Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta kasar Argentina da Inter Miami, Lionel Messi, ya bayar da sharadin da zai sa ya buga wa Argentina wasa a gasar FIFA World Cup na shekarar 2026 da za a buga a kasashen Arewacin Amurka, za a buga gasar cin kofin Duniya na 2026 a manyan biranen kasar Kanada, Amurka da Medico a lokacin bazara, kuma ana sa ran gwarzon dan wasan na Argentina zai halarci gasar.

Duk da haka, Messi ya ce zai shiga tawagar Argentina ne kawai idan yana cikin koshin lafiya, yana mai tabbatar da cewa ba ya son zama nauyi ga tawagar, Messi ya jagoranci Argentina zuwa ga nasara a gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 inda suka doke Faransa a wasan karshe, Messi zai zama daya daga cikin ‘yan wasa biyu kacal da za su buga gasar cin kofin Duniya har sau shida, tare da Cristiano Ronaldo.

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

A wata hira da Sport, an tambayi dan wasan mai shekaru 38 game da buga wasa a Gasar Cin Kofin Duniya na FIFA mai zuwa ta 2026, tauraron dan wasan Argentina ya ce, “Eh, a bayyane yake, Gasar Cin Kofin Duniya, wasa ne na musamman ga tawagar kasa, akwai bukatar a saka naci wajen ganin an samu nasara,” in ji Messi.

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika November 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe November 14, 2025 Wasanni Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati November 14, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kofin Duniya na Kofin Duniya Na

এছাড়াও পড়ুন:

Nijeriya ta doke Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya

Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles ta doke tawagar ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka fafata a yammacin wannan Alhamis.

Wasan wanda aka soma da ƙarfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat a Morocco, ya bai wa Super Eagles damar lallasa The Panthers har ci 4-1.

Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya

Wannan sakamakon ya bai wa Nijeriya nasarar kaiwa zagayen ƙarshe a wasan cike gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026.

Akor Adams ne ya fara ci wa Super Eagles ƙwallo a minti na 78, amma daga baya Gabon ta farke ta hannun Mario Lemina daf a tashi daga fafatawar.

A haka dai aka tashi 1-1 bayan minti 90 da suka buga, lamarin da ya sa aka yi ƙarin minti 30 saboda dole sai an samu wanda zai yi nasara.

Bayan an dawo daga hutun ƙarin lokacin ne aka ci gaba da fafatawar har ta kai ga Super Eagles ta ƙara na biyu ta hannun Chidera Ejuke, sannan Victor Osimhen ya ƙara na uku na hudu.

A ɗaya wasan daf da ƙarshen kuma, Kamaru ce za ta fafata da Jamhuriyar Congo a ranar Alhamis, inda duk wanda ya yi nasara a ciki, zai fuskanci tawagar ta Nijeriya a ranar Lahadi mai zuwa.

Wasan na yau dai shi ne na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.

An barje gumin ne ƙasa da awanni 24 bayan tawagar Super Eagles da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) sun warware matsalolin da suka shafi kuɗaɗe tsakanin ‘yan wasa da hukumomin ƙwallon ƙafa.

Kyaftin William Troost-Ekong ya tabbatar da cewa an biya dukkan haƙƙoƙin da suke bi, inda ya ce tawagar ta koma fili cikin karsashi da ƙwarin gwiwar neman nasara a wasan yau.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
  • Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika
  • Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe
  • Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati
  • Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana
  • Nijeriya ta doke Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
  • Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
  • Nijeriya Za Ta Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Gusau
  • ‘Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 10 Da Za Su Iya Buga Gasar Cin Kofin Duniya Ta Ƙarshe A 2026