Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya.

Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin.

Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona.

A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura yana dacewa da aikin da aka tsara, tare da samun ƙwararrun masu gyara.

Ministan ya bayyana cewa, manoma na Najeriya suna bukatar fasahohi na gida, waɗanda aka haɓaka bisa fahimtar ƙasa, irin amfanin gona, da kuma girman noman da ake yi.

END/ALI MUHAMMAD RABIU

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Noma Kwara

এছাড়াও পড়ুন:

Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi gwamnatin tarayyar Nigeria da ta wanke ‘yan Ogoni 9 ta fuskar shari’a, bayan gushewar shekaru 30 da zartar musu da hukuncin kisa.

“Ya Ogoni 9 da su ka hada da fitaccen marubuci Ken Saro Wiwa sun kasance masu fafutukar kare muhalli daga gurbata shi da kamfanin man fetur na Shell yake yi.

Wannan kiran daga kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ya zo ne a daidai lokacin da ake bude taron kare muhalli na duniya a kasar Brazil.

Shugaban kungiyar ta “Amnesty International” a Nigeria, Isa Sunusi ya bayyana cewa; Duk da cewa afuwar da gwamantin ta yi musu ci gaba ne,amma  masu rajin kare muhallin na Ogoni su 9 sun cancanci a wanke su ta fukar shari’a.

Sunusi ya ci gaba da cewa, kisan da aka yi Ken Saro Wiwa da sauran abokan fafutukar tashi, na dabbanci ne, kuma an yi shi ne bisa zalunci, domin ba su aikata wani laifi ba,don haka iyalansu suna bukatar a yi musu adalci.

Sojoji sun kutsa cikin kauyuka 43 a yankin Ogoni tare da kashe mutane da dama a cikin watan Maris na 1994, sun kuma yi hakan ne bisa bukatar kamfanin na Shell.

 An zartar da hukuncin kisa ne akan Ken Saro Wiwa da sauran abokan fafutukarsa 9 a ranar 10 ga watan Nuwamba na 1995

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hukumar Alhazai Ta Kasa A Nigeriya Ta sanar Da Rage Kudin Farashin Aikin Hajji Na Bana November 10, 2025 Hukumar Kare Hakkin Bil Adama Ta M D D Ta yi Gargadi Game Da Abin Da ke Faruwa A El-Fasher November 10, 2025 Iran Tayi Tir Da Rashin Kyakkyawar Niyyar Amurka Kan Batun Tattaunawa Bayan Kalaman Trump November 10, 2025 Afrika Ta Kudu Tace Babu Abinda Zai faru idan Amurka ba ta halarci taron G20 ba November 10, 2025  Babu Wani Zabi Da Ya Rage Face Amincewa Da Iran A Matsayin Cibiyar Kimiyyar Masana’antar Nukiliya November 10, 2025  Kamaru: Chiroma Ya Bai Wa Gwamnati Sa’o’i 48 Da Ta Saki Wadanda Ta Kama Bayan Zabe November 10, 2025 ‘Yan Jarida 44 Ne Su Ka Yi Shahada A Sansanonin Hijira Na Gaza November 10, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Isra’ila” A Yankin Saida November 10, 2025 Tarayyar Afirka (AU) Ta Yi Gargadi Akan Tabarbarewar Harkokin Rayuwa A Kasar Mali November 10, 2025 An Fara Gasar Karatun Alqur’ani Mai Tsarki ta Sheikha Hind Bint Maktoum November 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa
  • Bayan Da Muka Fara Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa
  • Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Shirya Faɗaɗa Gonakin Shinkafar Jangwa Don Ƙara Samar da Shinkafa
  • Hukumar Tsara Birane ta Kano Ta Fara Horar da Ma’aikata Kan Dokokin Aiki
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfado Da Filin Jirgin Sama Na Kano
  • Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa?
  • Gwamnatin Tarayya Ta Jinjinawa Gwamnan Jigawa Bisa Ayyukan Ci Gaban Jihar
  • Amnesty Ta Kira Yi Gwamnatin Najeriya Da Ta Wanke ‘Yan Ogoni 9 Da Aka Zartarwa Da Hukuncin Kisa Shekaru 30 A Baya
  • An sake rage kuɗin aikin Hajjin 2026 a Najeriya