Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto
Published: 2nd, August 2025 GMT
Bayan mutane da dama sun nuna ɓacin ransu kan al’amarin, gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamiti domin bincikar lamarin, tare da umarnin a miƙa masa rahoton cikin mako guda.
Gwamnan, ya taɓa goyon bayan jami’an tsaro wajen kama Danwawu, kuma ya umarci NDLEA ka da su sake shi.
Wani jami’i ya ce: “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki wannan aiki na Kwamishina a matsayin cin fuska ga gwamnatinsa da kuma yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.
An ruwaito cewar gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani shiri a ɓoye domin kama Danwawu, wanda Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Bakori ya jagoranta.
Me Ya Sa Gwamnan Bai Kore Shi Ba?Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi niyyar korar Namadi nan take, amma ya dakatar da hakan bayan ganawa da jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda shi ne ya bayar da sunan Namadi domin naɗa shi a matsayin Kwamishina.
Wasu majiyoyi sun ce gwamnan bai so naɗa Namadi ba tun da farko, amma saboda girmamawa da biyayya ga Kwankwaso ya ba shi muƙami.
Wani hadimina cikin gwamnatin ya ce: “Kwamishinan yana matsala da shugaban ƙungiyar direbobi ta NURTW, Kabiru Labour, saboda ƙoƙarin tilasta musu biyan harajin Naira 500,000 a kowane wata.”
“Haka kuma, Kwamishinan na gudanar da harkokin ma’aikatar ba tare da haɗin kai da sakatarenta Abdulmumin Babani ba. Saboda haka, sama da takardu 30 daga Ma’aikatar Sufuri ba su samu amincewar gwamna ba.”
Majiyar tace saboda rashin jituwa da kuma gazawar shugabancinsa, gwamnan yanke kauce wa hulɗa da ma’aikatar.
Martanin NamadiDa aka tambayi Namadi, ya ce: “Ban san da wancan zargin ba, kuma ba gaskiya ba ne.”
Sai dai ba da jimawa ba, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Waiya, ya ce an kawo ƙarshen lamarin.
Cikin fushi ya bayyana cewa: “Wane irin aikin jarida kake yi ne haka? Me ya sa kake bin wannan batun babu ƙaƙƙautawa? Me kake nema ne?”
Yadda Lamarin Ya Samo AsaliA ranar 24 ga watan Yuli, DAILY NIGERIAN ta fyadda Namadi ne ya taimaka wajen belin Danwawu, bayan kotu ta sanya masa sharuɗa masu tsauri.
A ranar 16 ga watan Yuli, kotu ta amince da buƙatar beli, amma ta buƙaci sai an samu Kwamishina a cikin majalisar zartarwa ta Jihar Kano da zai tsaya masa, tare da biyan Naira 5,000,000.
Namadi ne ya tsaya masa, ta hanyar rubuta wasiƙa zuwa kotun a ranar 18 ga watan Yuli, 2025, yana neman a amince masa domin ya tsawa wanda ake zargi.
Wasiƙar da jaridar DAILY NIGERIAN ta samu ta nuna cewa ya ce: “Ina roƙon kotu mai daraja da ta yadda na tsaya wa wanda ake tuhuma da laifi, Sulaiman Aminu, wanda aka bayar da beli kan kuɗi Naira 3,000,000 da kuma wanda zai tsaya masa. Sannan ya ajiye Naira 5,000,000.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Danwawu Gwamna Kwamishina Zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.
Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.
Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.
“Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon bayan ku don tabbatar da cewa an sanar da jami’an gwamnati tare da karfafa gwiwar su bi wannan sabon tsari,” in ji shi.
Da yake mayar da jawabi, shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya yi alkawarin wayar da kan jami’an gwamnati cikin tsanaki game da muhimmancin bayyana kadarorin su, kamar yadda hukumar da’ar ma’aikata ta ba su umarni.
Ya tunatar da cewa rashin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa ne.
Dagaceri ya bada tabbacin bada goyon baya da hadin kai domin cimma burin da ake so na wannan shiri.
USMAN MZ