Kenya: An gano tarin zinari da darajarsa ta haura Dala biliyan 5 a yammacin kasar
Published: 13th, November 2025 GMT
Wani kamfanin hakar ma’adinai na Biritaniya ya sanar a jiya Laraba cewa, an gano tarin zinari a karkashin kasa a gundumar Kakamega da ke yammacin kasar Kenya, wanda darajarsa ta kai sama da dalar Amurka biliyan 5.28 kwatankwacin shilin kasar Kenya biliyan 683, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi ga fannin hakar ma’adinai na kasar.
Kamfanin ShantaGold Kenya Limited ya sanar da cewa, an gano hakan ne a hanyar Lerehanda, wanda ya ratsa cikin kananan hukumomin Kakamega da Fihiga, bayan kwashe tsawon shekaru ana bincike.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce aikin yana da nufin samun lasisin da ya dace don hakar albarkatun zinare a mahakar Isolo-Bushiangala don kasuwanci.
Ta kara da cewa hakan na iya bunkasa tattalin arzikin cikin gida ta hanyar samar da ayyukan yi, da kuma bayar da gagarumar gudunmuwa ga gwamnatin Kenya ta hanyar haraji da kuma kudaden shiga, wadanda ake ganin zai iya kara hakaba ci gaban tattalin arzikin gida da na yankin.
Ana sa ran gano sabbin ma’adanan zai mayar da kasar Kenya ta zama babbar kasuwa a masana’antar zinari a gabashin Afirka.
Sanarwar kamfanin ta kara da cewa binciken ya hada da ma’adinai masu inganci da suka dace kasuwanci, kuma ana ci gaba da nazarin yiwuwar ci gaba da ayyukan hakarsu a karkashin kasa.
Binciken ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bukatar zinariya a duniya, inda farashinsa ya yi tashin gwauron zabi a duniya saboda rashin tabbas na tattalin arziki.
Manazarta sun ce a nan gaba bangaren zinari na kasar Kenya zai iya taka muhimmiyar rawa wajen jawo hankulan masu zuba jari da ke neman sabbin wuraren kasuwannin ma’adanai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Hamas Ta Nemi Kawo Karshen Kisan Kiyashi Da Lamunce Shigar Da Taimako November 13, 2025 MDD ta yi gargadi game da hadarin yunwa a wasu sassa na duniya November 13, 2025 Amurka Na Shirye-Shiryen Aikewa Da Sojoji Guda 1000 A Iyakar Isra’ila Da Yankin Gaza November 12, 2025 Shugaban Iran Ya Aike Da Wasika Ta Musamman Zuwa Ga Yarima Mai Jiran Gado Na Saudiyya November 12, 2025 Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki November 12, 2025 Iran Da Pakistan Sun yi Kira Da Yin Aiki Tare Don Tunkarar Makiyansu November 12, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Rikicin Yankin November 12, 2025 Gabon: An Daure Mata Da ‘Dan Tsohon Shugaban Kasa Bongo Shekaru 20 A Gidan Yari November 12, 2025 Tanzania: MDD Ta Yi Kira Da A Yi Bincike Akan Daruruwan Mutanen Da Aka Kashe Sanadiyyar Rikcin Zabe November 12, 2025 Iran Ta Zama Memba A Kungiyar Tattara Bayanai Na Ilimomi Da Kere-kere Ta Duniya ( ISKO) November 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Kenya
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na Venuzuela
Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta kakaba sabbin takunkumi kan bangaren manfetur na kasar Venuzwela da kuma iyalan shugaban kasar Nicolas Maduro da hakan ya shafi tattalin arziki, siyasa da kuma kara matsin lamba kan gwamnatin carakas.
Tattalin arzikin venuzuwela ya doru ne kan man fetur don haka sabon takunkumin kai tsaye zai cutar da gwamnatin maduro ne da kudaden shigarta na asali suna fitowa ne daga man fetur, gwamnatin Amurka ta sanar da sanya sabbin takunkumi kan bangaren man fetur din kasar Venuzuwel da kuma wasu mutane Ukku yan uwan matar Moduro,
Jaridar new york times ta fitar da rahoton cewa takunkumin na Amurka ya tilastawa gwamnatin moduro sayar da manfetur ta barauniyar hanya ta hanyoyin masu shiga tsakani da kuma tankomin mai, don haka shugaban Amurka Trump yayi amfani da wannan mataki wajen ci gaba da ikirarinsa na rusa gwamatin Muduro saboda zarginsa da fataucin miyagun kwayoyi,
Yanzu haka dai Amurka tana so ta yi amfani da matakin doka wajen kwace tankokin mai na kasar venzuwela , kuma ta sanya takunkumi ga kamfanonin mai guda 6 dake da kyakkyawar dangantata da safarar manfetur na kasar venuzuwela.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu December 13, 2025 Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai December 13, 2025 MDD ta amince da kudurin da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agaji a Gaza December 13, 2025 Benin ta fitar da sammacin kama dan fafutuka Kemi Seba December 13, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan December 12, 2025 Birtaniya Ta yi Barazanar Yanke Gudunmawar Da Take Bawa Kotun Duniya December 12, 2025 Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare December 12, 2025 Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan December 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci