AIG Zubairu Ya Umurci ‘Yan Sanda a Kwara Su Ninka Kokarinsu Don Karfafa Tsaro
Published: 12th, November 2025 GMT
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Babban Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda mai kula da shiyya ta 8, da ke Lokoja, AIG Abubakar Zubairu, ya bukaci jami’an ‘yan sanda a Jihar Kwara da su ninka kokarinsu wajen karfafa hadin kai da kuma zurfafa dangantaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma.
A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ta fitar, ta ce AIG Zubairu ya yi wannan kira yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kwara da ke Ilorin.
Sanarwar ta yaba wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar ‘yan sanda da kuma kudaden da gwamnatinsa ke fitarwa domin inganta tsaro.
Haka kuma, ta yi kira da a ci gaba da hadin kai, musamman ta fuskar tallafin kayayyakin aiki da kuma karfafa hulda da al’umma, domin kara inganta ayyukan rundunar.
Sanarwar ta kuma yaba wa jami’ai da ma’aikatan rundunar bisa kwarewa, ladabi da jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara Rundunar Yan Sanda Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina
An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.
Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.
Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da suka hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, bindiga kirar gida guda daya, harsasai 183, motoci uku, babura uku, babur mai kafa uku (Keke-napep) daya, da kuma dabbobi sama da 200 da aka sace.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA