa matsuguninsu daga El Fasher a birnin Al-Dabba na Jihar Arewa a ranar Asabar. Ya duba  yanayinsu da kuma irin taimakon da suke bukata.

A cewar Kamfanin dillancin labaran SUNA, al-Burhan ya jaddada ruhin hadin kan al’umma,  yana mai nuni da “jajircewar kasar wajen magance matsalolin mutanen da suka rasa matsuguninsu da kuma ba su damar rayuwa mai daraja.” Ya umurci dukkan hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su samar da muhimman abubuwan bukata  ga wadanda suka rasa matsugunin da kuma yin aiki kan kawar da duk wani abin da zai iya kawo cikas ga rayuwarsu ta yau da kullum.

A ranar 26 ga Oktoba, dakarun (RSF) suka sanar da kwace iko da El Fasher bayan fadace-fadace masu tsanani da sojojin Sudan. Duk da haka, al-Burhan ya tabbatar da cewa janyewar sojojin daga birnin don gujewa asarar rayukan fararen hula ne.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan November 9, 2025 Kasashen (AES) za su hanzarta kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro November 9, 2025 Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump November 9, 2025 Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin El-Fasher November 9, 2025 Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila November 9, 2025  An Kafa  Mutum-mutumin  Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran November 9, 2025  Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati November 9, 2025 Wasu Kasashe Takwas Sun Bukaci Ganin An kama Benjamine Netanyahu November 9, 2025 WFP: Ana Fama Da Matsananciyar Yunwa A Gabashin DRC November 9, 2025 Iran da Pakistan sun habaka cinikayyar kan iyaka don karfafa kasuwanci da tsaro November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Masar da Rasha sun tattauna batutuwan tsagaita wuta a Gaza da kuma  Sudan

Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun  tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan.

A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar a ranar Asabar, Abdelatty ya yi nazari kan ci gaba da kokarin da Masar ke yi na karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa.

Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya zuwa mataki na biyu na shirin tsagaita wuta, wanda zai  magance matsalolin siyasa da ayyukan  jin kai domin samun zaman laifiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin.

Jami’in diflomasiyyar Masar ya kuma tattauna shirye-shiryen taron kasa da kasa da nufin tallafawa sake gina Gaza. Ya jaddada bukatar samar da tallafin duniya don sake gina yankin da ya lalace, da kuma rage wahalhalun da yakin ya haifar.

Ministan harkokin wajen Masar ya ce aiwatar da shirin sake gina yankin Gaza zai dauki tsawon shekaru biyar bisa  tsarin da Kungiyar Kasashen Larabawa da Kungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC) suka amince da shi, wanda zai lakume kudi da zasu kai  dala biliyan 53.

A halin yanzu, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kudin da za a kashe wajen farfado da Gaza zai kai kimanin dala biliyan 70.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dan Wasan Taekwando Na Kasar Iran Abulfazl Zandi Ya Zamo Shi Ne Na Daya A Duniya November 8, 2025 Iraki Na Samu Zaman Lafiya Kuma Tana Kokarin Kawo Karshen Zaman Sojojin Ketare A Kasar November 8, 2025 Turkiya Ta Fitar Da Sammacin Kama Natanyaho Da Wasu Jami’ian Isra’ila Kan Yakin Gaza November 8, 2025 Shugaban Najeriya da takwaransa na kasar Saliyo Sun yi Ganawar Sirri a birnin Abuja   November 8, 2025 Nigeria: Za A Ci Gaba Da Zaman Shari’ar Shugaban Kungiyar “IPOB” A ranar 20 Ga Watan Nan Na Nuwamba November 8, 2025  Ukraine: Fiye Da ‘Yan Afirka 1000 Ne Suke Taya Rasha Yaki Da Kasar Ukiraniya November 8, 2025  Jirgin Kasan Dakon Kaya Na Farko Daga Rasha Ya Iso Kasar Iran A Yau Asabar November 8, 2025  Lebanon: Mutane 2 Sun Jikkata Sanadiyyar Harin “Isra’ila” A Garin Bint-Jubail November 8, 2025 Araqchi: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin November 8, 2025 Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta November 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa
  • Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin da aka aikata a El-Fasher
  • Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura
  • Masar da Rasha sun tattauna batutuwan tsagaita wuta a Gaza da kuma  Sudan
  • Iraki Na Samu Zaman Lafiya Kuma Tana Kokarin Kawo Karshen Zaman Sojojin Ketare A Kasar
  • Nigeria: Za A Ci Gaba Da Zaman Shari’ar Shugaban Kungiyar “IPOB” A ranar 20 Ga Watan Nan Na Nuwamba
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila
  • An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi