Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Shirya Faɗaɗa Gonakin Shinkafar Jangwa Don Ƙara Samar da Shinkafa
Published: 12th, November 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe.
Gwamnan ya ce faɗaɗa gonakin zai ƙara hektar 3,000 daga yawan da ake da shi yanzu, domin inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar aikin gona. Ya kuma nuna yadda jihar ta samu ci gaba a fannin noma, inda gonar ta faɗaɗa daga hektar 2,000 a bara zuwa hektar 3,300 a wannan shekarar.
Gwamna Sule ya sanar da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da kamfanin Silvex International, babban kamfani mai sarrafa shinkafa, domin ƙara samar da shinkafa a jihar.
A cewar Gwamna Sule, haɗin gwiwar zai baiwa Silvex International damar sayen shinkafar kai tsaye daga gonakin jihar sannan a tattara ta a ƙarƙashin tambarin Nasarawa Agro-Commodity Company (NASACCO).
Shinkafar, wacce za a kaita Kasuwa da suna “NASACCO Gold”, ana sa ran zai ƙara shahara da darajar kayan shinkafar jihar a kasuwa.
Gwamnan ya yi godiya ga Silvex International bisa wannan haɗin gwiwa, wanda ya ce yana daga cikin matakan gwamnatinsa na jawo jarin masu zaman kansu zuwa fannin aikin gona a jihar.
Haka kuma, Gwamna Sule ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen ƙara samar da shinkafa a jihar, tare da shirin faɗaɗa gonar zuwa hektar 8,000 nan gaba.
Gwamnan ya yaba wa matasa da al’ummomin garuruwan Jangwa, Ayakeke, da Agwatashi bisa jajircewarsu wajen tabbatar da nasarar gonar.
A nasa jawabi, Babban Jami’in Gudanarwa na Silvex International kuma Shugaban Aikin NASACCO, Abubakar Garba Ibrahim, ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin babban ci gaba ga kamfanin.
Ya bayyana cewa haɗin gwiwar zai amfani jihar ta hanyoyi da dama, ciki har da haraji, ƙara darajar kayayyaki, da raba riba ta ƙarshe.
Aliyu Muraki, Lafia.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: haɗin gwiwar
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Shugaban Majalisar Kebbi ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Sama’ila Bagudo, ya kuɓuta bayan shafe fiye da mako guda a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.
Aminiya ta ruwaito cewa an sace mataimakin shugaban majalisar ne a ranar Juma’a 31 ga Oktoba, 2025, jim kaɗan bayan ya kammala sallar la’asar a masallacin garinsu na Bagudo.
’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra Gwamna Soludo ya lashe Zaɓen Anambra karo na biyuSakataren gwamnatin jihar, Yakubu Tafida, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Asabar.
Bayanai sun tabbatar da cewa lamarin na zuwa ne daidai da lokacin da aka gudanar da addu’o’in haɗin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci domin neman zaman lafiya a jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da cewa an saki mataimakin shugaban majalisar.
CSP Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka yana tare da iyalansa bayan mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa a wani asibiti.
“An sace shi a ranar 31 ga Oktoba, amma an sako shi jiya [Asabar] kuma yanzu yana cikin ƙoshin lafiya kamar yadda mahukunta suka tabbatar,” in ji kakakin rundunar.
Ya ƙara da cewa rundunar ta yaba da jajircewar jami’an tsaro da suka shiga aikin ceto tare da goyon bayan al’umma, inda ya ce bayanan da jama’a suka bayar sun taka muhimmiyar rawa wajen ceto wanda aka sace lafiya.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a faɗin jihar, tare da kira ga jama’a su kasance masu lura da duk wani motsi da ake zargi su kuma rika sanar da hukumomin tsaro cikin gaggawa.