An gudanar da taro mai taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa”, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya dauki nauyi, a Johannesburg dake Afirka ta Kudu a ranar 11 ga wata. Jigon taron shi ne, “Matasa su tattauna kan tsarin shugabancin duniya, kuma su hada kai don samar da makoma irin ta zamani ga Sin da Afirka.

A gun taron, shugaban CMG, Shen Haixiong ya gabatar da rubutaccen jawabi, inda ya bayyana cewa, bai kamata matasan Sin da Afirka su shiga cikin harkokin shugabancin duniya kawai ba,matasa na da muhimmanci matuka wajen tsara tsarin shugabancin duniya. Ya kara da cewa, a ko da yaushe, CMG yana mayar da hankali kan hada kan matasan duniya, kuma yana goyon bayansu. Ya kara yin bayani cewa, ta hanyar amfani da harsuna 85 don watsa shirye-shirye ga kasashen duniya, CMG zai gina karin dandamali don tattara ra’ayoyi da tattaunawa, da ba da labarin matasa daga kasashe daban-daban game da yadda suke aiki tare, ta yadda za a taimakawa matasan duniya su inganta fahimtar juna ta hanyar musayar ra’ayoyi, da cimma matsaya daya ta hanyar cudanyar ra’ayoyi, da gabatar da damarmakin ci gaba, da kuma kirkirar makoma mai kyau tare. (Safiyah Ma)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya November 13, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu  November 13, 2025 Daga Birnin Sin Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe November 13, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar

Daga Usman Muhammad Zaria 

 

Ministan Yada Labarai Alhaji Mohammed Idris, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa jagoranci na gaskiya da tsari, yana mai cewa Jihar Jigawa ta zama abin koyi wajen gudanar da mulki da kuma ingantaccen aiki a ma’aikatu.

Ministan ya yi wannan yabo ne lokacin wata ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a Gidan Gwamnati da ke Dutse.

Muhammad Idris ya tuna da wata ziyarar da ya taba kaiwa Jigawa a baya, lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin duba harkokin noma. Ya ce yadda ya ga ana yin noman rani ya sa shi shauki game da irin ci gaban da ake samu a jihar.

Ya kuma bayyana godiyarsa kan kyakkyawan tarba da tawagarsa ta samu, yana mai cewa Jigawa jiha ce mai mutunci, zumunci da karimci.

Ministan ya kara tabbatar da aniyar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki, musamman ta hanyar gyaran da ake yi a rundunar tsaro domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

A jawabinsa, Gwamna Namadi ya yi maraba da ministan da tawagarsa, yana mai bayyana cewa taron matasan APC na Arewa maso Yamma wata dama ce ta musayar ra’ayi game da mulki, ci gaba da kuma bunkasar matasa.

Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen bunkasa karkokin matasa da mata a cikin tsarin shirye shiryenta na cigaban jihar.

“Muna goyon bayan mulikin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Mutanen Jigawa suna tare da shi, muna goyon bayan shirin sa na ‘Renewed Hope’ domin gina Najeriya mai da hadin kai,” in ji gwamnan.

Daga nan sai gwamnan tare da ministoci suka halarci taron matasan APC na Arewa maso Yamma a Dutse, inda aka tattauna batutuwan shugabanci, gudunmawar da matasa ke badawa, da ci gaba mai dorewa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya
  • Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya
  • An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea
  • Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu
  • Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
  • CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
  • Sudan ta soki shirun kasashen duniya game ta’asar dake faruwa a kasar
  • An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar