Leadership News Hausa:
2025-12-13@12:39:14 GMT

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

Published: 12th, November 2025 GMT

Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro

“Muna bincike wannan lamari, kuma muna tabbatar da cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka, za a kare shi. Ba za mu bari wani abu ya same shi (Yerima) ba matuƙar yana aikinsa yadda ya kamata kuma yana yin aikinsa sosai.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara

Rundunar ’yan sandan yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mutum mai suna Ahmed Abubakar mai shekara 32, bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai 1,000 ga ’yan bindiga a Jihar Zamfara.

Kwamishinan ’yan sanda na birnin, Miller G. Dantawaye, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a hedikwatar rundunar a Abuja ranar Laraba.

Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa

Dantawaye ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, kuma tawagar musamman ta rundunar ce ta kama shi bayan samun sahihin bayanan sirri a Unguwar Dodo da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana mu’amala da wani abokinsa da aka gano sunansa Yusuf Mohammed, inda aka gano cewa yana shirin sayo harsasai 1,000 domin kai wa ’yan bindiga da ke cikin daji a Zamfara.

“Bincikenmu ya ƙara nuna cewa wani ɗan uwansa, Ahmed Yakubu, ne ya turo shi kuma yanzu ya cika wandonsa da iska, domin ya sayo ya kuma kai wa ’yan ta’adda da ke aiki a yankin su na Zamfara,” in ji CP Dantawaye.

Ya ce wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama abokin aikin nasa da ya tsere.

Kwamishinan ya jaddada kudirin rundunar na kawar da masu aikata laifuka a Abuja da kewaye, tare da tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa ’yan sanda ta hanyar bayar da rahoton duk wani abin da ake zargin laifi ta layukan gaggawa na rundunar.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
  • Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda
  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
  • Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
  • ‘Yan Siyasa Ne Ke Zagon Ƙasa Ga Ci Gaban Nijeriya — Sarki Sanusi II
  • ‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’
  • Hukumomin Ilimi a Jihar Jigawa Sun Kare Kasafin Kudinsu a Gaban Majalisa
  • Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara