Aminiya:
2025-12-13@14:09:07 GMT

Dalilin da ya kamata PDP ta jingine taron da za ta gudanar— Saraki

Published: 13th, November 2025 GMT

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya buƙaci jam’iyyar PDP da ta ɗage babban taronta da ta shirya gudanarwa tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

Saraki ya ce ci gaba da shirin gudanar da taron duk da irin umarnin dakatarwa da kotuna suka bayar zai ƙara ta’azzara rikicin jam’iyyar sannan ya jefa ta cikin matsaloli a nan gaba.

An kama mutum 3 kan zargin safarar yara 17 a Zariya Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya

Ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan karɓar baƙuncin ’yan kwamitin amintattun jam’iyyar ƙarƙashin shugabancin Ambasada Hassan Adamu, a gidansa.

Tawagar ta ziyarci Saraki ne domin neman tabarrakinsa da shawarwari kan yadda za a cimma haɗin kai a jam’iyyar da ta samu rarrabuwar kai.

Tsohon shugaban da ya jagoranci Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019, ya ce umarnin kotuna kusan huɗu masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala kan halascin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.

Zuwa yanzu, akwai ƙararraki uku a gaban kotuna daban-daban waɗanda suka bayar da umarnin dakatar da shirin taron, yayin da PDP ta ce tana ci gaba da shirin gudanar da shi a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba.

Daga cikin waɗanda suka kai jam’iyyar kotu kan taron akwai Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Abubakar Bukola Saraki

এছাড়াও পড়ুন:

‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’

Wani mazaunin Kano, Namadi Bawa, ya bayyana yadda ya shiga cikin daji a Jihar Zamfara domin kai kudin fansa ga ’yan bindiga da suka sace ɗan uwansa, inda ya tarar da su cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, kafin daga bisani ya samu ya kubutar da shi. A tattaunawar mutumin da Aminiya, y ace an sace ɗan uwan nasa ne a Gusau babban birnin jihar Zamfara, a kan hanyarsa ta dawowa daga Sakkwato.A cewar Namadi, ɗan uwansa ya ci karo da shingen da ya yi kama da na jami’an tsaro a hanya, sai dai daga baya aka gano ’yan bindiga ne suka yi masa kwantan bauna tare da wasu fasinjoji.

“Sun kira ni suka tambaya ko na san ɗan uwana, na ce eh. Suka ce sun sace shi kuma yana hannunsu. A lokacin kwana ɗaya kenan da sace shi,” in ji Namadi.

Cinikin kuɗin fansa da tafiya daji domin kai musu

Ya ce masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa har Naira miliyan 16, amma bayan tattaunawa aka rage zuwa miliyan bakwai.

Namadi ya ce masu garkuwar sun yi gargaɗin cewa ba za su lamunci rage wani abu daga adadin kudin da aka yi cinikin ba, suna gargaɗin cewa muddin suka ƙirga kuɗin suka ga ba su cika ba, za a ga ba daidai ba.

“Sun ja hankali cewa kada a rage ko ƙwandala a ciki, idan aka rage za a ga ba daidai ba,” in ji shi.

Namadi ya bayyana yadda ya je da kansa ya kai kudin cikin daji.

A cewarsa, an umurce shi ya tsaya a wani ƙauye kafin daga bisani a nuna masa hanyar shiga. Daga bisani aka ba shi wata riga ya saka kafin ya isa wurin da aka karɓi kudin.

“Na zaci za su ƙirga kudin, amma sai suka tattaka su da ƙafa, suka ce sun cika. Bayan haka suka ce na gangaro daga kan dutsen da suka kai ni. Na yi ta kallo ko zan ga ɗan uwana, amma daga baya ne suka nuna min shi tare da wasu da aka sace, duk suna kwance cikin yanayin rashin lafiya,” in ji shi.

Yanayin dajin da masu garkuwar

Namadi ya ce yanayin da ya tarar da su ya nuna suna fama da cutar kwalara, inda aka ajiye su a bukka a tsakiyar dajin da ba motar da za ta iya shiga sai babur.

“Na san idan a wannan yanayin ne, ba za su yi dogon zango ba. Ta su za ta kare,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ɗan uwansa da sauran da aka sace sun shiga mawuyacin hali, inda dole ne aka kai ɗan uwansa asibiti bayan an karɓo shi saboda yanayin da aka same shi.

Namadi ya kuma ce duk da fargaba da tashin hankalin da ya shiga, addu’a ce ta taimaka masa ya dawo gida lafiya.

“Mu ci gaba da addu’a saboda tana da tasiri a kan mutanen nan. Insha Allahu Allah zai kawo ƙarshen su,” in ji shi.

Cin karo da wasu masu garkuwar a hanyar dawowa

Bayan ya karɓo ɗan uwansa, Namadi ya ce a hanyarsa ta fita daga dajin ya sake cin karo da ’yan bindigar sun kamo wasu mutanen, suna kaɗa su zuwa cikin daji.

“Sun ba ni shawara kada na bi ta inda na zo, saboda akwai ƙungiyoyin masu garkuwa da dama a yankin waɗanda ba sa ga maciji da juna da za su iya sake kama mu,” in ji shi.

Daga nan sai ya ce duk da muggan makaman da ’yan bindigar ke da su, ba su fi ƙarfin gwamnati ba.

Ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙoƙari wajen kawar da ’yan bindiga a yankin, tare da fatan addu’ar jama’a za ta taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe
  • Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan
  • ‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’
  • Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026”
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • Mahajjata 2,235 Ne Suka Yi Rijistar Aikin Hajjin 2026 A Sokoto
  • Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026
  • Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa
  • Ba ni da shirin ficewa daga PDP — Gwamnan Bauchi
  • Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jigawa Ta Nemi Kotuna Su Daina Jan Kafa Wajen Aiwatar da Shari’a