Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba
Published: 12th, November 2025 GMT
“Dukkanin bayanan da ake da su sun nuna cewa babu wani kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya… Wannan labarin ƙarya ne da ƙungiyoyi suka ƙirƙira, wanda Shugaba Trump ke ƙoƙarin yaɗawa.
“Wannan magana za ta iya ƙara tayar da hankali a Nijeriya… ‘Yan ta’adda suna kai hare-hare a kasuwanni, coci-coci, da masallatai, kuma suna kashe kowa ba tare da bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba,” in ji Bukarti yayin wata hira da gidan talabijin na Al-Jazeera.
Masana da dama sun yi gargaɗin cewa irin wannan kalamai daga shugabanni na iya haddasa tashin hankali a ƙasar.
Martanin Gwamnatin TarayyaGwamnatin Tarayya ta kuma mayar da martani ta hanyar ƙaryata batun cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.
Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa kowa damar yin addininsa cikin ‘yanci, don haka babu wani dalili da zai sa a ce gwamnati tana goyon bayan addini ɗaya.
Ya kuma ce Nijeriya na maraba da duk wani taimako da zai ƙara wa jami’an tsaronta ƙarfi wajen yaƙi da ta’addanci, amma cikin mutunta ƙasar.
Matakin DokaA matakin doka kuwa, babu wata hanya da Amurka za ta iya kai wa Nijeriya hari kai-tsaye. Dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya sun hana kowace ƙasa kai hari sai da izinin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Haka kuma, dokar Amurka ta ‘War Powers Act’ na buƙatar shugaban ƙasa ya sanar da majalisa cikin awa 48 idan zai tura sojoji ƙasar waje, kuma ya buƙaci amincewar majalisa idan za a tsawaita zaman sojojin.
Wannan na nufin cewa babu wata doka da za ta bai wa Trump damar kai hari kai-tsaye a Nijeriya.
A ɓangaren matakin soji liwa, hakan ma ba abu ne mai sauƙi ba. Nijeriya tana da yawan jama’a sama da miliyan 220, tana da faɗin ƙasa da ke da wahalar sarrafawa, kuma rikice-rikicen da ake fuskanta a ƙasar sun samo asali ne daga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da na masu aikata laifuka. Saboda haka, duk wani yunƙuri daga Amurka zai fi dacewa ya taƙaita ga bayar da horo, bayanan sirri, da tallafi wa sojojin Nujeriya, ba kai sojoji ƙasar ba.
Masana harkokin tsaro sun yi gargaɗin cewa irin wannan yunƙuri na iya haifar da tsadar abinci, asarar rayuka, da tashin hankali a ƙasar.
A yanzu dai, abin da zai iya yiwuwa shi ne amfani da hanyoyin diflomasiyya da takunkumi, maimakon yaƙi. Majalisar Dokoki ta Amurka na tattaunawa kan yiwuwar sanya wa mutanen da ke taimaka wa rikice-rikice a Nijeriya takunkumi, yayin da ECOWAS da sauran ƙasashen Afrika ke ƙaryata batun “yi wa Kiristoci kisan kiyashi”.
Masana a Nijeriya na jaddada cewa mafita game da lamarin shi ne haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da tsare-tsaren tsaro masu mutunta ikon ƙasar.
A gefe guda wasu na ganin ana so a yi amfani da bambacin addini ko siyasa domin samun damar yi wa Nijeriya kutse don samu damar wawushe mata albarkatun ƙasa kamar man fetur, ma’adanai da sauransu.
Wani lauya masanin harkokin tsaro mai suna Barista El-Zubair na ganin cewa akwai wasu ɓoyayyun dalilai da ya sa Trump ya fara waɗannan maganganu.
“Idan ya ce zai ɗauki matakin soji a kan Nijeriya, ta ina zai fara?
Nijeriya tana da girma da faɗi, kuma ga tarin al’umma, don haka wasu dalilai ne kawai suka saka yake waɗancan kalamai, amma batun ana kashe Kiristoci ba gaskiya ba ne, kawai yana son fakewa da shi ne don cimma wata manufa tasa.”
A taƙaice, dokokin ƙasa da ƙasa, ƙalubalen dabaru, da ra’ayoyin masana sun tabbatar da cewa kalaman Trump tsagwaron barazana ce ta siyasa, kuma ba gaske ba ce domin babu wata hujja da ta nuna ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: yi wa Kiristoci
এছাড়াও পড়ুন:
Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙiru da Bebeji daga Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC, wata biyu bayan jam’iyyar NNPP ta dakatar da shi.
A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar da sauya sheƙarsa tare da magoya bayansa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC tare da goyon bayan neman wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.
Abdulmumin Jibrin ya sanar ta shafinsa cewa sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa. “Na samu kyakkyawar tarba daga dubban al’ummar mazaɓata ta Kofa, Bebeji, da ke Jihar Kano.
“Taron ya yi ittifaƙin ficewa daga NNPP/Kwankwasiyya, mu koma APC, tare da goyon bayan Shugaba Tinubu ya yi wa’adi na biyu.
An ƙara rage kuɗin aikin Hajjin 2026 a Najeriya Mahaifiyar Minista Balarabe Lawal Abas ta rasu“Kafin nan, malamai kimanin 2,000 daga mazaɓarmu sun gudanar da addu’o’i na musamman ga Shugaban Ƙasa da neman samun zaman lafiya da ci-gaban Ƙiru/Bebeji, Kano, da ma Najeriya baki ɗaya.”
Idan ba a mata ba, Jam’iyyar NNPP ta dakatar da ɗan majalisar ne bisa zargin yi mata zagon ƙasa da kuma rashin kuɗin ƙa’ida na jam’iyya.
Tun bayan lokacin ba a ji daga gare shi ba game da makomar siyasarsa, duk da cewa makusantansa sun bayyana cewa yana ɗasawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC, wanda ya kawo hasashen yiwuwar komawarsa APC.
A safiyar Litinin ɗin nan ɗan majalisar ya sanar ta shafinsa cewa ya sun ɗauki matakin ne bayan tattaunawar al’ummar mazaɓarsa.
A ɗaya daga bidiyoyi daya wallafa, an ga ɗan majalisar yana jawabi ga magoya bayansa da cewa zai sauya sheƙa tare da magoya bayansa domin kauce wa kuskurensa na baya na sauya sheƙa shi kaɗai.
“Na yanke shawarar zuwa da wannan taron jama’a domin gyara kuskuren da na yi a baya. Kada daga baya wani ya zo yana cewa ai ba Ni da magoya baya.”
Daga nan ya tambaye su ko sun yarda su fice daga NNPP da Kwankwasiyya zuwa APC, inda suka yi ta shewa suna cewa “APC.”
Daga nan ya tambaye su wanda za su zaɓa a 2027, sai suka amsa cewa “Tinubu.”