Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-11-13@10:01:07 GMT

Wata Gidauniya Ta Kaddamar Da Kwamiti Kan Mata A Nasarawa

Published: 13th, November 2025 GMT

Wata Gidauniya Ta Kaddamar Da Kwamiti Kan Mata A Nasarawa

Gidauniyar  fadakar da al’umma akan dokoki da ka’idoji ta Nijeriya ta kaddamar da kwamiti a jihar Nasarawa domin aiwatarwa da sa ido kan shirin mata, zaman lafiya da tsaro, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen gina zaman lafiya a cikin jihar.

Daraktan gudanarwa na gidauniyar, Mista Peter Maduoma, ne ya bayyana hakan a Lafia yayin taron horarwa na kwanaki uku da aka shirya ga masu ruwa da tsaki kan batun mata, zaman lafiya da tsaro, wanda gidauniyar ta shirya.

Mista Maduoma, wanda Jami’in Shari’a da Albarkatun Ƙasa na Gidauniyar, Mista Ifeyinwa Akwiwu, ya wakilta, ya ce shirin wani ɓangare ne na aikin gidauniyar mai taken “Ƙarfafa tsarin adalci ta hanyar kare haƙƙin ɗan adam da bunƙasa zaman lafiya a Najeriya.”

Ya bayyana cewa ana aiwatar da wannan shiri ne a jihohi biyar — wato Benue, Nasarawa, Plateau, Kaduna da Imo, domin haɓaka ingantaccen tsarin haɗin kai da amfani da bayanai wajen magance rikice-rikice ta hanyar tsarin da ya dace da bukatun mata.

Ya ƙara da cewa gidauniyar, tsawon shekaru 27, tana aiki wajen inganta tsaron jama’a, zaman lafiya da adalci a Najeriya da ma nahiyar Afrika ta hanyar bincike da fadarwa akan dokoki, da haɗin gwiwa da gwamnati da ƙungiyoyin farar hula.

A nasa jawabin, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar Nasarawa, Barista Isaac Danladi, ya yaba da muhimmiyar rawar da mata ke takawa a al’umma, yana mai cewa ma’aikatarsa ta tanadi matakai na tabbatar da gurfanar da masu aikata ta’addancin fyade da cin zarafi ga mata, domin zama izina ga wasu.

Ita ma Kwamishinar Mata da Harkokin Jin Kai ta Jihar Nasarawa, Hajiya Hauwa Jugbo, ta bayyana shirinta na yin haɗin gwiwa da duk ƙungiyoyin da ke da sha’awar kare haƙƙin mata, tare da bada tabbacin cewa ma’aikatarta za ta goyi bayan cikakken aiwatar da dokoki da ke tabbatar da haƙƙin mata da adalci ga waɗanda aka zalunta.

Aliyu Muraki, Lafia.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gidauniyar Nasarawa zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Shirya Faɗaɗa Gonakin Shinkafar Jangwa Don Ƙara Samar da Shinkafa

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe.

Gwamnan ya ce faɗaɗa gonakin zai ƙara hektar 3,000 daga yawan da ake da shi yanzu, domin inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar aikin gona. Ya kuma nuna yadda jihar ta samu ci gaba a fannin noma, inda gonar ta faɗaɗa daga hektar 2,000 a bara zuwa hektar 3,300 a wannan shekarar.

Gwamna Sule ya sanar da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da kamfanin Silvex International, babban kamfani mai sarrafa shinkafa, domin ƙara samar da shinkafa a jihar.

A cewar Gwamna Sule, haɗin gwiwar zai baiwa Silvex International damar sayen shinkafar kai tsaye daga gonakin jihar sannan a tattara ta a ƙarƙashin tambarin Nasarawa Agro-Commodity Company (NASACCO).

Shinkafar, wacce za a kaita Kasuwa da suna “NASACCO Gold”, ana sa ran zai ƙara shahara da darajar kayan shinkafar jihar a kasuwa.

Gwamnan ya yi godiya ga Silvex International bisa wannan haɗin gwiwa, wanda ya ce yana daga cikin matakan gwamnatinsa na jawo jarin masu zaman kansu zuwa fannin aikin gona a jihar.

Haka kuma, Gwamna Sule ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙara samar da shinkafa a jihar, tare da shirin faɗaɗa gonar zuwa hektar 8,000 nan gaba.

Gwamnan ya yaba wa matasa da al’ummomin garuruwan Jangwa, Ayakeke, da Agwatashi bisa jajircewarsu wajen tabbatar da nasarar gonar.

A nasa jawabi, Babban Jami’in Gudanarwa na Silvex International kuma Shugaban Aikin NASACCO, Abubakar Garba Ibrahim, ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin babban ci gaba ga kamfanin.

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar zai amfani jihar ta hanyoyi da dama, ciki har da haraji, ƙara darajar kayayyaki, da raba riba ta ƙarshe.

Aliyu Muraki, Lafia.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa
  • Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Shirya Faɗaɗa Gonakin Shinkafar Jangwa Don Ƙara Samar da Shinkafa
  • Karamar Hukumar Gwarzo Ta Kaddamar da Sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya
  • Abdel-Aty: Diflomasiyya Ce Kawai Hanyar Da Maido Da Zaman Lafiya A Libya
  • An Kaddamar Da Babbar Hanyar Mota Da Sin Ta Tallafa Wajen Ginawa A Namibia
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Hanyoyi Ba Naira Biliyan 81 A Malam Madori
  • Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano
  • Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5