2025-11-07@20:58:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8824

«wani sabon babi»:

      A nata tsokacin kuwa, kwamishiniya mai lura da ababen more rayuwa da makamashi a hukumar zartarwar kungiyar AU Lerato Dorothy Mataboge, kara tabbatar da alaka ta yi tsakanin hadin gwiwar Sin da Afirka, da burin da ake da shi na bunkasa masana’antu a sassan nahiyar.   Mataboge ta kara da cewa, yunkurin bunkasa samar da masana’antu a Afirka na bukatar karfafawa ta hanyar gina kwarewa, da horar da sana’o’i, da samar da cibiyoyi da albarkatun al’umma, don haka ta yi kira da a hada karfi-da-karfe wajen tsara shirye-shiryen bunkasa sanin makamar aiki a cikin gida, da samar da cibiyoyin horo masu nagarta, don horar da jama’a fasahohin amfani da makamashi marar gurbata yanayi. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
    “Mutanen duk sun manta da ‘yan garancin da suka yi gaba dayansu suka shiga wani sabon babi. Babban bango da ake ingina da shi ya fadi. Yanzu Kudancin Kaduna na jam’iyyar APC ne.” Ya yi bayanin komawar manyan mutanen biyu zuwa APC wani kokarin ci gaba ne na shi Kakakin majalisar, ya ce SHugaban majalisar ya kara jadddad Sanata Katung da Honorabul. Amos “sun zabi lamarin kawo ci gaba ne. Sun zabi su ci gaba da kasancewa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne da kuma APC. Wannan ba karamin sauya jam’iyya bane. Jirgizar kasa ce ta siyasa. Wani sabon babi ne ga siyasar Kudancin Kaduna, da kuma gaba dayan Nijeriya.” “’Yan ‘uwana maza da mata wannan sauay shekar wani...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birni Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassa Abu Turabi Fard, ya bayyana cewa; Tsayin dakar da kungiyar Hizbullah ta Lebabon da Ansurllah na kasar Yemn da kuma al’ummar Iran su ka yi wajen fada da masu girman kai na duniya, sakamako ne na koyarwar alkur’ani maigirma, Ahlul Bayt ( a.s) da kuma Ashura da jagorar matan duniya Fatima az-Zahra ( a.s). Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya ambato limamin na birnin Tehran yana kuma cewa; Makarantar gwgawarmaya tana yi wa zuriya bayan zuriya tarbiyya akan riko da gaskiya da kuma kalubalantar masu danniya. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
    Tarayyar turai ta bayyana cewa ma’aikatan Agaji ba za su iya isha cikin garin Al-fahar ba,kuma birnin ya zama tamkar makabarta. Tarayyar turai din ta  bakin mai Magana da yawunta Eva Herneserova ta kuma ce; Sudan ta zama daya daga cikin kasashen da gudanar da ayyukan agaji ya tsananta a duniya,kuma har yanzu da akwai fararen hula da aka killace su adaidai lokacin da ake ci gaba da kai wa asibitoci hare-hare. Eva Herneserova ta kuma ce; Babu sauki ko kadan a kokarin shiga cikin birnin domin isar da kayan agaji. Ma Magana da yawun kungiyar tarayyar turai din ta kuma yi gagradi akan cewa bai kamata a rika amfani da yunwa da kuma kisan kiyashi a matsayin makamin yaki...
    Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
    Kwamandan Ƙungiyar sa kai ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) reshen Jihar Kaduna, Abdulwahab Muhammed ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta amince da Ƙungiyar a matakin ƙasa ta hanyar sanya hannu a kan ƙudurin da aka gabatar. A cewar ƙungiyar bisa la’akari da irin rawar da take takawa wajen daƙile ayyukan miyagu da samar da tsaro a sassan ƙasar nan. An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta sa hannu kan kudurin amincewa da kungiyar domin kasancewa cikin jerin hukumomin tsaro na kasa, la’akari da irin jajircewar da suke nunawa musamman a Jihar Kaduna. Abdulwahab...
    3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
    Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 ​​a cikin  masai. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a. Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai. “Hukumar kashe gobara ta...
    Wata kotu a Ƙasar Jamus ta yanke wa wani ma’aikacin jinya hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin kashe marasa lafiya 10 da kuma yunƙurin kashe ƙarin wasu 27 ta hanyar yi musu allurar guba. Kotun da ke birnin Aachen a yammacin Jamus, ta tabbatar da cewa mutumin mai shekaru 44 ya aikata laifukan ne tsakanin watan Disamban 2023 zuwa Mayun 2024 a asibitin Wuerselen. Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kotun ta bayyana cewa laifin da ya aikata babban laifi ne, wanda zai hana shi samun ’yanci bayan shekaru 15 kamar yadda ake yadda...
    “A yayin da ake tarwatsa masu kai harin, DPO na Sassan A da B sun tura ma’aikatansu suka harba hayaki mai sa hawaye, amma wasu motoci cikin motar gwamnan sun lalace,” in ji Abiodun. Ya bayyana cewa mutane uku na farko da ake zargi sune Ali Mohammed da Adamu Hussain, dukkansu daga yankin Nasarafu, Bida, da Isah Umaru na yankin Darachita, Bida. Ya kara da cewa an kama Nagenu, mai shekaru 39, daga yankin Bello Masaba, daga baya dangane da wannan lamari, sannan ya ambaci wasu biyu, Salihu Mohammed da Abdulrahman Baba, yayin tambayoyi. “Dukkan wadanda ake zargi suna karkashin bincike kuma suna taimaka wa ‘yansanda wajen gano wasu. Ana ci gaba da kokarin kama karin mutane da ake zargi,”...
    Ina gaishe da Mamana da Babana, sai kannena Labiba, Nasira, Fati, Maimuna, Khairat, da yayyene Yaya Muhammad, Yaya Ibrahim, Yaya Maryam, Yaya Abu, Yaya Larai. Sannan malaman makarantarmu na boko da islamiyya, Malama Aisha, Malama Kubra, Malam Isah, Malam Nuhu, Malam Yahyah, Malama Batulu, ai kawayena na boko da na islamiyya kamar su Wasila Sabo, Fatima Muhammad, Hauwa Yunus, Walida Tahir, da dai sauransu. Da fatan sunyi Juma’a lafiya. Sako daga Ummu’aimana daga jihar Gombe: Ina gaishe da Mahifana, da fatan Allah ya kara masu lafiya da nisan kwana, sai y’an’uwa, makoftana, dama kawayena irinsu Zahra’u(maman daddy), Bara’atu Saleh, Shafa Liman mai turare, Asiya Muhammad Tayo (maman Shahid), sai Binta Usman,p Jummai, Yahanasu Jabir, Fatima Jafar, Alhaji Abdulkadir Abdullahi, Zakiyya,...
    “Wannan mummunan hari ya yi sanadiyyar mutuwar jaruman jami’an tsaro da suka sadaukar da rayukansu wajen kare shi,” in ji sanarwar. Majalisar ta yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu, da hukumomin tsaro, da al’ummar jihar Neja, tare da yi wa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙin cikin gaggawa. A ƙarshe, Majalisar Wakilai ta sake tabbatar da jajircewarta wajen ganin an tabbatar da tsaron jama’a da jami’an gwamnati. Ta yi alƙawarin ci gaba da bai wa ɓangaren zartarwa da hukumomin tsaro goyon bayan doka wajen yaƙi da ta’addanci, da fashi da makami, da sauran nau’o’in laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa...
    Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna...
    Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin megawat 1 a garin Talasse, karamar hukumar Balanga. Aikin, wanda aka kulla ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), Bankin Duniya, da kamfanin MIDS Dynamics, na da aniyar samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba ga sama da gidaje 8,000 a Talasse da kauyuka makwabta, idan aka kammala shi cikin watanni huɗu. Harin bam a masallacin Juma’a ya jikkata sama da mutum 50 a Indonesia Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 A wajen bikin kaddamar da aikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana shi a matsayin muhimmin ci gaba a...
    ’Yan sanda a kasar Indonesia sun ce an garzaya da daruruwan mutane zuwa asibiti bayan wani abu da ake zargin bam ne ya fashe a wani masallacin Juma’a da ke Jakarta babban birnin kasar. Lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma’a a cikin wani ginin makaranta da ke Kelapa Gading, a arewaci Jakarta. Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Kwamishinan ’yan sandan birnin, Asep Edi Suheri, ya ce har yanzu ana bincike don gano musabbabin fashewar. Shaidun gani da ido sun ce sun ji fashewa biyu masu ƙarfi da misalin ƙarfe 12 na rana a agogon kasar, daidai lokacin da aka fara hudubar sallar Juma’a...
    Dangane da fargaba game da karancin abinci na amfanin gona da aka canza jinsinsu (GMOs), farfesan ya ce domin tabbatar da lafiyar abinci da kare lafiyar jama’a, dole ne kowace iri da za ta shigo kasar ta bi matakan doka da ka’idoji da ke tabbatar da cewa tana da aminci. Ya ce, dokokin da ake amfani da su wajen kula da GMOs ma sun fi tsauri fiye da na amfanin gona na gargajiya saboda an kara musu sinadaran halittu (genetic materials). “Kafin a saki kowane irin amfanin gona domin a fara amfani da shi a kasuwanci, dole ne ta bi diddigin binciken halittu da sinadaran gina jiki sosai. Bayanai da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa amfanin...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza. Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin...
    Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da dage takunkumin da ya sanya wa al-Julani Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a ranar Alhamis domin amincewa da daftarin kudirin da zai cire takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Shugaban rikon kwaryar kasar Siriya Abu Muhammad al-Julani da Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Anas Khattab, inda kasashe 14 suka kaɗa ƙuri’a kan amincewar, yayin da kasar China ta kauracewa kada kuri’a. Daftarin kudurin, wanda Amurka ta rubuta kuma ta gabatar, ya yi kira da a dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa al-Julani da Khattab. A cewar jami’an diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya, ofishin jakadancin Amurka ya rarraba daftarin kudurin ga mambobi, kuma an...
    Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya a daidai lokacin da ake kara samun karuwar fada a Darfur da El Fasher Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi gargadin cewa: Matsalar karancin abinci mai gina jiki ta kara ta’azzara a Sudan, yana mai tabbatar da cewa matsalar karancin abinci mai gina jiki ta wuce matakin gaggawa a cikin sama da kashi 60 cikin 100 na yankunan. A halin yanzu, shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya jaddada kudurin rundunar sojin kasar na tabbatar da tsaron dukkan iyakokin Sudan da kuma murkushe ‘yan tawayen. Wani sabon gargadin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya Sudan a kan gaba wajen fuskantar bala’in...
      ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an November 6, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025 Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025
    Yau 7 ga watan Nuwamba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Paul Biya murnar yin tazarce a wani sabon wa’adin shugabancin kasar Kamaru. Shugaba Xi ya ce, kasar Sin da Kamaru suna da daddadiyar alaka mai kyau. A cikin ‘yan shekarun nan, amincewar siyasa tsakanin kasashen biyu ta kara zurfafawa, kuma an samu nasarori masu yawa a fannoni daban-daban na hadin gwiwa, tare da mara wa juna goyon baya a kan batutuwan da suka shafi muradunsu da kuma batutuwa masu muhimmanci. A shekara mai zuwa ce za a cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Kamaru, matakin da ya samar musu da sabbin damammaki na ci gaban huldarsu. Xi yana dora muhimmanci sosai kan ci...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho November 7, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria October 25, 2025 Tattalin Arziki Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life October 25, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025 Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari  November 7, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT November 6, 2025
    Shugaban ya kuma yaba bisa gudunmawar da kwararrun matasa ke samar wa, musamman masu yiwa kasa hidima da ke yin aikin yiwa kasa hidama, a Hukumar ta NPA. Ya danganta su a matsayin matasan gobe da za su samar da sauyi wajen ci gaba da bunkasa fannin tattalin azrki na Teku da kuma ga daukacin tattalin arzikin kasar nan. An kirkiro da wannan ranar ta NMD ce, a shekarar 2014 wadda kuma aka kaddamar da ita a kasar Ingila a shekarar 2016, wadda kuma ake gudnar da bikin zagoywar ranar, a duk ranar 27 na watan Okutobar kowacce shekara. Kazalika, gudanar da bkin wannan ranar, ta yi daidai da cimma muradun karni, na Majalisar Dinkin Duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
    A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Trump ya sake mayar da Nijeriya matsayin kasa mai matukar damuwa, sannan ya yi gargadin cewa; “idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bayar da izinin kashe kiristoci, nan take Amurka za ta dakatar da duk wani taimako da take bai wa Nijeriya, sannan kuma mai yiwuwa ta shiga kasar, domin kakkabe ‘yan ta’addan Islama da ke aikata wadannan munanan ayyuka na ta’addanci.” Kazalika, ya kuma umarci Ma’aikatar Yakin Amurka, da ta shirya domin daukar mataki. Pete Hegseth, Sakataren Yakin Amurka, a ranar Asabar ya ce; Ma’aikatar Yaki na shirin daukar mataki. Barazanar Trump dai, ta biyo bayan zargin da wani dan majalisar dokokin Amurka, Ted Cruz, ya yi a shafinsa na D,...
    Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na shiyyar Abuja (AEDC) ya fara aikin rage ma’aikata kusan 800, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da fama da hauhawar farashi, tsadar rayuwa, da rashin tabbas wajen samun wutar lantarki. Matakin korar wanda ta fara a ranar Laraba, ya biyo bayan watanni na sake fasalin cikin gida a kamfanin da ke ba da wutar lantarki ga Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Kogi, Neja da Nasarawa. Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa shugabannin kamfanin sun fara ne da shirin korar ma’aikata 1,800, kafin su rage...
    Sai dai, bisa batun gasakiya, karya ce tsagwaronta kan batun kisan kiyashin da ake yamadidin cewa, ana yiwa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya. Bugu da kari, wannan batun ana wani yunkuri ne na son kawo rudadi a kasar nna, musamman duba da cewa, masu son kawo rudadin, a zahiri, sun jahilci irin yanayin sarkakiyar lamarin tsaro na kasar nan. Wannan Jaridar, ta sha yin tsokaci, kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar nan, tare da kuma yawan gabatar da kira ga Gwamnatin kasar da ta tashi tsaye, domin daukar matakan da suka dace, na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya. Batun aikata ta’addanci, yin garkuwa da mutane da kuma aukuwar rikici a tsakanin manoma da makiyaya, matsaloli ne, da...
    An rantsar da Paul Biya mai shekaru 93 a matsayin shugaban kasar Kamaru karo na takwas a majalisar dokokin kasar da ke Yaoundé. Ya shafe shekaru 43 yana mulki, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai. Biya wanda shine shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na kuri’un zabe, yayin da abokin hammayarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar kasa. Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaben, yana zargin cewa an yi maguɗi,wanda hukumomi suka musanta. Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi. Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alkawarin dawo da doka a kasar...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan yace rarrabuwa da sabanin tsakanin musulmi shi ne babban abin da makiya musulunci suke so, kuma yayi gargadin cewa rabe-rabe na cikin gida yana kare manufofin makiya ne da kasashe ma’abota girman kai na duniya. shugaban ya fadawa manya- manyan malaman Ahalus sunna da sauran malaman addini dake Sanandaj a yammacin lardin Kurdistan cewa ta hanyar hadin kai da rikon amana da kuma riko da yan uwantaka na musulunci ne kawai  musulmin duniya za su iya tunkarar makircin Amurka da Israila da ma sauran yan sahayuniya. Har ila yau ya kara da cewa wannan rarrabar ce isra’ila da Amurka da sauran yan sahyuniya na duniya suke so, domin su shagaltar da kasashen musulmi su yi...
    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya “ta hanyar difilomasiyya” game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a yanzu. Kalaman shugaban na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kutsawa Najeriyar domin kai wa ‘yan bindiga hare-hare bayan ya zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale su suna “yi wa Kiristoci kisan gilla” Da yake magana yayin zaman majalisar ministocinsa a jiya Alhamis, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen”ta’addanci”. “Duk da kalubalen irin na siyasa da fargabar da mutanenmu ke ciki, muna ci gaba da tattaunawa da kawayenmu, muna tattaunawa a difilomasiyyance,” “Ina tabbatar muku cewa za mu kawo karshen ta’addanci. Abin da muka saka a...
    Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya ta buɗe kofofin tattaunawa da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, dangane da barazanar kasar ta kaddamar da yaki a Najeriya. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, Ministan ya ce gwamnatinsu ba ta son ƙara yin yamadidi da maganar. An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa “Babban nauyin da ke kanmu a matsayin gwamnati shi ne tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar mataki a kan duk wata damuwa ta gaskiya da ke da alaƙa da tsaron ’yan...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST November 6, 2025 Daga Birnin Sin Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya November 6, 2025 Daga Birnin Sin Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji November 6, 2025
    Kungiyar Genoa ta naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Italiya, Daniele De Rossi, a matsayin sabon kociyarta, domin maye gurbin Patrick Vieira wanda ya bar ƙungiyar a ƙarshen mako. A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Genoa ta bayyana cewa tana “maraba da Daniele De Rossi” wanda ya jagoranci atisaye na farko da yammacin wannan ranar. Za a gudanar da taron manema labarai na farko da shi a ranar Juma’a.” Victor Osimhen ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a Champions League Ajax ta kori kocinta John Heitinga De Rossi, wanda ya taka leda na tsawon shekaru 17 a Roma kuma ya lashe Kofin Duniya tare da Italiya a 2006, ya taɓa horas da ƙungiyoyin Spal da Roma. Roma...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya  November 6, 2025 Labarai Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu November 6, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari November 6, 2025
    Ɗan wasan gaba na Nijeriya, Victor Osimhen, ya sha gaban fitattun ‘yan wasa irin su Erling Haaland, Harry Kane, da Kylian Mbappé a yawan zura ƙwallaye a gasar Champions League ta bana. Osimhen ya cimma wannan nasarar ce bayan ya zura ƙwallaye uku rigis a ragar Ajax a wasan zagaye na huɗu na gasar. Ajax ta kori kocinta John Heitinga Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe Wannan ya kai adadin ƙwallayensa zuwa shida, yayin da Haaland, Kane da Mbappé ke da ƙwallaye biyar-biyar kowannensu. A watan da ya gabata, Osimhen ya kuma zura ƙwallaye uku a ragar Jamhuriyyar Benin a wasan neman tikitin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026, abin da ya ƙara masa farin jini a...
    A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar gina ingantaccen yankin ciniki cikin ’yanci na tashar ruwa ta Hainan ko FTP a takaice. Shugaba Xi ya bayyana bukatar ne yayin dake sauraron rahoton aiki game gina yankin na FTP a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. A cewarsa, gina yankin FTP na Hainan muhimmiyar manufa ce ta kwamitin kolin JKS, wadda aka tsara domin zurfafa cikakkun sauye-sauye, da bude kofa ga waje a sabon zamani. Shugaban na Sin ya kara jaddada bukatar kyautata nazari, da aiwatar da ka’idojin aiki na cikakken zama karo na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, tare da kokarin cimma burikan da aka sanya gaba, dangane da bunkasa yankin...
      Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin cin zarafin Kiristoci da sauran tsirarun addinai a Nijeriya.   Dan majalisa Smith ya yaba wa shugaban Amurka Donald Trump kan ayyana Nijeriya a matsayin ‘Kasar da ke da damuwa ta musamman’ (CPC), inda ya ambato cewa, akwai rahotanni da ke cewa, ana kai wa Kiristoci hare-hare a sassan jihohin Benuwe da Filato. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama November 6, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro November 6, 2025 Manyan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Harin Amurka ya bayyana karara kan Venezuela Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Barazanar da ake yi wa Venezuela ba ta dace da al’ummar duniya ba, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance kuma za ta ci gaba da kasancewa cikin hadin kai da gwamnati da al’ummar Caracas. Da yake jawabi a bikin rantsar da ofishin wakilin Ma’aikatar Harkokin Waje a Lardin Hamadan, Araqchi ya bayyana cewa: Wannan ofishin zai taimaka wajen karfafa alakar tattalin arziki, kimiyya, da al’adu ta lardin, da kuma sauƙaƙe hulɗar jakadanci da gudanarwa ga ‘yan ƙasar. Ya lura cewa: Baba’i Ragheb, wani jami’in ma’aikatar da ya ƙware, zai jagoranci sabon...
    Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran ya jaddada muhimmancin aiwatar da kuma kammala yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Pakistan Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqir Qalibaf, ya jaddada muhimmancin matakin da ake dauka a yanzu na dangantakar da ke tsakanin Iran da Pakistan a dukkan fannoni na hadin gwiwa. Ya bayyana ziyararsa zuwa Pakistan a matsayin wani bangare na kokarin da ake yi na fadada dangantaka, musamman hadin gwiwar yankin tsakanin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillacin labaran Iran ‘IRNA’ bayan ya isa birnin Islamabad, fadar mulkin kasar Pakistan, a safiyar Laraba, Qalibaf ya ce: “Iran da Pakistan, a matsayin kasashe makwabta, suna jin dadin hulda daban-daban a fannin tattalin arziki, siyasa, da...
    Kwamitin Tsaro Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Amurka ta bukaci duba kudurin da aka gabatar na neman kafa rundunar kasa da kasa a Gaza Rahotannin daga Amurka sun bayyana cewa: Gwamnatin Amurka ta Trump tana neman amfani da rikicin Gaza wajen kwace makaman kungiyar Hamas da take amfani da ramuka wajen yakar ‘yan sahayoniyya, don aiwatar da wani tsari na kwace makamai daga hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa. A ƙarƙashin tutar tsaro da kwanciyar hankali, Amurka, da kuma Isra’ila, suna ƙoƙarin kafa sabon tsari a Gaza wadda ke neman murkushe ‘yan gwagwarmaya, tare da tabbatar da tsarin babakeren ‘yan mamaya karkashin wani tsari mai sauƙi, da zai buɗe sabon babi na iko a kan yankin. A tsakiyar tambayoyi game da...
    Muhimmin fadakarwa daga Sayyid Muqtada al-Sadr kwanaki kafin zaɓen kasar Iraki Malamin Tafarkin Shi’a na Iraki Muqtada al-Sadr ya umurci magoya bayansa a ranar Alhamis da su dakatar da duk wani zaman dirshan da zanga-zanga har zuwa lokacin zaben ‘yan majalisa dokokin kasar mai zuwa. A cikin wata sanarwa, ofishin al-Sadr ya ce ya yi nazari kan ayyukan da suka hada da tarurrukan kabilanci da na matasa da ke goyon bayan shawararsa ta kauracewa zaben kuma ya yi tsokaci, “Daga yanzu har zuwa ranar zabe, babu bukatar wani karin zanga-zanga.” Wannan shawarar ta ci gaba da tsarin al-Sadr na nisantar da kansa daga tsarin zaben tun bayan sanarwarsa a watan Yunin shekara ta 2022 na janye kansa gaba daya daga...
    An rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas mai shekaru 93 a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé. Paul Biya ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai nan gaba. Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa Biya wanda shine shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na ƙuri’un zaɓe, yayin da abokin takararsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar ƙasa. Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaɓen da aka yi yana kuma zargin cewa an yi maguɗin zabe, wanda hukumomi suka...
    A wasan farko na gasar cin kofin ƙwallon yashi wato Beach Soccer da aka fara gudanarwa yau Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, Kada BSC ta lallasa Kebbi BSC da ci 8 – 5. Kada ta samu nasarar zura ƙwallayen ne ta hannun Frank Dozievda da ya zura 4 a raga, sai Sani Hassan 2, sai kuma Hammed Kareem shi ma da ya zura ƙwallaye 2 a raga. Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa Sojin Amurka sun gabatar da shirin ƙaddamar da hari a Najeriya A ɓangaren Kebbi United kuwa ‘yan wasan na biyar ne kowanne ya zura ƙwallo a raga da suka haɗa da: Isyaku Atiku da Ibrahim Malami da Sadik Umar da Abdullahi Aliyu da...
    Kwamishinan lafiya na Jihar Adamawa, Dokta Felix Tangwami ya bayyana cewa, cutar kwalara a Ƙaramar hukumar Mubi ta yi sanadin mutuwar mutane 10, inda ya buƙaci mazauna yankin da su kula da tsaftar jikinsu. Da yake yi wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) bayani a Yola ranar Laraba, Tangwami ya ce marasa lafiyan sun mutu ne a gida maimakon a cibiyoyin lafiya. Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maita Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ɗauki matakin gaggawa don daƙile ɓarkewar cutar. “Tun daga farko, mun ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin, kasancewar mu a can, kuma ba...
    Wasu fusatattun matasa a ƙauyen Sokupkpan da ke karamar hukumar Edu a jihar Kwara, sun kashe Babban Limamin yankin, Mallam Abdullahi Audu, bisa zargin shi da alhaki kan mutuwar wani matashi, Ibrahim Gana ta hanyar maita. Shaidu sun ce lamarin da ya faru a ranar Laraba ya jefa al’ummar yankin cikin rudani da firgici. Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An ce wannan farmakin ya samo asali ne daga zargin cewa limamin ya yi amfani da maita wajen cutar da mamacin. A cewar majiyoyi, kafin rasuwarsa, Gana ya dade yana fama da wata cuta da ba a bayyana ba, kuma ya sha faɗa cewa Babban...
    Dakarun Sojin Amurka sun kammala shirye-shiryen kai hare-hare a Najeriya bayan umarnin da Shugaba Donald Trump, ya bai wa Ma’aikatar Tsaron ƙasar kan ɗaukar mataki game da zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa rundunar sojin Amurka da ke nahiyar Afirka (AFRICOM), ta gabatar da yadda hare-haren za su kasance. An kama mutum 2 kan sukar shugaban karamar hukuma a Kano Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Daga cikin shirin akwai kai wa ’yan ta’adda hare-hare da jiragen yaƙi da amfani da jirage marasa matuƙa. Sannan kuma akwai tsarin haɗin gwiwa da sojojin Najeriya ta hanyar musayar bayanan leƙen asiri da tallafin kayan aiki. Sai dai...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba. Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12.   Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni. A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu. A yau, Iran tana...
    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa Moscow za ta dauki “matakan mayar da martani” idan Amurka ta koma gwada makaman nukiliya, a yayin da ake kara samun takun saka tsakanin manyan kasashen biyu masu makamman nukiliya. A yayin wani taro da ya yi da Majalisar Tsaron Rasha a ranar Laraba, Putin ya umarci Ma’aikatar Harkokin Waje, Ma’aikatar Tsaro, hukumomin leken asiri, da su tantance yiwuwar sake fara gwaje-gwajen makamman nukiliya da kuma gabatar da shawarwari don matakan farko. “Dangane da wannan batu, ina umurtar ma’aikatun dasu gabatar da shawarwari kan matakan farko da za su iya mayar da hankali kan shirye-shiryen gwaje-gwajen makaman nukiliya,” in ji Putin. Umarnin da ya bayar ya nuna martani ne ga umarnin da...
    Kasahen Iran, Rasha da kuma China sun gana a tsakaninsu a jajibirin taron Kwamitin Gwamnonin Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA),  Zaman ya hada jakadun kasashen uku a birini Vienna ranar Laraba don daidaita matsayinsu kan manyan batutuwan da suka shafi zaman na gwamnonin IAEA da ke tafe. Michael Ulyanov, jakadan Rasha kuma wakilin dindindin a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa kasashen uku sun yi “wani zagaye na shawarwari ” game da batun nukiliyar Iran. Ya kara da cewa wakilan sun daidaita matsayinsu don su shirya sosai don taron Kwamitin Gwamnonin da ke tafe. A cewar shirin da aka sanar, za a gudanar da zaman kwamitin na gaba daga ranar...
    Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da matakin da Gwamnatin Amurka ta dauka na sanya sunan Najeriya cikin jerin “Kasashen Da Ake Tauye ’Yancin Addini” , wato jerin kasashen da ake zargi da take hakkin addini. Ministan Yada Labarai da Al’adu, Mohammed Idris Malagi ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya ba ta shafi wani rukuni na addini ko kabila kai-tsaye ba. Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai Ya ce masu yada bayanan karya ne suka sa ake ganin kamar Najeriya tana nuna bambanci ta fuskar addini. Malagi, ya ce...
    Ya yi Allah-wadai da wannan lamari, tare da roƙon Allah Ya tona asirin waɗanda suka aikata laifin kuma Ya kare ƙaramar hukumar Gaya daga irin wannan lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro November 6, 2025 Labarai Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140 November 5, 2025 Labarai Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i November 5, 2025
    Gwamnatin Najeriya ta jaddada matsayinta na yin watsi da ayyata a matsayin kasa mai take hakkokin addinai da Amurka ta yi. Da yake kare tarihin Najeriya, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce “barazanar Trump na ɗaukar matakin soja ba ta da tushe kuma hakan yana a matsayin kawar da ido ne daga ƙalubalen tsaro masu sarkakiya da Najeriya ke fuskanta,” ya ƙara da cewa “duk wani labari da ke nuna cewa Najeriya ta gaza ɗaukar mataki kan hare-haren da ake kai wa mabiya addini ya dogara ne akan bayanan ƙarya ko maganganu marasa tushe.” A ranar Litinin, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Olufemi Oluwedi, ya bayyana cewa “Najeriya tana fuskantar ta’addanci, ba kai...
    Tawagar masu sa ido ta Tarayyar Afirka ta sanar a ranar Laraba cewa zaɓen Tanzania “bai cika ƙa’idodin dimokraɗiyya ba,” tana mai tsokaci kan zaɓen da aka yi jayayya a kansa wanda ya haifar da zanga-zanga mai tsanani kwanan nan. An ayyana Shugaba Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen da gagarumin rinjaye a zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga Oktoba, amma ‘yan adawa sun zargi gwamnati da yin magudi a zaɓen, kuma zanga-zangar ta ɓarke ​​bayan da aka soke manyan abokan hamayyarta. Tawagar ta ƙara da cewa “a wannan matakin farko, tawagar ta kammala da cewa babban zaɓen 2025 a Tanzania bai yi daidai da ƙa’idodin Tarayyar Afirka da tsarin ƙa’idoji na kasa da kasa...
    Gwamnatin Tarayya ta ce ƙofofinta buɗe suke ta sayar da dukkan matatun manta na Warri, Fatakwal da Kaduna ga ’yan kasuwa domin ƙarfafa gasa a fannin tace mai a Najeriya. Mai ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wata hira da Bloomberg TV a gefen taron makamashi na ADIPEC da aka gudanar a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa, ranar Talata. Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir Verheijen ta ce wannan mataki na daga cikin shawarwarin da ake dubawa don inganta harkar man fetur a Najeriya. “Daya daga cikin matakan da za...
    Hafsan Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci dukkanin kwamandojin rundunar da su ƙara ƙaimi wajen yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta ta sama  A yayin wani taron da suka gudanar da Abuja a ranar Laraba, Aneke, ya umarci kwamandojin da su kai hare-hare masu yawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa. Za a gudanar da wasannin ƙwallon yashi a Abuja An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Ya ce, “Dole ne yayin kowane aiki a nuna ƙwarewa da ƙaunar ƙasa.” Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce taron ya mayar da hankali kan duba dabarun aiki da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin kwamandoji....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.   A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta. Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Shirin Najeriya  A...
      “Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.   Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.   A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.   An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
    Hukumar shirya gasar ƙwallon yashi ta ƙasa ta tabbatar da cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na bana a filin wasa na Jabi Lake Park, da ke babban birnin tarayya Abuja. Kodinetan hukumar a Najeriya, kuma shugaban hukumar a nahiyar Afirka, Mahmud Hadejia, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da Trust Radio a cikin shirin “Bakin Raga” da safiyar yau Laraba. An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Shugaban ya bayyana cewa wannan ce gasa ta biyar da za a buga, kuma ta farko da za a fafata a Abuja. A cewarsa, za a fara buga wasannin ƙarshe daga...
    Majalisar Tarayya ta amince da hukuncin cin sarƙa ga duk wani malami da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a makarantu a faɗin ƙasar nan. Hakan ya biyo bayan amincewar majalisar da Dokar Hana Lalata da Dalibai ta 2025 (HB.1597), bayan tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai a ranar Laraba. Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos A ƙunshin bayanan da dokar, za a iya yanke wa duk wanda ya saɓa mata hukuncin ɗaurin shekara 14 ko shekara biyar mafi ƙaranci ba tare da zaɓin biyan tara ba. Laifukan da dokar ta bayyana a matsayin cin zarafi sun haɗa da...
      A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina. Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka.   Wani abu da na lura da shi...
    Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu A cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu. Duk da ƙoƙarin jama’a na...
    Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.   Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A...
      Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou November 5, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE  November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025
    Wani jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a shataletalen Abbatuwar Phototake da ke birnin Jos a Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa an tabbatar da mutuwar direban da wani fasinja guda ɗaya, tare da jikkatar wasu mata biyu. Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Laraba, bayan tasowar jirgin daga Bukuru zuwa Jos. Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu Likitoci sun wayar da kan mata kan cutar Sankara a Gombe Wasu mazaunan yankin sun ɗora alhakin faruwar hatsarin kan rashin mutumin da ke kula da shingen tsallaka titin jirgin, wanda ya ratsa titin motoci a daidai shataletalen Abbatuwar Phototake. Sai dai mai magana da yawun...
    Majalisar Dattawa ta dakatar da aikin tantance Dokta Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa domin zama minista, sakamakon rashin gabatar mata da rahoton jami’an tsaro a kansa. Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya ce ba za su ci gaba da tantancewar ba sai an samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro. Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano A ranar Talata ce Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar sunan Mista Udeh, ɗan asalin Jihar Enugu cikin wata wasiƙar neman sahalewarta. “Ina farin cikin miƙa sunan Dokta Kingsley Tochukwu...
    Kungiyoyin da suka yi hadin gwiwar shigar da karar sun hada da Interfaith Partners for Peace and Development, Fityanul Islam of Nigeria, Sairul Qalbi Foundation, Tijjaniyya Youth Enlightenment Initiative, Hablullahi Mateen Foundation, Dariqa Qadiriyya of Nigeria, Kadiriyya Youth Awareness, Kadiriyya Riyadul Janna Kofar Na’isa, Ashabul Kahfi Foundation, da Majmau Ashabul Yameen.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa, takaddamar da ta shafi Malam Lawan Triumph ta fara ne a watan Satumba bayan da wasu ƙungiyoyin addini suka ɗauki wasu wa’azozinsa a matsayin ɓatanci ga Annabi SAW, wanda ya haifar da cece-kuce da muhawara a faɗin jihar. Wannan lamari ya sa gwamnatin jihar ta shiga tsakani ta hannun Majalisar Shura ta Jiha, wadda aka ba da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.  ...
      Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025 Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio November 5, 2025
    Kungiyar ‘yan tawayen M23 tare da hadin gwiwar kungiyar AFC sun kafa kotunan shari’a a cikin yankunan da suke iko da su a gundumar Kivu ta Arewa. A garin Goma kungiyar ta sanar da kafa kotuna 378 a fadin yankunan da suke karkashin ikonta, lamarin da gwamnatin Kinshasha ta bayyana a matsyin haramtacce. Wani makusancin kungiyoyin tawayen dake rike da yankunan gabashin DRF, Elie Mutela ya sanar da cewa; Tsarin mulkin kasar ya tabbatar da cewa bai kamata a bar mutane ba tare da tsarin shari’a ba, wannan ne dalilin da ya sa kungiyoyin M23/AFC su ka kafa kotuna domin yi wa mutane shari’a akan matsalolin yau da kullum. Tun a ranar 14 ga watan Satumba ne dai aka fara...
    Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko.   A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora daga makaranta sakamakon faduwa a jarrabawa.   Bayan tattaunawa, shugaban majalisar Jibrin Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin ilimi domin ci gaba da bincike da neman shawarwari. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana...
    Ƙungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) tare da Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Gabas (NEDC), sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kan mata game da cutar sankara a Jihar Gombe, domin kare mata daga kamuwa da cutar. Dokta Halima Usman Faruk, ɗaya daga cikin likitoci mata da suka halarci wajen taron ta ce, cututtukan sankarar nono da bakin mahaifa na kashe mata da dama a duniya, musamman a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya. Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri “A Gombe kawai, ana samun aƙalla sabbin mata bakwai masu fama da sankara a duk mako. “Don haka yana da muhimmanci mata su rika zuwa...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce zai ci gaba da yin siyasa matuƙar yana numfashi a doron duniya. Shekarau ya bayyana cewar siyasa wata babbar hanya ce ta hidima wa jama’a. Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano Yayin da yake hira da ’yan jarida a Kano a yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 70, Shekarau, inda ya ce gina siyasarsa ne bisa tafarkin addini da ɗabi’a. “Siyasata addinina ce, addinina kuma siyasata ce. Shiga cikin tsarin samar da shugabanni na gari masu gaskiya hidima ce ga jama’a kuma wannan ibada ce a Musulunci,” in ji shi. Tsohon...
    Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum,  ya mika motocin sintiri 63 ga hukumomin tsaro da kuma Rundunar Hadin Gwiwa ta Farar Hula (CJTF) da ke aiki a Maiduguri da kewaye. Daga cikin motocin 63, an ba da motocin 30 ga sassa daban-daban na Sibiliyan JTF, 16 ga Jami’an tsaron kai daukin gaggawa don dakile masu aikata laifukan cin Zarafi, 10 ga kungiyoyin tsaro, 6 ga mafarauta da kuma daya ga jami’an Hukumar Kula da Fataucin Mutane (NAPTIP). Rarraba motocin yana da nufin inganta karfin yin sintiri da mayar da martanin gaggawa musamman ga ‘yan sanda, sauran jami’an tsaro, da rundunar hadin gwiwa ta farar hula wajen magance barazanar...
      Haka kuma, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Sin za ta soke matakin da ta dauka a kan wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin kamfanoni marasa aminci da ta sanar a ranar 4 ga Maris na wannan shekara, kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana a cikin wata sanarwa.   Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa kamfanonin cikin gida za su iya gabatar da bukata da neman yin ciniki da kamfanonin Amurka da aka ambata a sama da zarar an amince da bukatunsu. (Amina/Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri. Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya. Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka An raba motocin ne domin inganta sintiri da kai ɗaukin gaggawa, domin yaƙi da laifuka da barazanar tsaro irin su ’yan daba da sauran masu aikata laifi a Maiduguri da kewaye. Wannan na cikin irin tallafin da Gwamna Zulum ke bayarwa don inganta tsaro da kare...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa daƙile hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka Abba ya yi wannan yabo ne, yayin da yake karɓar babban kwamandan rundunar soji ta 1, a Hedikwatar Kaduna, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, a fadar gwamnati da ke Kano. Manjo Janar Wase, ya ziyarci Kano domin duba halin tsaro a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa. Ya bayyana yadda mahaifinsa,...
    Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo sun kama wata mata mai suna Chioma Success mai shekaru 27, bisa zargin kitsa garkuwa da kanta don karɓar kuɗin fansa daga mijinta. An kuma kama wasu mutum biyu da ake zargin sun taimaka mata wajen aikata laifin, wato Martins Chidozie mai shekaru 23 da Osita Godfrey mai shekaru 33. Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 Mataimakiyar Kakakin rundunar a jihar, ASP Eno Ikoedem, ta ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan bincike kan wani rahoton garkuwa da aka kai wa ’yan sanda. Ta ce a ranar 27 ga Oktoba, 2025,...
    Kungiyoyin agaji da dama na kasashen duniya sun yi gargadin cewa tallafin da ake bai wa yankin Gaza bai isa ba kusan wata guda bayan da aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yayin da yankin ke ci gaba da fuskantar matsalar abinci da matsugunai yayin da hunturu ke gabatowa. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) ta nuna cewa rabin kayan abinci da ake bukata ne kawai ke isa yankin da aka killace. Abeer Etefa, babban mai magana da yawun WFP, ya bayyana cewa hukumar ta isar da tan 20,000 na abinci, kusan rabin adadin da ake bukata, kuma ta bude wuraren rarraba abinci 44 daga cikin 145 da aka tsara. Ofishin...
    China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci. A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana mai gargadin cewa Amurka za ta iya tura sojoji idan gwamnatin Najeriya ta gaza dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ta’addacin masu kaifin kishin islama. Ya kuma sanar da cewa za a saka Najeriya cikin jerin “kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.” ke sa wa ido. Hukumomin Najeriya dai sun yi watsi da wadannan zarge-zargen, suna bayyana su a matsayin marasa tushe a...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
    Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar, duk da suka daga Shugaba Donald Trump da ‘yan Republican, da wasu ‘yan Democrat masu matsakaicin ra’ayi. Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump A jawabin nasararsa bayan doke tsohon Gwamna Andrew Cuomo, Mamdani ya ce yana da cikakken goyon baya daga jama’a, kuma ya bayyana...
    Daga Khadijah Aliyu  An fara shirye-shirye  gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Umaru A. Pate, ya umarci kwamitin da ya gudanar da aikinsa da himma da jajircewa domin tabbatar da nasarar taron, wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Kano. Ya bayyana cewa ana sa ran masana sama da 400 da sabbin mambobi daga ciki da wajen jihar za su halarta. Farfesa Pate ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan jajircewarta wurin...
    Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku. Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a hira da manema labarai a Gombe, a cikin shirin bikin Watan Wayar da Kan Jama’a game da Cutar Sankara. Ta ce an shirya gwajin ne domin inganta gano cutar tun da wuri da kuma bada magani cikin lokaci, kasancewar cancer na nono da na mahaifa su ne manyan cututtukan sankara da suka fi addabar mata. Dr. Hauwa Saurayi ta jaddada cewa gano cuta tun da...
    Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin wani gida, suna harbi a sama, sannan suka tafi da wasu daga cikin mazauna gidan. Daga nan ne rundunar ’yan sanda tare da ’yan banga da masu farauta suka isa yankin cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga ceto sun hada da Fatima Wasiu da Kudus Wasiu da jaririya mai watanni shida, ba tare da jin rauni ba. Sai dai har yanzu ana ci gaba...
    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta zuwa ganawa da jama’arsa kan muhimmin shirin ci gaba. Bayan harin, Honarabul Jafaru da tawagarsa sun samu rauni, inda aka garzaya da su asibiti, kuma suna karbar kulawar likitoci a halin yanzu. A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun isa yankin domin fatattakar ‘yan bindigar da kuma kare rayukan jama’a. Duk da haka, babu wata sanarwa ta hukuma a hukumance a yanzu game da...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce ta samu amincewar gwamnatin tarayya domin gina sabbin gada biyu na sama da kuma ta karkashin kasa (under-pass) a yankin Mararaba da ke Karamar Hukumar Karu. Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Abdullahi Sule kan Harkokin Jama’a, Mr. Peter Ahemba, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. A cewar Ahemba, gwamnati za ta fara aikin kafin gwamnatin yanzu ta kai ga karewar wa’adinta a shekara ta 2027. Ya ce tun da dadewa Gwamna Abdullahi Sule ya ware kudaden aikin, kafin ma a kammala tsarinsa. Ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2019, gwamnatin jihar ta kan ** tabbatar da ajiyar kuɗi kafin fara kowanne babban aiki**,...
    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar. Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, ya kai masa ziyara a Gidan Gwamnati Kano. Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa da yadda sojoji ke gudanar da aikinsu cikin kwarewau, jajircewa da kishin kasa, tare da bayar da tabbacin ci gaba da hadin kai tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro. Ya kuma gode wa Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu, bisa nada manyan hafsoshi masu kwarewa da suka himmatu wajen yaki...
    Kwamishinan Habbaka kiyon Dabbobi na Jihar Kano, Dr. Aliyu Isa Aliyu, ya fara ziyarar wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Ajingi da Dawakin Tofa. Ziyarar ta yi daidai da shirin gwamnati na kaucewa rikici, musamman sakamakon yuwuwar shigowar makiyaya daga Jamhuriyar Nijar cikin jihar. A Ajingi, Dr. Aliyu ya jagoranci tawaga ta jami’an tsaro, ma’aikatan ma’aikatar da shugabannin kungiyoyin manoma da makiyaya, inda ya bukaci tattaunawa, fahimtar juna da zaman lafiya, domin kauce wa sabani. Wakilin Hakimin yankin, Alhaji Abdulkadir Abdullahi, da shugaban karamar hukumar Dr. Abdulhadi Chula, sun yaba da wannan yunkuri tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kafa ma’aikatar da naɗa kwamishina mai nagarta. A Dawakin...
    Shugaban Juyin Juya Halin Musulunci Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ce sabanin da ke tsakanin Iran da Amurka “babban abu ne” kuma ya samo asali ne daga rikicin muradun kasa, yana mai gargadin cewa hadin gwiwa da Amurka zai yiwu ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta janye sansanonin soji daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran. Da yake jawabi a jajibirin ranar 4 ga Nuwamba, wato “Ranar Dalibai da Ranar Yaki ta Kasa da Girman Kai a Duniya,” Ayatollah Khamenei ya yi jawabi ga dubban dalibai da iyalan shahidan yaki a Tehran don tunawa da ranar tunawa da kwace Ofishin Jakadancin Amurka da ke Tehran a shekarar 1979, inda...
    Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Musa abu marzuk ya shaidawa gidan talabijin din Aljazeera cewa  sun yi watsi da batun tura dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa yankin Gaza wadanda zasu yi aiki a madadin sojojin mamayar Isra’ila Yace ba zamu taba amincewa da aikewa da sojojin da za su zama madadin sojojin Isra’ila a gaza ba, Wannan bayanin ya zo ne bayan da kasar Amurka ta fitar da wani daftarin kuduri a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya dake bukatar kafa dakarun tababtar da zaman lafiya na wucin gadi a yankin Gaza, akalla na shekaru 2 adaidai lokacin da falasdinawa ke fargabar tsoma bakin kasashen waje a yankin, Rahotanni da aka fitar ya nuna cewa...
    An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin Shugaban Amurka, Donald Trump, na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman,” yana zargin Gwamnatin Tarayya da bari a ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar. DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU Batun ya taso ne a ƙarshen zaman majalisar na ranar Talata, lokacin da Akpabio ya shaida wa ’yan majalisar cewa ’yan Najeriya na...
    Dakta Bukar ya bayyana wannan hadin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda yazo a kan gaba wajen karfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe , da dorewar cigaban kasa.   Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da kafafen yada labarai wajen isar da bayanan Hukumar ga al’umma.   A cikin jawabinsa, Kwamishinan yada labarai Malam Ahmed Maiyaki, ya yaba da wannan shiri tare da tabbatar da cikakken goyon bayan Ma’aikatarsa ga manufofin Hukumar.   Yace samar da sahihan da kafa gwamnati mai wacce da dogara da adalci yana daga cikin manifofi da kudirorin gwamnatin jihar Kaduna wanda hakan zai taiama wajen kawo...
    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba. Jaridar Vanguwar ta ruwaito wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar kan harkokin ƙasashen ƙetare, Anouar El Anouni ya fitar, yana cewa ƙungiyar EU na jajanta wa mutanen da rikicin ya rutsa da su a Kudanci da Arewa maso Gabashin ƙasar. HOTUNA: Mun kori jami’ai fiye da 100 cikin shekara guda — DSS Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar Jaridar Vanguard ta bayyana cewa matakin na ƙungiyar EU na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kan abin da ya kira...
    Cibiyar kandagarki da dakile cututtuka masu yaduwa ta Sin (CDC) ta fara kwas din horon fasahar gwaje-gwaje a kasashen waje a ranar 3 ga wata a hedkwatar CDC ta Afirka. Masana daga gwamnatocin Sin da Afirka da fannin kiwon lafiya, da kuma dalibai 30 daga kasashen Afirka 16, sun halarci bikin bude horon.   An bayyana cewa, wannan horon zai dauki tsawon makonni 3, inda cibiyar Africa CDC za ta taimaka wajen gudanar da shi. Fannonin horon sun hada da binciken kwayoyin cuta, da parasite, da gwajin cutar sida, nazarin kwayoyin halitta wato DNA, da ilimin halittu, da sa ido kan juriyar magunguna, da sauran fannoni masu muhimmanci. Manufar ita ce, horar da daliban da ma’aikatan gwaje-gwaje na Afrika CDC...
    Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
    Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa ta sallami jami’anta fiye da 100 a tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025, a wani yunƙuri na aiwatar da gyare-gyare a cikin hukumar. Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, DSS ta ce jimillar jami’ai 115 ta sallama daga aiki saboda dalilai daban-daban da suka shafi aiwatar da tsare-tsaren sabunta tsarin aiki. Fitaccen ɗan wasan tseren motoci Jenson Button zai yi ritaya Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar Sanarwar wadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce an fitar da sunaye da hotunan jami’an da abin ya shafa domin ankarar da jama’a. “A wani ɓangare na ci gaba da aiwatar...
    Shahararren ɗan wasan tseren motoci, Jenson Button, ya bayyana cewa gasar tseren Bahrain na sa’o’i takwas da za a gudanar a ƙarshen mako, ita ce za ta zama ta ƙarshe da zai yi a wasannin ƙwararru na tseren motoci. Button ɗan asalin kasar Birtaniya, wanda yake da shekaru 45, ya shafe shekaru biyu da suka gabata yana fafatawa a gasar World Endurance Championship (WEC) tare da ƙungiyar Jota. Tsohon gwarzon Formula 1 ɗin ya taɓa lashe Gasar Duniya ta Formula 1 a shekarar 2009 tare da ƙungiyar Brawn, kafin ya yi ritaya daga F1 a 2016 — bayan fafatawa a wasanni 306 cikin shekaru 18 na aikinsa, inda ya lashe Grand Prix sau 15.
    Daga Shamsuddeen Mannir Atiku  Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani ta Jihar Kaduna, wacce za ta taimaka wajen ƙarfafa tsarin fasaha na jihar da inganta gasa a fannin tattalin arziki. Dokar mai taken “Kaduna State Information Technology and Digital Economy Agency and for Related Matters, 2025” ta samu amincewa bayan karatu na uku a zaman majalisar na ranar Talata. Shugaban majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana muhimmancin dokar, yana mai cewa kafa hukumar zai faɗaɗa damar tattalin arziki tare da bai wa jihar Kaduna damar cin moriyar cigaban fasahar zamani a duniya. Ya ce hukumar za ta ƙarfafa kirkire-kirkire, bunƙasa ƙwarewar dijital, da daidaita...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
    Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump, kan kada ya ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya bayan zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar. Mista Tuggar, wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin tare da takwaransa na ƙasar Jamus, Johann wadephul, yana mai cewa Najeriya ƙasa ce mai bin doka da tsarin mulki, wadda ke tabbatar da cikakken ’yancin addini ga dukkan ’yan ƙasa. Dalilin da Trump ya yi iƙirarin ana kisan Kiristoci a Nijeriya — Ndume Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich “Kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ƙasa sun haramta cin zarafin addini, kuma suna tabbatar da damar...